28/09/2025
Ku taho kuji sirrin Izalah
Daga: Shehu A. A. Gashua
{1} Bin Allah Da Manzon tsira
(Qur'ani da sunnah).
{2} Kafa hujja da Qur'ani da hadisan Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).
{3} Neman Ilimi da karantaswa.
{4} Da'a da biyayya ga shugabanci bisa doron Alqur'ani da Sunnah.
{5} Gina Addinin Musulunci ta hanyar gina: masallatai, makarantu, Majalisun karatuttuka, Asibitoci, ĆŠakunan karatu (Library), motocin da'awa da babura, ciyar da Tufatar da marayu harma da Aurar su da kuma basu magani.
{6} Sada zumunci tsakanin juna, Girmama juna da kyakkyawar mu'amala.
{7} Horas da Al'umma yadda zasu tsaya da kafafun su ta hanyar koyar da sana'o'i.
{8} Samar da guraben karatu ga ĆŠalibai masu hazaka ta hanyar Yin Daura da bada horo.
{9} Shirya Wa'azozi tin daga matakin ƙasa, Jihohi, ƙananan hukumomi, Gundumomi da unguwanni Birane da ƙauyuka.
{10} samar da haÉ—in ka Taimakon Juna tsakanin Al'umma.
WaÉ—annan kaÉ—an kenan daga cikin Abubuwan dake cikin Izalah
Shugaban mu na Duniya Ash-Sheikh (Dr) Imam Abdullahi Bala Lau, Allah ya ƙara maka Hakuri da juriya akan wannan namijin Aiki.
Shugaban mu na malamai Ash-Sheikh Dr. Imam Ibrahim Jalo Jalingo (ĆŠan Madina mai Rigar hujja)
Allah ya ƙara Ilimi da Daukaka.
Allahu Akhbar, Shugaban mu na Rundunar Agaji ta ƙasa da ƙasa
Ash-Sheikh Engr. Imam Mustapha Imam Sitti (Jagoranci ba wasa) Allah ya ƙara Lafiya da Nisan kwanaki masu Albarka.
Izalah kenan Idan bakayi É—an yana yi, ko matar ka, ko jikan ka, ko sirikin ka, ko! ko!! ko!!! (Sunnah Leka Gidan kowa.
Jibwis Social media Yobe State Directorate