Qafilatul muhabbah Dass Local Government

Qafilatul muhabbah Dass Local Government Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Qafilatul muhabbah Dass Local Government, AIDS Resource Center, Gidan Sarkin malamai, unguwan wakili Dass, Bununu Dass.

24/10/2025

Ziyaran mako mako daga masalacin Na'ibi limami Dass

24/10/2025
ASHEKARAR DATA GABATA.YAUMUL AYTAM NA QAFILATUL MAHABBAH DASS LOCAL GOVERNMENT BRANCH. 29/09/2024.A safiyar yau ne wanna...
29/09/2025

ASHEKARAR DATA GABATA.

YAUMUL AYTAM NA QAFILATUL MAHABBAH DASS LOCAL GOVERNMENT BRANCH. 29/09/2024.

A safiyar yau ne wannan gidauniya ta Qafilatul Mahabbah reshen wannan karamar hukuma ta Dass, ta sami damar gabatar da wannan rana mai taken YAUMUL AYTAM, inda a irin wannan rana ne ta saba ciyar da yara marayu kanana, inda a bana ta sami nasarar ciyar da marayu kimanin guda saba'in (70) wanda s**a hada maza da mata harma da yara wad'anda s**a daata.

Ayayin gudanarwan, an sami nasarar halartan manya bakin da s**a hada da masu unguwanni, malamai, harma da shi kansa Sarkin malaman na Dass, inda ayayin jawabinsa ya bayyana godiyarsa sannan yayi kira ga mabukata dama sauran al'ummah wajen koyi da irin wadannan ayyuka na wannan gidauniya ta Qafilatul Mahabbah.

Shi ma anasa Jawabin, Mal. Yakubu Hassan Balif shugaban wannan gidauniya ta Qafilatul Mahabbah reshen wannan karamar hukuma, ya bayyana farin cikinsa dakuma godiyarsa ga ubangiji, inda ya sake mika godiyar ga dukkan mahalarta musamman wadanda s**a taimaka wajen gudanuwar wannan hidima, dama sauran membobi da shuwagabannin committees na wannan gidauniya mai albarka, inda daga karshe yayi Addu'ar ubangiji Allah ya saka wa kowa da mafificin sakayya yakuma kaimu na badi da rai da lafiya.

QAFILATUL MAHABBAH MEDIA TEAM, DASS LGA. 29, Sep. 2024.

ALHAMDULILLAHI MÀSHA ALLAH.Yayinda tawagar gamayyar wannan gidauniya ta Qafilatul Mahabbah na shiyar Bauchi ta kudu, s**...
22/09/2025

ALHAMDULILLAHI MÀSHA ALLAH.

Yayinda tawagar gamayyar wannan gidauniya ta Qafilatul Mahabbah na shiyar Bauchi ta kudu, s**a kai ziyara gidan Maulana Sheikh Tahir Usman Bauchi (RTA), inda s**a sami tarban wakilin Maulana Sheikh Mal. Hadi Babban jika ga Sheikh. tabbas Sheikh yayi murna da wannan ziyara, inda shima yayi addu'a da fatan alkhairi ga wannan gidauniya.

DAFATAN UBANGIJI ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI YAKUMA CIGABA DA TALLAFAWA WA WANNAN GIDAUNIYA.

MÀSHA ALLAH II.Yayinda tawagar gamayyar ressan gidauniyar Qafilatul Mahabbah ta shiyyar Bauchi ta kudu ta ziyarci gidan ...
22/09/2025

MÀSHA ALLAH II.

Yayinda tawagar gamayyar ressan gidauniyar Qafilatul Mahabbah ta shiyyar Bauchi ta kudu ta ziyarci gidan Mal. Balarabe Isah, inda ta kai masa gaisuwar ta'aziya na rasuwar ɗiyarsa dakuma neman tabarruki ga wannan gidauniya dama waɗannan yara marayu, tabbas mal. yaji daɗin wannan ziyara, inda yayi addu'ar da fatan alkhairi ga wannan gidauniya.

DAFATAN UBANGIJI ALLAH YA KAIMU NA BADI RAI DA LAFIYA.

MÀSHA ALLAH.Yayinda tawagar gamayyar ressan gidauniyar Qafilatul Mahabbah na shiyar Bauchi ta kudu s**a kai ziyara gidan...
22/09/2025

MÀSHA ALLAH.

