10/11/2025
Menene yanar ido (Cataract).
Yanar ido wato cataract cuta ce ta ido da ke haifar da gajimare a ruwan tabarau na ido wanda ke jawo kankantar gani, dishi-dishi, ko matsaloli wajen ganin abubuwa musamman da dare. Yana tasowa a hankali, yawanci yana da nasaba da tsufa ko wasu dalilai kamar rauni ko hasken radiation.
Hanyar kare kai daga yanar ido ta hada da amfani da tabarau masu kare ido daga rana, saka hula mai fadi, cin ganyayyaki da 'ya'yan itatuwa masu gina jiki, gujewa shan taba, da kula da lafiya gaba daya.
Idan cataract ya riga ya ci gaba, hanya mafi tasiri ita ce tiyata inda ake cire ruwan tabarau mai gajimare a maye gurbinsa da sabon na'ura mai kyau domin dawo da hangen nesa.
Menene Yanar Ido (Cataract).?
Cataract wani yanayi ne inda ruwan tabarau na ido ke rufe gajimare, wanda ke haifar da duhun gani da matsaloli wajen ganin abubuwa a hankali.Yana iya shafar ido daya ko duka biyu, kuma alamomin sun hada da ; ɓata launi, diahi-dishi, hangen abu, sai rabe su zama biyu, da matsala wajen gani da rana ko dare.
Cataract sanadi ne na manyan matsalolin makanta a duniya, musamman ga masu shekaru, mata, da wasu yankuna kamar Afirkan mu.
>Hanyoyin Kare Kai Daga
Yanar Ido;
1. Amfani da tabarau masu kare ido daga hasken ultraviolet na rana.
2. Sanya hula mai fadi don kariya daga hasken rana kai tsaye.
3. Kara cin ganyayyaki da 'ya'yan itace masu sinsadaran antioxidants.
4. Gujewa shan taba da rage shan abubuwan da ke dauke da caffeine sosai.
5. Gudanar da lafiyar jiki gaba daya, kamar rage ciwon suga da kuma kula da hawan jini.
6.Magani da Tiyatar Cataract. Idan yana da tsanani, tiyata ce hanyar magancewa inda suke cire ruwan tabarau mai gajimare (cataract) a ido. Ana amfani da hanyoyi kamar Phacoemulsification da Extracapsular Surgery.
A Phacoemulsification, ana karya gajimaren ruwan tabarau ta na'ura kafin cirewa, sannan a saka ruwan tabarau na wucin gadi.Wannan tiyata na da sauri kuma mai inganci wajen dawo da hangen nesa.
Wannan bayanin na iya taimakawa wajen fahimtar yanar ido da yadda za a kare kai da kuma magance matsalar idan ta taso. Mu hadu a rubutu na gaba.