21/02/2026
BABU ANNABAWA A SIYASA...
Daga shafin Abdulmajid
Fakewa da ake yi wajen neman maasumin dan siyasa na nuni da cewa samsam ba mu shirya neman gyara a kowane bangare na siyasa ba.
Na lura da haka ne kan yadda aka yi ca wajen caccakar Sheikh Isa Pantami sakamakon sauya matsaya da yayi daga abinda yake kai shekarun baya zuwa zama cikakken dan siyasa kuma dan boko a yanzu.
A zatona da gaske ne mun yarda cewa bata-gari sun kanainaye siyasar Najeriya, kuma lallai ana neman sauyi, shi kuma wannan sauyi zai zo ne kawai a yayinda mutane na gari s**a mamaye guraben da ake neman a gyara, ko dai ta hanyar gwagwarmaya wadda kan janyo zubar da jini, ko kuma hanyar salama ta siyasa, sai dai da zaran wani na gari ya sa kai a wannan bangare sai ya ci karo da fushin masu neman a gyara su ce ya zama na banza. Idan a gwagwarmaya ya fito su jefe shi da kafirci, idan a siyasa ya fito su jefe shi da cin amana.
Abinda ya kamata mu tambayi kanmu shine, shin mun san adadin mutane na gari da ke shirin shiga gyaran Najeriya, kuma da suna cikin gwamnati da gyaran ya zo da sauki, amma saboda gudun magana da yarfe s**a gwammace su ci gaba da zama a inda jamaa ke son ganinsu ko da kuwa za a rufta tare babu maceci?
A halittar Dan Adam dai Annabawa ne basa kuskure, kuma Annabawan nan sun kare ba zasu shiga siyasa ba, don haka duk wanda zai shiga duk kyawunsa yana da kuskuren da ko dai yayi a baya ko kuma zai yi nan gaba, zai iya kere na Sheikh Pantami ma ko ya kasa, na san dai ko a kudin sayen Data a bana kun san amfanin Pantami a bara, don haka da bakikkirin gwanda baki-baki. Ku bar na gari-gari su shiga siyasa don Allah