Novels Books

Novels Books The main purpose of this page is tom give you news and any related to education

A Sanadin Makwabtaka Asanadin Makwabta 3 Complete Hausa Novel DocumentBy Zee Laluh ...bayan ta gama warware takardar, zu...
17/09/2024

A Sanadin Makwabtaka
Asanadin Makwabta 3 Complete Hausa Novel Document
By Zee Laluh ...bayan ta gama warware takardar, zuba ma content d'in ciki ido tay tana Karantawa, lokacin data gama a matuk'ar razane ta d'ago idanunta a waje ta kalli Hajiyar kawae sai taga tana mata dariya, kai idon ta tay kan Haisam shima taga yayi mata d'an guntun murmushi tare da lumshe ido, rud'ewa tay ta kasa Fahimtar komai hakan yasa ta k'ara maida idon ta kan takardar ta k'ara karanta abunda aka rubuta a ciki k**ar haka,
_WE ARE SO HAPPY TO WELCOME YOU INTO OUR FAMILY ZARAH_
_It's such a joy to be with u, We hope your presence will brightens up our days. You're a Wonderful person Zarah, we are so lucky to know u._
*We look forward to all the Wonderful things you'll bring to our lives. We love u so much Zaraah.*
Lokacin data gama d'agowa
tay ta waro idanu ta kalli Fanan dake tsaye a gabanta har lokacin kawai sai gani tay itama tay mata d'an murmushi, gaba d'aya sun rud'ata har Fuskarta ta bayyanar da hakan, d'age mata gira Fanan tayi Calmly ta furta "Nima na rama halin da Message d'in ki ya sani Zaraah" ta6e baki ta fara kawae sai ta fashe da Kuka Fanan ta kai hannu ta rungumo ta a jikinta a hankali take furta mata is okey, d'agota tayi bayan wani lokaci ta k**a hannunta s**a nufi ciki har lokacin Fatuu kuka take tasa gefen gyalenta tana ta goge k'wallan dake zubo mata, Kujerar data taso ta nufa da ita ta Zaunar da ita itama ta zauna a gefenta ta yadda s**a saka Fatun a tsakiya har lokacin tanata sharar k'walla da gyalenta, Hannu Fanan ta kai ta dafa Shoulder d'inta tana ce mata ya isa haka kada tayi ciwon kai tayi mata wasa ne, Hajiya itama ta fara bata hak'uri tace mata sune s**a shirya mata haka ita ba ruwan ta, daina yin kukan tayi ta sadda kanta k'asa har lokacin gabanta na d'an fad'uwa ganin komai take k**ar a Mafarki don bata ta6a zaton haka daga Fanan d'in ba, a hankali ta d'an juyar da kanta ta saci kallon Haisam dake gefenta karaf s**a had'a ido dashi ya kafeta da idanun shi dake a d'an lumshe da sauri ta maida kanta k'asa, Hajiya ce tayi d'an gyaran murya tace masu suyi ma Annabi salati (SAW), bayan sun gama ta fara masu Nasiha gaba d'aya kan zaman tare da kuma hak'uri da juna daga baya ta fara ma Haisam shi kadae kan rike amanar matan shi da kuma yin Adalci a tsakanin su, bayan ta gama dashi ta koma kan Fanan ta nuna mata kada ta dauki duk abunda ake fad'a akan kishiya ta d'auka ita d'in Alkhairi ce sai taga ta zame mata Alkhairin ta rufe idanunta ta kuma toshe kunnuwan ta daga dukkan wata zuga da za'ai mata kan Fateema, kada ta goyi bayan a cutar da ita domin tasan Allah baya barin cuta, tace ta ci gaba da yi mata kallon k'anwarta k**ar yadda take yi mata a da, a matsayinta na babba ta zamo mai hak'uri sosae akan komai in taga tayi ba daidai ba ta nusar da ita...Sosae tayi mata Nasiha itama Fanan d'in dake jingina da kujera tana ta d'an jinjina mata kai, a k'arshe ta yaba mata sosae akan Namijin kokarin da tayi wurin yak'i da zuciyarta ta danne kishinta don Farincikin su ta nuna samun matan da zasu iya yin hakan yanada matuk'ar wahala ta nuna mata kar ta d'auki hakan gazawa face jarumta wurin yin abunda yake daidai, ta nuna more ma rayuwa shine ka sanya farinciki a zukatan mutane ba ka za6i ka saka kanka kad'ai ba hakan zai saya maka soyayya da k'ima a idon mutane, haka kuma ko bayan ba ranka za'a ji rashin ka baza kuma a manta da kai ba riba biyu kenan sa6anin ka za6i Farincikin kanka kai kad'ai ka cuta ma mutane su rink'a k'in ka k'arshe ka mutu aita murna tunawa ma da kai yayi wuya,
Kallon Haisam tay dake kishingid'e yana sauraran ta tace "ina son ka sani Fanan masoyiyar ka ce ta hak'ika tunda har ta za6i Farincikin ka fiye da nata don haka indai ka wulakanta ta wllh sai Allah ya saka mata duk da bani da haufi a kan ka kawai tuni nake maka" jinjina mata kai yay a lokacin Fanan tasa hannu ta d'an dafe goshinta jin kuka na niyyar taho mata ita kad'ai tasan abunda take going through don ma tana ta yin Addu'oi a cikin ranta, komawa Hajiya tayi kan Fatuu da kanta ke a sadde tace ta dawo gareta, farko maraba da shigowa cikin Family d'in su ta k'ara yi mata tace tasan halinta itama bata da shakku a kanta don haka kada ta sake ta canza daga yadda ta santa ga Fanan nan taci gaba da d'aukar ta matsayin Yayarta kar ta sake daidai da rana d'aya tace zata mata kallon kishiya, in tana da matsala ta sanar da ita tana da yak'inin zata bata shawarar kirki sannan ta taimaka ma mijin su wurin ganin yayi masu Adalci hakan shine son gaskiya, in Fanan tana yi mata abunda bata jin dad'i ta fad'i mata idan bata gyara ba ita ta fad'i mata duk da tasan in sha Allahu hakan bazata faru ba, daga k'arshe bayan ta gama yi masu nasihohin da s**a tsuma masu jiki sosae tayi masu Addu'oi tasa Haisam shima yayi duk s**a d'aga hannuwa suna amsawa har ya gama gaba d'aya s**a shafa, shiru ta biyo baya duk s**a cigaba da yin kallo saidai kowa da abunda ke kai kawo cikin Zuciyar shi, gaba d'aya Fatuu ta kasa sakewa don jikinta na bata Haisam kallon ta yake hakan yasa duk ta takura ga kuma yanayin Fanan data lura tana a cikin damuwa k'arfin hali kawai take hakan yasa duk ta sha jinin jikinta, kiran sallar Magrib da aka fara yi yasa Haisam mik'ewa hannunshi ruk'e da rigar shi ta sama daya d'auka yace ma Hajiya zai je salla tai mashi a dawo lpy, d'an d'aga ido Fatuu tayi tana kallon bayan shi har ya kusa fita sannan ta maido shi k'asa, zuciyarta ce ta shiga raya mata wani abu game da shi, bayan fitar shi Hajiya ta mik'e tace masu suje suyi salla, Fanan ce ta fara mik'ewa da d'an murmushi ta kalli Fatuu data d'ago tana kallonta ta mik'a mata hannu, a sanyaye ta k**a hannun ta mik'e s**a nufi ciki.
Yadda hakan ta faru, bayan Haisam sun gama Magana da Fanan kan zuwa Nigeria ranar talata, da yamma Hajiya Maryam ta kirata don ta ji halin da ake ciki game da tahowarta nan take sanar mata yadda s**ai da Haisam kan zuwa Nigeria ta yi ma Hajiyar Magana da kanta, nan Hajiya Maryam taji dad'i sosae don tasan da wuya in Hajiyar bata bari an saki Fatun ba Saboda su duka sun nuna basu so kuma tasan yadda take ji dasu gaba d'aya, hakan ne yasa washe gari da Hajiya ta kira Hajiya Maryam game da zancen dawowar Farha da Maganar data yi mata sam bata damu ba, tun bayan da s**a yanke zuwa Nigeria Haisam ya kasa samun natsuwa, damuwa tayi mashi yawa don yasan shi dae ba iya sakin Zaraah zai yi ba yadai biye mata ne don ya kwantar mata da hankali k'arshe kuma yasan indae s**a zo Nigeria yak'i sakin Fatuu to abun zai k'ara kwa6ewa ne, hakan yasa ya yanke tunkararta akan hakan, Ranar Alhamis da daddare ya isketa a d'aki lokacin tana zaune akan gado tana latsa wayarta, tana ganin shi ta d'ago tana mashi dariya ya nufi bakin gadon ya zauna shima yana mata murmushi, aje wayar tayi ta matso inda yake ta kwanta a bayan shi ta yadda yay k**an ya goyata ta sak'alo hannuwanta a wuyan shi nan ta shiga fad'a mashi kalaman soyayya, sosae yaji fargabar sanar da ita abunda ya kawo shi k'arshe dai yay k'arfin hali yace mata magana yake so zasu yi, tana jin hakan ta sake shi ta dawo daga gefe tana kallon shi, d'an jimm yay ta kafe shi da ido daga baya ya fara magana gently, ce mata yay Alfarma yake son ya nema a wurinta for the first time a zaman su, jinjina mashi kai tay gaba d'aya ta maida hankalinta akan shi, ce mata yay ya zauna yayi dogon tunani gaskiya idan ya saki Zarah bai mata Adalci ba zai zama ya cuce ta ne Saboda shi ya fara saninta sannan tayi k'arama ace ta zama bazawara, wani kallo take bin shi dashi yanayin fuskar ta ya canza da alamun d'aurewar kai tace to mi yake nufi kenan, kauda idon shi yay tana ta kallon shi can ya juyo ya kalleta yace "I can't divorce her...
Domin Sauke cikakken littafin ko kuma karanta shi a cikin wayoyinku sai ku danna bulun rubutun dake kasa ko kuma hoton 👇👇👇👇👇
https://enovels.com.ng

YOUR TITLE GOES HER
31/07/2024

YOUR TITLE GOES HER

CategoriesUncategorized July 31, 2024 By Abdul YOUR TITLE GOES HER Post navigationPrev DIYAM Na Maman Maama Leave a Reply Cancel replyYour email address will not be published. Required fields are marked * Save my name, email, and website in this browser for the next time I comment. Δ

DIYAM Na Maman Maama Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani damar fara wannanrubuta, ina rokonsa ya bani ikon rubuta alkh...
31/07/2024

DIYAM Na Maman Maama Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani damar fara wannanrubuta, ina rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi ya kuma haneni daga rubutasharri. Allah ya sa wannan rubutu ya amfane ni da duk wanda Allah ya bawa ikonkarantawa. Littafin DIYAM kyauta ne, ina fatan ya zamanto minsadakatujjariya har bayan raina. Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana, na…...

DIYAM Na Maman Maama

Abban Sodoji Na Bos Bature
31/07/2024

Abban Sodoji Na Bos Bature

CategoriesHausa Novels, Download July 31, 2024 By Abdul Abban Sodoji Na Bos Bature 0 downloads Abban Sododji Takun Karshe Na Boos Bature Download File 💋♥️-ABBAN-SOJOJI-💋♥️-Takun-Karshe-cmplt.-By-♥️Ubeera-♥️.pdf – 9.61 MB Tag: hausa novels Post navigationPrev GUDUN KADDARA NA ...

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2 ".............ya fada soyayya?,yana nufin kenan aure yake da buqatar yi?,bama fadawa soya...
30/07/2024

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2 ".............ya fada soyayya?,yana nufin kenan aure yake da buqatar yi?,bama fadawa soyayyar ba,wadda ya fada soyayyar da ita, yarinyar dake da gatan da ya kerewa nasa,suke da dukiya da tarin gatan da ya yiwa hankali nisan tazara,kai koda ma ace ya kammala karatunsa ya k**a aiki ina yaga kudin auren hamdiyya abdu me kano?,ko yana da kudin aurenta dinmma sakayyar da zai yiwa bibi da mohmoud dake tsaye a kansa ba dare ba rana?,ya tattara 'yan kudinsa yayi aure ba tare da sun mori komai daga gareshi na wahalar da s**a sha dashi ba?....

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2

🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U G U M A PAGE 01 *Da sunan Allah me rahama me jin qai,dukkan yabo da godiya sun tabbata ga u...
30/07/2024

🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U G U M A PAGE 01 *Da sunan Allah me rahama me jin qai,dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin talikai,tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta annabi muhammadu S A W wannan karon labarin namu zai sauka ne a qasar nijer,duk inda akaga kuskure ko gyara sai ayi haquri,domin ni banigerian ce😂...

