Allurar cikin ruwa Albarka Radio

Allurar cikin ruwa Albarka Radio Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Allurar cikin ruwa Albarka Radio, Alternative & holistic health service, Mambila Avenue, Sunday awoniyi New GRA Bauchi, Bauchi.

29/07/2024

Yau shirin Allurar cikin ruwa zai mayarda hankali ne akan tsangwamar da ake nunawa masu fama da cutar Tarin Fuka wato TB

28/06/2023
17/10/2022

Ranar Wanke Hannu Ta Duniya🤚🤚🏼🤚🏿
A Fafata...

1. Wasu gurare ne idan aka yi mu'amala dasu sai an wanke hannu?
2. Menene taken bikin bana (2022)
3. Matakai nawa ake bi idan za'a wanke hannu?

06/10/2022

Hukumar gudanarwar Albarka Radio tana sanar da masu sauraronta cewa tashar ta samu tangarda a ranar Alhamis. Muna bada tabbaci wa dumbin masu sauraronmu cewa tawagar injiniyoyinmu suna aiki tukuru wajen ganin cewa an dawo watsa shirye shirye cikin kankanin lokaci. Hukumar gudanarwar tana bada hakuri...

Shanyewa, rauni, sagewa ko ciwo na iya biyo bayan allura a dantse.Waɗannan matsaloli na faruwa ne idan aka samu kuskure ...
13/09/2022

Shanyewa, rauni, sagewa ko ciwo na iya biyo bayan allura a dantse.

Waɗannan matsaloli na faruwa ne idan aka samu kuskure yayin allura a dantse kamar haka:

1. Tsira allura a kan jijiyar laka.

2. Allura na iya haifar da kumburin da zai danne ko shaƙe jijiyar laka.

3. Lahani daga ruwan allura wanda wa'adinsa ya riga ya ƙare, da dai sauransu.

Waɗanda s**a fi gamuwa da wannan matsala sun haɗa da:

1. Ƙananan yara, musamman saboda tsoron allura suna yin zille-zille yayin yin allurar ko kuma saboda tsokokin jikinsu ba su gama girma ba.

2. Wanda bai ba da haɗin kai ba yayin allura na iya gamuwa da wannan matsala ko da babba ne.

3. Tsofi, musamman saboda raguwar kaurin tsokokin jiki yayin da shekaru s**a fara miƙawa.

4. Mai siririn dantse ko wanda ya rame sosai.

5. Wanda ya faɗa hannu wanda bai ƙware ba.

6. Wanda tsautsayi ya faɗawa, saboda wasu su kan ce "allura ba ta da gwani!"

Daga cikin matsalolin da ke iya ƙara afkuwar matsalar shanyewar hannu ko ƙafa bayan allura, musamman ga yara, akwai al'adar nan ta tsorata yara da yi musu allura idan suna ƙiriniya ko kuma idan ana so su yi ko bar wani abu. Tsorata su da allura yana shiga tunaninsu cewa allura aba ce mai ciwo sosai. Saboda haka, duk lokacin da za a yi musu allura suke tsorata har su fara zille-zille. Hakan kuma na iya sa allura ta sauya hanyarta zuwa jijiyoyin laka.

Idan kana fama da shanyewar hannu, gaza damƙa ko riƙo da hannu, sagewa, zogi ko ciwo bayan allura a dantse, tuntuɓi likitan fisiyo a yau.

AMFANIN SHAN RUWA DA SAFIYA KAFIN ACI KOMAI:;Shan ruwa da zarar an tashi da safe yana da matukar amfani ga lafiyar dan a...
12/09/2022

AMFANIN SHAN RUWA DA SAFIYA KAFIN ACI KOMAI:;

Shan ruwa da zarar an tashi da safe yana da matukar amfani ga lafiyar dan adam. masana fannin kimiyya sunyi bincike akan hakan. masu bibiyar mu a wannan gida mai albarka saiku biyoni sannu ahankali donjin amfaninsa. Yana maganin:

1.ciwon kai
2.ciwon jiki
3.daidaita tsarin bugun zuciya
4.amosanin gabbai
5.farfadiya
6.daidaita jikin da yawuce kima
7.asthma
8.ciwon koda
9.cutukan dake cikin fitsari
10.ciwon suga.....

Kadan daga ciki kenan...

Lafiya uwar jiki

Alamun Ciwon Siga Shida Da Mutane Ke Buris Da Su. Ana yi wa Ciwon Siga take da "ga ƙoshi; ga kwanan yunwa". Saboda akwai...
11/09/2022

Alamun Ciwon Siga Shida Da Mutane Ke Buris Da Su.

