04/12/2025
CIWON AFENDIS - APPENDICITIS
Afendis (Appendix) wani ƙaramin yanki ne mai kamar jela da ke hade da ƙaramin hanji da babban hanji. Yana da girman kusan yatsan hannu.
Ciwon kumburin afendis (Appendicitis) yana faruwa ne idan kwayoyin cutar bakteriya s**a taru a ciki, wanda ke sa afendis ɗin ya kumbura har ya kai ga fashewa idan ba a dauki mataki ba cikin lokaci.
👉 Abubuwan da ke jawo kumburin afendis sune kamar haka.
1. Taruwar kwayoyin bakteriya a cikin afendis.
2. Cinkoso ko shinge da ke hana ruwa ko datti fita daga afendis.
3. Rashin kulawa da matsalar da wuri na iya janyo fashewar sa.
👉 Alamomin ciwon afendis.
1. Ciwon ciki da ke fara daga cibiya, daga baya ya koma gefen ciki daga ɓangaren dama a ƙasa.
2. Ciwon ciki mai ƙaruwa lokacin motsi, tari ko numfashi mai ƙarfi.
3. Tashin zuciya da amai.
4. Gudawa ko zawayi.
5. Jin zazzabi ko rashin lafiya gaba ɗaya.
👉 Appendicitis na buƙatar a magance matsalar cikin gaggawa ta hanyar yin tiyata (appendectomy) don cire afendis kafin ya fashe ko ya haddasa wata cuta.
👉 Idan kin/ka fuskanci waɗannan alamomi, garzaya asibiti nan da nan kada a yi jinkiri!
© Jami'in Aikin Jinya
27/11/2024.