Yayinda tawagar gamayyar ressan gidauniyar Qafilatul Mahabbah na shiyar Bauchi ta kudu s**a kai ziyara gidan Dr. Zubairu Madaki (shugaban JIBWIS na jihar Bauchi), bayan kammala walima da wasanni da marayu, Dr. yaji daɗi sosai, inda ya shigar da wannan tawaga izuwa maktabarsa (Library) don gani dakuma sanya albarka.

DAFATAN UBANGIJI ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI YAKUMA KAIMU NA BADI.

GAMAYYAR RESSAN GIDAUNIYAR QAFILATUL MAHABBAH NA SHIYAR BAUCHI TA KUDU SUN GABATAR DA RANAR JINKAI NA MARAYU (YAUMUL MAR...
21/09/2025

GAMAYYAR RESSAN GIDAUNIYAR QAFILATUL MAHABBAH NA SHIYAR BAUCHI TA KUDU SUN GABATAR DA RANAR JINKAI NA MARAYU (YAUMUL MARHAMA).

Ayau ne gamayyar ressan gidauniyar Qafilatul Mahabbah na shiyar Bauchi ta kudu s**a gabatar da ranar jinkai na marayu acikin garin Bauchi, inda taron ya gudana karkashin kulawar kodinetotin ressan shiyar amatsayinsu na wakilan shugaban gidauniyar na kasa prof. Ibrahim Ahmad Maqari (Chief Imam National mosque Abuja)

Yayin gabatar da taron, ressan gidauniyan da s**a haɗa da kananan hukumomin DASS, TAFAWA BALEWA, TORO, BAUCHI, KIRFI, ALKALERI sun sami damar ziyartar cibiyar wasanni na yara mai suna CINDRELLA MINI PARK dake kusa da Jifatu Mall, inda s**a gabatar da gagarumin walima na kayan makulashe da shaye shaye, inda daga bisani s**a gabatar da wasannin lilo, calili, da sauran nau'ukan wasannin na yara da suke haifar da nishaɗi da kuma ɗebe kewa.

Daga karshe gidauniyar ta sami gabatar da ziyarce ziyarce izuwa ga gidajen wasu maluma don neman albarka dakuma tabarruki na shawarwari, inda s**a ziyarci gidajen da s**a jaɗa da:-

1- Gidan Maulana Sheikh Tahir (RTA)
2- Gidan Mal. Balarabe Isah
3- Gidan Dr. Zubairu Madaki (shugaban JIBWIS na jihar Bauchi), Inda duka malaman s**a nuna farin ciki kana s**ayi addu'a na fatan alkhairi ga jagoran wannan gidauniya na kasa da sauran dukkanin shuwagabanni da membobi na ressan wannan gidauniya.

DAFATAN UBANGIJI ALLAH YA SAKA WA KOWA DA ALKHAIRI YAKUMA KAIMU NA BADI DA RAI DA LAFIYA.

QAFILATUL MAHABBAH
MEDIA TEAM ✍️ ✍️ ✍️
21, SEPTEMBER, 2025.

ANSAMI CANJIN RANA DAGA YAU ZUWA GOBE LAHADI ( TAFIYA ZIYARA DA MARAYU) ZUWA FILIN SHAKATAWA DA WASANNI NA CINDRELLA MIN...
20/09/2025

ANSAMI CANJIN RANA DAGA YAU ZUWA GOBE LAHADI ( TAFIYA ZIYARA DA MARAYU) ZUWA FILIN SHAKATAWA DA WASANNI NA CINDRELLA MINI PARK BAUCHI.

Amadadain wannan gidauniya mai albarka na Qafilatul Mahabbah, muke farin cikin sanar da ɗaukacin al'ummar musulmai cewa ansami canjin rana don gabatar da ranar jin daɗin marayu (YAUMUL AYTAM), inda wasu dalilai masu karfi yasa aka dage tafiyar daga yau asabar zuwa gobe lahadi idan Allah ya kaimu.

za'a tashi domin tafiyar ne kofar Makarantar Nooron Ala Noor dake bayan fada, inda anan kowa zaizo da marayansa don wannan tafiya.

GURAREN DA ZA'A ZIYARTA SUN HADA DA:-

1- Gidan Maulana Sheikh Tahir Usman Bauchi RTA (Ziyarah)
2- Zawiyyar Mal. Balarabe Isah ( Ta'aziya)
3- Gidan Dr. Zubairu Madaki ( Ziyara da godiya)
4- CINDRELLA MINI PARK DAKE TITIN JIFATU MALL BAUCHI, inda anan za'a gabatar da walimah da kuma wasanni don jin dadin marayu.

DAFATAN UBANGIJI ALLAH YA KAIMU YAKUMA SA MU GABATAR DA WANNAN ZIYARA LAFIYA.

QAFILATUL MAHABBAH DASS
MEDIA TEAM ✍️✍️✍️✍️
20, SEPTEMBER, 2025.

RANAR JINKAI (YAUMUL MARHAMA) NA QAFILATUL MAHABBAH DASS LOCAL GOVERNMENT BRANCH.Ajiya ma kamar kowace shekara wannan gi...
20/09/2025

RANAR JINKAI (YAUMUL MARHAMA) NA QAFILATUL MAHABBAH DASS LOCAL GOVERNMENT BRANCH.

Ajiya ma kamar kowace shekara wannan gidauniyar ta Qafilatul Mahabbah reshen karamar hukumar Dass, ta sami damar bin sahun takwarorinta dake faɗin ƙasar nan wajen gabatar da wannan rana ta jinkai, inda a irin wannan ranar ne ta saba gabatar da ziyarce-ziyarcen asibitoci don gaisuwa da nuna tausasawa ga majinyata cikin bayyana murna ta munasabah da zagayowar wannan wata da aka haifi fiyayen halitta ANNABI MUHAMMAD Sallallahu alaihi Wasallama.

Ayayin ziyarar na bana, gidauniyar ta samu damar ziyartar Asibitin ALHAYAT CLINIC AND MATERNITY dake da matsuguni a unguwar TAKKWANGEL TUDUN WUS DASS, inda ta sami kyakkyawan tarba da rakiya daga jami'an asibitin, wanda hakan ya bada dama aka gabatar da ziyarar cikin tsari da bin hakkokin kare mutunci ta ɗan adam musamman ayanayi na rashin lafiya.

Daga ƙarshe hukumar Asibitin ta yaba da ƙoƙarin wannan gidauniya bisa irin wannan ziyara data kawo dakuma ɗan tallafin data bayar ga majinyatan, inda ta mika godiyarta amadadin dukkan majinyatan nata, kaana tayi ƙira ga sauran kungiyoyi na addini dama waɗanda ba na addini ba wajen koyi da irin waɗannan ayyuka na jinkan musamman duba da hali na matsi da ake ciki.

DAFATAN UBANGIJI ALLAH YA SAKA YA KUMA KAIMU NA BAƊI DA RAI DA LAFIYA.

QAFILATUL MAHABBAH
MEDIA TEAM ✍️✍️✍️
20, SEPTEMBER, 2025.

RANAR JINKAI DA RANAR MARAYU NA GIDAUNIYAR QAFILATUL MAHABBAH.Gidauniyar Qafilatul Mahabbah reshen karamar hukumar Dass ...
19/09/2025

RANAR JINKAI DA RANAR MARAYU NA GIDAUNIYAR QAFILATUL MAHABBAH.

Gidauniyar Qafilatul Mahabbah reshen karamar hukumar Dass take farin cikin sanar da gabatar da ranar jinkai ( Yaumul marhama), dakuma ranar marayu (Yaumul Aytam), inda zata ziyarci asibitoci don gaida marasa lafiya da kuma ciyar da marayu da kaisu cibiyar wasanni da buɗe ido. waɗannan ranaku guda biyu zasu gudana ne kamar haka:-

1- YAUMUL MARHAMA (RANAR JINKAI):
RANA: Yau juma'a 19/09/2025.
LOKACI: Bayan Sallahr juma'a
WURI: Alhayat clinic and maternity takwngel Dass.

2- YAUMUL AYTAM( RANAR MARAYU):
RANA: Gobe asabar 20/09/2025.
LOKACI: tara na safe
WURI: Cikin Garin Bauchi, Bauchi state.

DIRECTOR MEDIA TEAM ✍️
QAFILATUL MAHABBAH DASS BRANCH.

Address

Gidan Sarkin Malamai, Unguwan Wakili Dass
Bununu Dass

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qafilatul muhabbah Dass Local Government posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram