Cibiyar Hasheer Herbal & Islamic Medicine Research Center

Cibiyar Hasheer Herbal & Islamic Medicine Research Center Muna hada magunguna na dukkan cututtuka sannan muna jinyar kowani irin matsala da yardan Allah

Bissmillah!Yan’uwa masu bibiyar mu,kwana biyu na ɗan yi shiru saboda aiki, amma yau Alhamdulillah mun dawo da ɗan darasi...
29/10/2025

Bissmillah!
Yan’uwa masu bibiyar mu,kwana biyu na ɗan yi shiru saboda aiki, amma yau Alhamdulillah mun dawo da ɗan darasi mai amfani.

A yau zanyi magana kan cutar tari da zazzabin kirji.
Akwai masu yawan tari musamman da dare, kirji yana cunkushewa, numfashi yana wahala.

Magani:
A haɗa ganyen lemongrass (fari tsamiya), habbatussauda, da ɗan zuma.
A dafa, a sha ɗumi safe da yamma na kwana 5–7.
In Sha Allah, tari zai daina, kirji ya buɗe, jiki ya warke.

CIBIYAR HASHEER HERBAL
muna da magani ga kowacce irin cuta In Sha Allah:
Ulcer, hawan jini, suga, matsalar fitsari, farji, maza da mata, da sauran su.

> Tuntube mu don neman lafiya ta gaskiya, Allah ne Mai warkarwa. 🌿

Dr Asheer Yusuf Sambo

Domin Tambaya ko Neman karin Bayani za'ayi tuntubarmu ta Wadannan Hanyoyi

07048862426
09029510644

29/10/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Bilal Yusuf Bingi, Iliya Musa Inuwa, Nusaiba Yusuf

08/10/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Salisu Balkisu, Kareematu Nuruddeen

Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatu,shin ko kunsan Cewa dankalin turawa Yana magance matsalar cutar olsa?Idan ka...
19/09/2025

Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatu,shin ko kunsan Cewa dankalin turawa Yana magance matsalar cutar olsa?

Idan kasamu dankalin turawa matsakaici Guda daya seka wankeshi sosai sannan kamarkadeshi seka Samu zuma Mai kyau ko Madara kamar maidaicin kofi kazuba markaddan dankalin aciki

Kashanye Wannan hadin Cikin kwanaki uku,zakayita haka har seka Allah yakawo Maka sauki,

Domin neman Karin Bayani ko tambaya zaku iya tuntubarmu ta Wadannan Hanyoyi

Dr Asheer Yusuf Sambo 󱢏?07048862426
09029510644

🟣 HORASWA TA MUSAMMAN GA 'YAN UWA MATA 🟣Kin taɓa fuskantar matsaloli irin su:✨ Matsalolin mata da ake taɓuwa dasu a rayu...
20/08/2025

🟣 HORASWA TA MUSAMMAN GA 'YAN UWA MATA 🟣

Kin taɓa fuskantar matsaloli irin su:
✨ Matsalolin mata da ake taɓuwa dasu a rayuwa
✨ Matsalolin al’ada (period) kamar zubar jini fiye da kima, ciwon mara, ko rashin daidaiton haila
✨ Matsalolin sanyi (infection) da ke damun mata, da hanyoyin magance su

To ki kwantar da hankalinki, akwai horaswa ta musamman online da za ta taimaka miki wajen:
✅ Fahimtar dalilan wadannan matsaloli
✅ Koyi hanyoyin gargajiya da na zamani wajen magance su
✅ Karin ilimi da zai taimaka wajen kare kanki da lafiyarki

📌 Wannan horaswa za ta kasance online don sauƙin kowa.

💰 Kudin shiga:

₦3,000 ga zallar horaswa

₦5,000 idan kina son Certificate a ƙarshe

👉 Kada ki bari wannan damar ta wuce ki. Lafiya na buƙatar kulawa tun kafin ta lalace!

DOMIN NEMAN KARIN BAYANI

🤳 PHONE NUMBER
07048862426

🤳 PHONE NUMBER
0706 464 9013

14/08/2025

Wa alaikumus salam
Tambaya ce daga gare ni:
Kawata ta yi allurar family planning mai kare haihuwa na wata uku (3 months injection), sati ɗaya da ta gabata. Yanzu ta shiga wata bakwai tana da ciki. Tambayar mu ita ce, shin za mu iya tunanin watakila tagarin ciki ne (twin pregnancy) ko kuwa akwai wata matsala?

Nau’in family planning ɗinta na wata uku ne.

Bayanin likitanci:
Allurar Depo-Provera ko irin ta, ana yin ta ne kowane watanni uku don kare daukar ciki. Idan aka yi ciki a lokacin da ake amfani da ita, hakan na iya zama saboda:

1. An yi allurar bayan an riga an ɗauki ciki — wato lokacin yin allurar mace tana da ciki amma ba ta sani ba.

2. An makara wajen yin allura ta gaba — tazara ta wuce kwanaki 90–100 kafin a yi sabuwa.

3. Rashin aiki yadda ya kamata (rare side effect) — wasu lokuta jiki baya amsawa daidai.

Yin ciki bayan irin wannan allura ba lallai ba ne ya nuni da ciki tagari (twin pregnancy). Twin pregnancy yawanci yana faruwa ne saboda kwayoyin halitta ko wasu abubuwa, ba saboda family planning.

Idan kawarki na da ciki yanzu, ya kamata ta:

Je asibiti a tabbatar da tsawon cikin ta (ta hanyar ultrasound).

Duba lafiyar jariri/jarirai.

Nemi shawarwarin likita game da yadda za ta ci gaba da kula da kanta,
Kokuma ta nemi family planing na maganin gargajiyya Mai kyau domin wasu lokuta ana iya samun ƙarancin jini ko wasu matsaloli idan aka yi ciki tare da family planning.

30/07/2025

Amfanin Dabino Ga Lafiyar Dan-adam

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Shi dai wannan dan itaciya ba bakon abu ne ba ga masu karatu. Kuma mun san cewa shi dabino ya sha bam-bam wajen girmansa, launinsa da kuma dandanonsa (zakinsa). Ana cin danye ko busasshen dabino,gwargwadon bukata. Ko dai a wanne irin yanayi akai amfani da shi ya na dauke da sanadarai masu matukar muhimmanci ga lafiya.

Mafi yawan mutane suna cin dabino ne don zakinsa, ba tare da sanin amfaninsa ga lafiyarsu ba. To sai dai dabino na da matukar fa'ida ga lafiyarmu.

Binciken masanan zamani ya nuna yawan cin dabino ga maza yana kara musu karfin sha'awa da kuma karfin mazakuta. Wasu masana sun shadawa jaridar Premium Times cewa yin amfani da dabino ga maza na kara musu karfin sha'awa da kuma karfin mazakuta. Dr Aminu Kareem ya shaidawa jaridar cewa, yawan cin dabino ga maza da ke da matsalar gamsar da iyali, na iya magance musu wannan matsala.

Saboda haka ne, mu ke son amfani da wannan dama don kawowa masu karatu irin dibim baiwar da ALLAH(S.W.T.) yai wa wannan dan itaciya ga lafiyar al'umma.

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

1. Karfin Mazakuta.


Kamar yadda muka fara ambatawa a sama, bincike ya nuna cewa dabino na kara karfin maza. Don samun sakamako mai kyau, a zuba dabino cikin nonon awaki ya kwana, sai a nike shi a hada da nonon da aka cire shi daga ciki a hada da zuma a sha. Hakanan a samu dabino kamar cikin tafin hannu,sai a cire kwallon a zuba a ruwa ya samu kamar awa biyu ko uku,a markade shi a zuba madara gwangwani daya da zuma cokali uku a sha sau daya a kullum.

2. Cushewar Ciki.

Dabino yana magance cushewar ciki, saboda yana kunshe da sinadarin da ake kira "Soluble fibre" a turanci. Shi kuwa wannan sinadari yana taimakawa wajen kewayawar abinci a cikin hanji cikin sauki.

Yadda za'a samu ingancin magance wannan matsala,a zuba dabino guda bakwai ko tara cikin ruwa su kwana a ci da safe.

3. Karfin kashi.

Saboda dabino na kunshe da sanadaran selenium, manganese,

YADDA ZA KA GANE AZZAKARINKA YANA DA LAFIYA .Azzakari mai lafiya yana da alamomi da za ka iya lura da su kanka. Idan ka ...
26/05/2025

YADDA ZA KA GANE AZZAKARINKA YANA DA LAFIYA .

Azzakari mai lafiya yana da alamomi da za ka iya lura da su kanka. Idan ka cika waɗannan , to ka godewa Allah, zakarinka yana da koshin lafiya:

1. Tsayuwa da ƙarfi da sassauci.

Idan azzakarinka yana tashi da karfi lokacin da kake buƙatar jima’i, kuma yana sassautawa bayan gamsuwa — alama ce ta lafiyayyen tsarin jini da jijiyoyi.

2. Fitar maniyyi mai kauri da ƙarfi.

Maniyyinka yana fita da kauri, ba ruwa kamar famfo, kuma yana zuwa da jin daɗi?
Wannan yana nuna garkuwar azzakari da lafiya ta haihuwa.

3. Sha'awa tana zuwa yadda ya kamata.

Kana jin sha’awa a lokaci-lokaci ba tare da matsin lamba ba?
Ba yawa, ba ƙaranci — alama ce cewa hormones ɗinka suna aiki daidai.

4. Babu zafi ko ciwo lokacin fitsari ko jima'i.

Idan kana fitsari ko jima’i cikin kwanciyar hankali, ba tare da radadi ko ƙaiƙayi ba, to baka da cututtukan da ke shafar zakari.

5. Babu fitar ruwa ko wari daga zakari.

Idan baka ganin wani ruwan fari, rawaya ko wari daga zakari — wannan babban

MAGANI A GONAR YAROBincike ya tabbatar da Rake yana da matukar amfani ga jikin Dan Adam kamar haka:1- Rake Yana Taimaka ...
08/05/2025

MAGANI A GONAR YARO

Bincike ya tabbatar da Rake yana da matukar amfani ga jikin Dan Adam kamar haka:

1- Rake Yana Taimaka ma HANTA.
2- Shan Rake Yana Maganin CIWON KODA.
3- Shan Rake Yana Saukar da ZAZZABI.
4- Shan Rake Yana Maganin Matsananciyar MURA.
5- Shan Rake Yana Saukar da HAWAN JINI.
6- Shan rake Yana taimaka ma kwakwalwar Dan'adam.

Domin Shi sukarin da yake cikin Rake Yana dauke da sinadarin FOLIC ACID
6- Yana da amfani ga namiji me matsalar Zafin Fitsari.
7- Haka kuma yana da matukar muhimmanci ga mace mai juna biyu.

Dan Allah Yan uwa kuyi Sharing Dan Yan uwa su amfana.

17/04/2025

IDAN KANA NAMIJI KUMA KANA DA HAWAN JINI KASAMU INGANTACCEN MAGANIN MUSULUNCI KO NA GARGAJIYA YAFI MAKA ALKHARI GA SYSTEM DINKA 👌

Address

Bayan Maternity Sabon Titin Bakaro
Bauchi

Telephone

+2347048862426

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Cibiyar Hasheer Herbal & Islamic Medicine Research Center posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Cibiyar Hasheer Herbal & Islamic Medicine Research Center:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram