16/01/2026
CIWON KAI BA KOYAUSHE YAKE BUƘATAR MAGANI BA.
Ciwon kai abu ne da yawanci ke faruwa, kuma mutane da yawa kan garzaya shan magani nan da nan. Amma ba duk ciwon kai ke buƙatar magani ba. Wasu na faruwa ne saboda damuwa, rashin bacci, yunwa, ƙarancin ruwa a jiki, ko kallon waya📱 da yawa.
A irin wannan yanayi, shan magani na iya ɓoye matsalar kawai ba tare da magance tushenta ba.
Abin da ya kamata ka sani:
• Rashin shan ruwa na iya jawo ciwon kai
• Damuwa da rashin bacci na daga cikin manyan dalilai
• Yawan shan painkillers na iya ƙara ciwon kai
Abin da za ka gwada da farko:
• Shan ruwa
• Hutu ko yin bacci
• Rage kallon waya
• Yin miƙa da jiki(stretching)
• Ci abinci idan kana jin yunwa
Pharmacist’s Note:
Yawan shan maganin ciwo kai na iya haddasa ciwon kai mai dawowa.