28/08/2025
CIKAKKEN BAYANI GAMEDA CUTAR NOSOCOMIAL INFECTION,
Nosocomial Infection Koh Kuma A Kirata Da Suna Hospital Acquired Infections Wato (HAIs) Ita Wannan Cuta Ce Da Ake Samunta Ko Dauka Daga Asibiti, Ma'ana Anan Shine Cuta Ce Da Idan Marassa Lapiya Sunje Asibitin Zaman Jinya Suke Daukar Cutar,Ma'ana Majinyaci Yaje Asibi Neman Lafiya Kuma Yaƙara Daukan Wata Cutar Yayin Zaman Jinyarsa A Asibiti,Ita Wannan Cuta Ana Samunta Daga Ƙwayoyin Cuta Irinsu Bacteria,Virus,Da Kuma Fungi,
ABINDA YAKAMATA A SANI GAMEDA CUTAR NOSOCOMIAL INFECTION,
1.Ita Wannan Cuta Ana Samunta Ne Sakamakon Rashin Tsaftace Muhallin Marar Lafiya,Sannan Kuma Da Kasancewar Marar Lafiya Yana Jinya Cikin Yanayin Rashin Tsafta Sosai, Da Kuma Amfani Da Wasu Contaminated Medical Equipments Din Wanda Akayi Aiki Dasu Kuma Ba'ayi Sterilize Dinsu Ba Wanda Hakan Ke Baiwa Ƙwayoyin Cuta Irinsu Bacteria,Viruses Da Fungi Zama A Cikin Equipments Din,
2.Nosocomiak Infection Na Kawo Kamuwa Da Cuttuka Irinsu, UTI's, Blood Stream Infections, Surgical Site Infections Da Sauransu,
3.Za'a Kare Kamuwa Da Cutar Nosocomial Infection Ne Kawai Ta Hanyar Marar Lafiya Ya Zauna Cikin Tsafta Shi Da Muhallinsa,Sannan Staffs Kuma Su Tabbatar Suna Amfani Da (PPE's) Yayin Treating Patient,A Tabbatar Anyi Sterilize Dik Wasu Medical Equipments Din Da Akayi Amfani Dasu Domin Kawar Da Zaman Ƙwayoyin Cuta Irinsu Bacteria, Virus Da Fungi A Cikin Equipments Din
RAWAR DA EHO'S SUKE TAKAWA WAJEN DAKILE CUTAR NOSOCOMIAL INFECTION,
Jami'an Kiwon Lafiyar Muhalli Da Al-umma Wato (Environmental Health Officers) Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Dakile Cutar Nosocomial Infection A Asibitoci Da Wasu Healthcare Facilities
1.EHO's Na Yin Bincike A Asibitici Da Dik Wasu Healthcare Facilities Domin Tabbatar Da Cewa Anbi Ka'idar Bin Matakan Dakile Yaduwar Dik Wata Infectious Diseases,
2.EHO's Na Sanya Idanu Da Bincike Kan Abinda Ya Jawo Infections Din,Domin Bin Matakai Wajen Magancewa,
3.EHO's Na Wayar Da Kan Ma'aikatan Lapiya Na Wajen Da Kuma Majinyata