Ana yi wa Ciwon Siga take da "ga ƙoshi; ga kwanan yunwa". Saboda akwai wadataccen siga(gulukos) a cikin jini amma ƙwayoyin halitta, wato "cells", sun gaza samun sigan wanda kuma shi ne makamashin da ƙwayoyin halittar ke ƙonawa domin cigaban rayuwa.

Sinadarin "insulin" wanda matsarmama ke samarwa shi ne ke shigar da sigan daga cikin jini zuwa cikin ƙwayoyin halitta. Wato sinadarin "insulin" shi ne ke daidaita siga a jikin mutum. Idan "insulin" bai yi aikinsa ba, to siga zai hauhawa a cikin jini fiye da ƙima. Wato ga sigan a cikin jini amma "insulin" ya gaza shigar da shi daga cikin jini zuwa cikin ƙwayoyin halitta. Wannan shi ne "ga ƙoshi; ga kwanan yunwa" kenan!

A taƙaice dai, ciwon siga na afkuwa sakamakon rashi ko ƙarancin "insulin" ko kuma gazawar ƙwayoyin halitta wajen amfani da shi yadda ya kamata a jiki.

Alamomin ciwon siga sun haɗa da:

1. Yawaita fitsari akai-akai, musamman da daddare.

2. Matsananciyar ƙishirwa / shan ruwa fiye da ƙima.

3. Rama / raguwar nauyin jiki

4. Jin matsananciyar yunwa.

5. Ƙan-jiki, wato jinkirin warkewar rauni ko miki a jiki.

6. Saurin harbuwa da ƙwayoyin cutuka, musamman masu haddasa cutukan hanyoyin fitsari.

Tuntuɓi likita da zarar ka fara fuskantar waɗannan alamomi.

Amfanin Kubewa Ajikin Dan Adam:Mutane da dama suna amfani da kubewa a matsayin miya ba tare da sanin tarin amfanin ta ga...
11/09/2022

Amfanin Kubewa Ajikin Dan Adam:

Mutane da dama suna amfani da kubewa a matsayin miya ba tare da sanin tarin amfanin ta ga jikin dan Adam ba.

Bincike ya nuna kubawa na dauke da sinadarai kaman haka:

Calories
Carbs
Protein
Fiber
Magnesium
Folate
Vitamin A
Vitamin C
Vitamin K
Vitamin B6

Wassu sinadaran sun hada da sinadaran kare cells da kuma lalata ta guba a jiki kaman:

- polyphenols
- flavonoids
- isoquercetin
- Lactin

Ga kadan daga cikin amfanin kubewa a jikin dan Adam:

1- Kara Karfin Gani.
Kubewa yana taimaka wajen kara karfin gani. Ko mai karatu ya san dalili, sabida yana dauke da sinadaran Vitamin A da carotene.

2- Yana taimakawa masu juna biyu:
Kubewa yana matukar taimakawa masu juna biyu wajen inganta lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki, domin kubewa na kunshe da dimbin sinadaran Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki da. lafiyarsa.

3- Yana rage hadarin kamuwa da ciwon koda.
Wani bincike da aka gudanar a jami’ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da cewa, yawan amfani da kubewa na matukar rage hadarin kamuwa da ciwon koda.

4- Yana taimakawa masu cutar Asthma.
Kubewa yana maganin cutar wahala wajen fitar da numfashi wato Asthma, saboda sinadarin Vitamin C da ke tattare ta ita.

5- Ana amfani da kubewa wajen maganin cutar siga wacce ta zamo ruwan dare a tsakanin al'umma a yanzu. Tana dauke da sinadarin fibre a cikinta, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan siga a cikin jikin dan Adam.

6- Inganta Lafiyar Uwar Hanji.
Kubewa na inganta lafiyar hanji da tumbi ta hanyar fitar da sanadaran da ka iya lahani ga hanji ko tumbin. Kuma sakamakon haka ne, ta ke maganin kumburi da cushewar ciki wanda kuma ke rage karfi ciwon siga ko ma maganinsa.

7- Kubewa Na Kara Karfin Garkuwan Jiki.
Yawan amfani da kubewa na kara bunkasa tare da karfafa garkuwar jikin dan-adam. akwai wasu Sinadarai dake cikin kubewa masu matukar amfani a garemu da s**a hada da, Bitamin C da 'Calcium' da 'Magnesium' dake taimaka wa wajen yaki da cututtu.

Daman ba iya mai juna biyu nankarwa ke fitowa ba?Duba Abubuwa 10 Da S**a Kamata Ka Sani Game Da Nankarwa.1. Nankarwa ala...
10/09/2022

Daman ba iya mai juna biyu nankarwa ke fitowa ba?

Duba Abubuwa 10 Da S**a Kamata Ka Sani Game Da Nankarwa.

1. Nankarwa alama ce ta talewar fata. An fi ganinta galibi a tsatstsaye a kan fata. Kalar nankarwa ya dogara ga kalar fatar mutum.

2. Akwai shimfiɗu uku da s**a haɗu s**a samar da fata. A likitance, nankarwa na faruwa sakamakon talewar shimfiɗar fata ta biyu.

3. Galibi ta fi fitowa a kan fatar ciki. Sai dai wasu lokutan tana bayyana a kan fatar cinyoyi, nonuwa, ƙugu, damatsa da sauransu.

5. Nankarwa aba ce ruwan dare. Kuma tana iya fito wa kowa, maza da mata, babba da yaro, ba sai mata masu juna biyu kawai ba.

6. Waɗanda suke da sabuban fitowar nankarwa sun haɗa da:

i. juna biyu: Kaso 8 cikin 10 na masu juna biyu nankarwa na fito musu.

ii. waɗanda suke cikin shekarun balaga.

iii. Wanda ya rame ko ya yi ƙiba nan da nan.

7. Ga masu juna biyu, nankarwa na bajewa ko ta tsutstsuke bayan haihuwa.

8. Wasu nau'in mayukan shafawa suna iƙirarin magance nankarwa, sai dai babu ƙwararan dalilai da s**a tabbatar da iƙirarin nasu.

9. A likitance, nankarwa, musamman ga masu juna biyu, ba ta da wata matsala. Sai dai idan akwai ƙaiƙayi ko kuma damuwa game da munin da nankarwar ke haifarwa ga fata, za a iya tuntuɓar likitan fata.

10. Har wa yau, a tuntuɓi likita idan nankarwa ta yi faɗi sosai tare da bayyanar tarun kitse / teɓa a ciki, wuya da ƙirji domin hakan na iya zama alamun wata cutar daban.

10/09/2022

Illolin cire 'yar-wuya ga lafiyar jarirai.

Al'adar cire 'yar-wuya ga jarirai wato "traditional uvulectomy" a turancin likita, daɗaɗɗiyar al'ada ce a ƙasar Hausa. Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa abin da Bahaushe ke cewa 'yar-uwa, wacce ke da sifar tsiro ko kuma kan yatsa, a can cikin baki daga sama, wani rumbu ne da ke ɗauke da ƙwayoyin garkuwar jiki domin yaƙar cutuka daban-daban. Sai dai, al'adar Bahaushe ta gudana kan cire 'yar wuyan ga jarirai tsawon zamani, musamman a ƙasashen Hausa da kuma wasu ƙasashen Afrika.

Malam Bahaushe dai yana ganin cewa 'yar-wuyan wani tsiro ne da zai iya cutar da jariri yayin shayarwa ko kuma ya kawo ciwon maƙogaro can gaba. Sai dai, wannan al'ada ta yi baram-baram da binciken kiwon lafiya a yau, a maimakon haka ma, cire 'yar-wuyan na iya jefa lafiyar jariri cikin haɗura kamar haka:

1. Yi wa jariri mummunan miki/rauni a ganɗa.

2. Ciwo tare da kumburi a ganɗa.

3. Ɓallewar jini, musamman ga jariran da kan zo da larurar tsinkewar jini bayan miki.

4. Shigar ƙwayoyin cutuka ta hanyar wuƙa ko askar da aka yi amfani da ita wajen cire 'yar-wuyan, ko kuma shigar ƙwayoyin cutuka cikin raunin da aka yi bayan cire 'yar-wuyan.

5. Shigar ƙwayar cuta mai janyo ƙaƙƙamewa ko kakkafewar jiki, wato "tetanus" a turance, saboda haɗarin shigar cutar ta hanyar amfani da aska mai tsatsa.

6. Matsalar shayarwa — saboda raunata hanƙa, jariri kan fuskanci wahalar haɗiyar nono yayin shayarwa.

Daga ƙarshe, likitoci sun tabbatar da cewa barin 'yar-wuya ba shi da wata matsala ga lafiyar jariri, kuma shi ne ma mafi alfanu ga lafiyar jaririn. Kuma cire ta na iya jefa lafiyar jariri cikin haɗuran da aka ambata a sama.


Address

Mambila Avenue, Sunday Awoniyi New GRA Bauchi
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Allurar cikin ruwa Albarka Radio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram