Hausa 24

Hausa 24 Ku kasance da (Hausa 24) domin samun ingantattun labarai cikin harshen hausa

“Ganduje fa neman shi ake yi, a Kotuna wurin guda biyu, an ce masa ya zo yaƙi zuwa, amma sai ga shi a gidan Gwamnati ga ...
29/01/2026

“Ganduje fa neman shi ake yi, a Kotuna wurin guda biyu, an ce masa ya zo yaƙi zuwa, amma sai ga shi a gidan Gwamnati ga ‘yan sanda ga jami'an tsaro ga komai, k**ar wasan kwaikwayo? - Barr. Abba Hikima.

Barista Abba Hikima ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Manhajar Facebook, inda ya bayyana cewa yanzu haka Kotuna biyu suna neman Ganduje bisa tuhumar da ake masa na Handama, ya ce maimakon a k**a shi a lokacin da ya zo gidan Gwamnatin Kano, sai ba a yi haka ba, duk da akwai jami'an tsaro a wurin.

MAZAN JIYA; Shugaban Nigeria Na Mulkin Soji Gen. Muhammad Sani Abacha Tare Da Dan Shi Ahmad Lokacin Rayuwar Shi.
22/01/2026

MAZAN JIYA; Shugaban Nigeria Na Mulkin Soji Gen. Muhammad Sani Abacha Tare Da Dan Shi Ahmad Lokacin Rayuwar Shi.

Sheikh Ibrahim Isa Makwarari ya kwana guda ɗaya a gidan gyaran hali da tarbiyya da ke Kano, sak**akon rashin cika sharuɗ...
22/01/2026

Sheikh Ibrahim Isa Makwarari ya kwana guda ɗaya a gidan gyaran hali da tarbiyya da ke Kano, sak**akon rashin cika sharuɗɗan belin da kotu ta gindaya masa.

Jami’an Gidan Gyaran Hali da Tarbiyya ne s**a tafi da shi gidan yari, a ranar Laraba bayan ya kasa cika sharuddan belin da Kotun Majistri ta bayar a zaman da ya gabata.

Tun da farko dai, rundunar Ƴansandan jihar Kano ce ta gurfanar da Sheikh Ibrahim Isa Makwarari, ranar Talata bisa zargin mallakar takardun filaye na bogi, sai dai a ranar Laraba kotun ta bayar da shi belin bayan neman hakan daga lauyansa, bisa tsauraran sharuɗɗa, waɗanda bai samu damar cikawa ba, abin da ya sa aka tsare shi.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci domin ci gaba da sauraron ƙorafe-ƙorafen da ke kansa.

Kungiyar Karuwai a Najeriya Ta Yi Barazanar Yajin Aiki Kan Amfani da Magungunan Ƙarfafa MazaWata ƙungiya da ke wakiltar ...
09/01/2026

Kungiyar Karuwai a Najeriya Ta Yi Barazanar Yajin Aiki Kan Amfani da Magungunan Ƙarfafa Maza

Wata ƙungiya da ke wakiltar karuwai masu zaman kansu a Najeriya ta bayyana shirin tsunduma yajin aiki, sak**akon yadda wasu maza ke amfani da magungunan ƙarfafa maza yayin hulɗarsu da su.

A cewar ƙungiyar, lamarin ba wai ya tsaya kan rashin daidaiton kuɗin da ake biyansu kaɗai ba, har ma da matsalolin lafiyar da wasu daga cikinsu ke fuskanta bayan hulɗa da mazan da s**a yi amfani da irin waɗannan magunguna.

Matan sun bayyana cewa amfani da magungunan na haifar da tsawaitar lokaci fiye da kima, wanda ke jawo musu gajiya da radadin jiki, tare da illolin lafiya da ke bukatar kulawa ta musamman.

Wata wakiliyar ƙungiyar ta ce idan har ba a ɗauki matakan da s**a dace ba, za su iya dakatar da ayyukansu na wani lokaci domin jawo hankalin hukumomi da al’umma kan matsalolin da suke fuskanta.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu martani daga hukumomin lafiya ko na tsaro ba dangane da wannan batu. Masana kiwon lafiya dai na ci gaba da gargadi kan amfani da magungunan ƙarfafa maza ba tare da shawarar likita ba, suna mai cewa hakan na iya haifar da illa ga lafiyar jiki.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta zargi Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da amfani da ofishin Mashawarcin Tsaron Kasa NSA wajen...
09/01/2026

Gwamnatin Jihar Zamfara ta zargi Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da amfani da ofishin Mashawarcin Tsaron Kasa NSA wajen tsoratar da ƴan adawa, lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin siyasa a jihar.

Mataimakin ministan ya musanta zargin tare da cewa ba gaskiya ba ne.

'Yan Kwankwasiyya na Tsokanar Masu madafin Iko a Gwamnatin Abba a kafofin sada zumunta
04/01/2026

'Yan Kwankwasiyya na Tsokanar Masu madafin Iko a Gwamnatin Abba a kafofin sada zumunta

KAJI MAZA: Yadda Matashi Ya Gwangwaje Da Auren Matansa Uku Rigis, A Rana Daya.me zakuce 👇 Wane fata zakuyi masa?
01/01/2026

KAJI MAZA: Yadda Matashi Ya Gwangwaje Da Auren Matansa Uku Rigis, A Rana Daya.

me zakuce 👇

Wane fata zakuyi masa?

Wane sunan Hausawa ne zai dace da shugaban Amurka Donald Trump?
28/12/2025

Wane sunan Hausawa ne zai dace da shugaban Amurka Donald Trump?

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara jihohin Borno da Bauchi, kafin daga bisani ya wuce Lagos domin bikin sabuwar sh...
20/12/2025

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara jihohin Borno da Bauchi, kafin daga bisani ya wuce Lagos domin bikin sabuwar shekara.

Fatima garba Yar akuya  Daga Jihar Zamfara.
19/12/2025

Fatima garba Yar akuya Daga Jihar Zamfara.

Da Ɗumi Ɗumi Gwamnati Ta Hana Biyan Sama Da Dubu Dari Biyu Da Goma (210,000) A Matsayin Kuďin Hayar Gida Komai Girman Sa...
19/12/2025

Da Ɗumi Ɗumi

Gwamnati Ta Hana Biyan Sama Da Dubu Dari Biyu Da Goma (210,000) A Matsayin Kuďin Hayar Gida Komai Girman Sa A Jihar Sokoto!

Doka a jihar sokoto ta hana biyan kuďin hayar gida sama da abun dake kasa:

1. 4 Bedroom a manyan unguwanni (na masu kuďi) = Dubu ďari biyu da goma(210,000).

2. 4 Bedroom a matsakaitan unguwanni = Dubu ďari da saba’in (170,000).

3. 4 Bedroom a kananan unguwanni = Dubu casa’in (90,000).

Duk gidan da ba ďakuna huďu ba, kuďin shi bai kai yawan abun dake sama ba. Kuma lallai duk mai gidan hayan da ya karbi sama da haka a jihar sokoto zai fuskanci hukunci.

Saboda haka matasa, samarin jihar sokoto da tuzurai a motsa ayi aure, doka tayi muku saukin haya.

Daga Abdurrahman Muhammad Jariri

RUGUM BABBAN MOTSI...: Yanda Wani Matashin Saurayi Ya Zaɓo Wata Tsaleliyar Budurwar Domin Aurenta.
18/12/2025

RUGUM BABBAN MOTSI...: Yanda Wani Matashin Saurayi Ya Zaɓo Wata Tsaleliyar Budurwar Domin Aurenta.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram