18/10/2025
Bin Inuwa
Jamila ta gama jera kayan miya a madafi tana bin waƙarta Gwanka da ke tashi daga wayarta a hankali, lokacin da ƙawarta, Kande, ta shigo falon ba ko sallama. Kande ta zauna a kan kujera ta miƙe ƙafafuwanta, idanunta na yawo a cikin gidan. "Ke kuwa har yanzu kina cikin wannan aikin hidimar? Kina bata lokacinki wajen faranta wa ɗa namiji rai," Kande ta faɗa tana latsa wayarta.
Jamila ta fito daga kicin tana murmushi. "Kande kenan, ai wannan shi ne jin daɗin auren."
Kande ta kyalkyale da wata muguwar dariya. "Jin daɗi? Ko ba jin daɗi ba? Ke yanzu fa 'yar aiki ce ba mata ba. Dubi Zulai, jiya mijinta ya siyo mata sabon leshi na dubu hamsin. Ke fa? Tsoffin zaAnuwanki ne dai har yanzu tun na lefe. In ba ki buɗe ido ba fa, wallahinza a bar ki a baya, sai dai kiji wasu suna baza vapacity amma ba ke ba."
Wannan magana ta zama kamar tsinke da aka soka a zuciyar Jamila. Tun daga wannan rana, kowace shawarar Kande bi take kawai kai tsaye ba taree da da yin wani dogon tunani ba. Idan mijinta, Aliyu, ya dawo gida, a maimakon ta tarbe shi da fara'a, sai ta fara korafi. "Aliyu, wayata ta tsufa," ko "Anko na bikin wance sa wance fa ya fito, amma ni ba ni da ko sisi." Gidan da a baya yake cike da ƙauna da kwanciyar hankali, yanzu ya zama filin gunaguni da hayaniya. Aliyu ya rasa inda zai sa kansa, domin Jamila ta sauya gaba ɗaya daga matar da ya sani a baya.
Wata rana, Jamila ta shirya zuwa gidan Kande ba tare da ta sanar da ita ba, don su je kasuwa tare. Tana gab da ƙwanƙwasa ƙofa, sai ta ji muryar Kande tana waya da wata ƙawarsu. "Waccan sakaryar, Jamila? Ai na kusa gamawa aikinta na koma kan wata ballagazar kuma. Na koya mata yadda ake wulaƙanta miji. In ta fito daga gidan, sai mu haɗa ta da Alhaji Bala kawai ai kin dai gane." Taɓsɓeƙe da wata dariya irin ta riƙaƙƙun ƴan duniya.
Jamila ta ja da baya kamar wacce aka watsa wa ruwan zafi. Kalmomin da ji daga bakin kande a wayar da take wasu ma ba za su faɗu ba. Kalmomin s**a soke ta kamar kibiya. Ta juya a guje ta koma gida, hawaye na bin fuskarta. Ta shiga gidanta, ta kalli yadda ya zama babu wani armashi saboda halinta. Ta durƙusa a tsakiyar falon tana kuka, tana nadamar bin inuwar da ta kai ta ga halaka. A wannan ranar, ta gane cewa ba kowace ƙawa ce abokiyar tafiya ba, kuma zaɓin abokai na iya zama ginshikin farin cikin gida ko kuma rushewar sa.
Idan ke ce ki ka ji batun Kande, wane mataki za ki ɗauka a kanta? Sai mun ji amsarki a comment: 👇👇
Lambun Ma'aurata