Gudun Kaddara na Huguma Book 1

Innocent Girl Na Nameera and Nainarh بسم الله الرحمن الرحيم Ep. One. Shigowa s**a yi ganin yadda aka taru yasa ta ce. "D...
30/07/2024

Innocent Girl Na Nameera and Nainarh بسم الله الرحمن الرحيم Ep. One. Shigowa s**a yi ganin yadda aka taru yasa ta ce. "Dan Allah menene yake faruwa ne?." Kallonta guard ɗin ya yi yayi gaba abin sa, suna shiga compound ɗin gidan ƙara waro idanu tayi ganin jama'ar har sunfi na waje yawa har s**a ƙaraso gabansa wani mutumine wanda aƙalla zaikai 65yrs ɗin ta kalleshi bakinta narawa ta ce....

Innocent Girl Na Nameera and Nainarh

Hamshakiyar Uwa Na Maryam Abdullahi K/Mashi Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai,tsira da amin...
30/07/2024

Hamshakiyar Uwa Na Maryam Abdullahi K/Mashi Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai,tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad(S.A.W). Kamar yadda na fara lafiya,Allah ka bani ikon gamawa lafiya,Allah ka bani ikon faɗakarwa gwargwadon iyawata,Ya Allah ka yafe min duk wani kuskure da hannuna zai rubuta,Allah ka bani ladar faɗakarwar. *Free Page 1* Kan shi a ƙasa bayan ya zube a gaban ta gwiwoyin sa suna ƙasa tamkar mai neman gafara....

Hamshakiyar Uwa Na Maryam Abdullahi K/Mashi

ƘASAITA NA MARYAM KABIR MASHIƘASAITA NA Page 1 Mota ƙirar ƙasar (South Korea) ce ta tsaya a dai-dai ƙofar wani kanti, wa...
30/07/2024

ƘASAITA NA MARYAM KABIR MASHIƘASAITA NA Page 1 Mota ƙirar ƙasar (South Korea) ce ta tsaya a dai-dai ƙofar wani kanti, wanda zamu iya kiranshi da suna na tailoli, ma'ana shagon ɗinki kenan,Mai suna Almansir Tailoring and Fashion Design Company. Mutumin ƙofar shagon shi ya nuna mana cewa mata da maza na iya kai ɗinki a shagon. Ruwan toka ash colour shi ne fentin motar, wanda zamu iya kiran motar da suna KIA Saloon....

ƘASAITA NA MARYAM KABIR MASHIƘASAITA NA

TSUTSAR NAMA BOOK complete Book 𝑃𝑎𝑔𝑒 𝑜𝑛𝑒_Free page بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمDa sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai ...
26/07/2024

TSUTSAR NAMA BOOK complete Book 𝑃𝑎𝑔𝑒 𝑜𝑛𝑒_Free page بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمDa sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai. ………Humm wato Bilyn Abdull atawa fahimtar da abinda shekaran jiyata da jiyata har zuwa yau ɗina tazo min dashi zan iya cewa JARUMTA itace asalin RAYUWA. HAƘURI shike jagorantar numfashi da samun tsahon rai ga kowanne halitta a cikin salama....

TSUTSAR NAMA BOOK complete Book

CANJIN RAYUWA Complete Book 2 (1)Ahaji bishir ya kosa ya isa gidansa don kai wannan albishir.haka nan MIMI ta kosa matuk...
25/07/2024

CANJIN RAYUWA Complete Book 2 (1)Ahaji bishir ya kosa ya isa gidansa don kai wannan albishir.haka nan MIMI ta kosa matuka dad din nata ya dawo don ta sanar da shi labarin masoyinta khalil.momy nafisa kuwa tana cikin damuwa,tana ta tufka da warwara a kan yadda zata hada fitina tsakanin MIMI da mahaifinta. A haka alhajin ya iso gidan,cikin doki.tun daga shigowarsa falon yake zuga kiran nafisa!nafisa ta fito cikin sauri tana cewa, "Alhaji ga ni.lafiya kake ta kira na?"ya ce,"Lafiya lau....

CANJIN RAYUWA Complete Book 2

Address

No. 191 Sauna Kawaji Nasarawa
Kano
700001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Novels Books posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram