12/01/2026
BAMBANCI TSAKANIN SIHIRI DA MU'UJIZA DA KARAMA
Da kuma wadansu abubuwa masu k**a da su.
Daga shafin Bashir Halilu.
Lambar waya 08162600700.
Da akwai bambanci tsakanin Karama da Sihiri, ta yadda wasu suke fakewa da karama suna aikata sihiri. Haka nan akwai wadansu abubuwa da suke faruwa ga mutane masu k**a da sihiri amma kuma ba sihiri ba ne.
Anan dai insha Allahu za mu kawo bayanin wasu daga cikin wadannan abubuwa ko da guda biyar ne.
(1) MU'UJIZA.
Wani abin mamaki ne da Allah Ya ke horewa Annabwansa, wanda babu wanda zai iya yin irinsa a zamaninsu sai su kadai, su kan yi haka ne don su tabbatarwa da jama'arsu cewa lallai Allah Madaukakin Sarki ne Ya aiko su da sako, su kan yi mu'jiza kuma idan mutanensu sun nemi cewa su aikata wani abun mamaki wanda zai tabbatar da cewa su mutanen Allah ne.
Annabawa su kan aikata wani abu na mu'ujiza kuma don wadanda su ka yi imani da su su kara imani. Annabawan Allah ne kawai suke iya yin mu'ujiza, in ba su ba babu wanda zai iya.
Yadda mu'ujiza take.
1- Ita Mu'ujiza a fili ma'abocinta yake aikatata, wato Annabin Allah. A gaban kowa, babu 6oye-6oye acikinta.
2- Aikata mu'ujiza ba ya kasancewa sai da da'awar Annabta. Ma'ana in ba mai da'awar Annabta ba babu wanda zai ce yana da wata mu'ujiza.
3- Ita Mu'ujiza Annabin Allah yana yinta ne don mutane su amfana da ita ko don ya ceci rayuwarsu ko kuma don ya kira su zuwa ga addini amma ba a yin mu'uzija don kawai nishadi ko don a birge mutane.
4- Ita mu'ujiza gaskiya ce kuma tana da hakika. Ma'ana, idan misali Annabin Allah ya nuna wani dutse, sai Taguwa ta fito daga cikin dutsen, to Taguwar ta gaske ce kuma fitowar ma ta gaske ce, ba k**ar film bane da za nuna maka abu ya faru alhali bai faru ba.
6- Ita Mu'ujiza Annabawa suna aikata ta ne bayan Allah Ya ba su umarnin aikatawa kuma Ya sanar da su yadda za su aiwatar da ita.
Misalin Mu'ujiza.
1- Annabi Nuhu Alaihis salam ya kera jirgin ruwa kuma ya dora kowacce nau'in dabba daga cikin halittun duniya acikin jirgin, ya tserar da su daga ambaliyar ruwa.
2- Annabi Ibrahim Alaihis salam kafurai sun jefa shi acikin wuta, yay kwanaki acikin wutar tana ci amma ya fito bai kone ba.
3- Annabi Musa Alaihis salam ya yi addu'a, aka dinga saukarwa mutanensa tsuntsu daga sama gashashshe suna ci.
4- Annabi Isa Alaihis salam yana yiwa wanda ya mutu addu'a, sai ya tashi, ya dawo da ransa.
5- Annabi Dawuda Alaihis salam in yana tasbihi ko zikiri sai tsuntsaye da duwatsun da ke kewaye da shi su ma su k**a yi.
6- Annabi Sulaiman Alaihis salam yana shinfida dadduma, mutane su hau da kayan abincinsu da sauran kayayyakin amfani, sai ya sa iska ta daukesu, ta kaisu unguwa, har sama da tafiyar wata guda.
7- Annabi Muhammad (SAW) ya zo da littafin da ba wanda ya isa ya zo da k**arsa, ko duk duniya za su hadu akan haka.
(2) SIHIRI KO TSAFI.
Sihiri shi ne hadin kai tsakanin Boka da Aljani bisa wata yarjejeniya don a aikata wani abu wanda ya sa6awa Allah. Wani lokacin Sihiri yana kasancewa ko ba tare da aiki da Aljanu kai tsaye ba amma dai kayan aikin da kuma hanyoyin da ake bi sun sa6aWa Allah Madaukakin Sarki.
Sihiri shi ne aikata wani abun mamaki, ta hanyar da wanda aka yiwa kon wanda aka yi a gabansa zai kasa gane yadda aka yi abun ya faru, saidai sihiri yana kasancewa da sa hannun Aljanu acikin aikin ko kuma da amfani da wasu kayan tsafi k**ar najasa da jini da dai sauransu.
BAMBANCIN SIHIRI DA MU'UJIZA.
1- Shi Sihiri a 6oye ake yinsa. Misali, idan mutum zai yi sihiri, to zai rufe abinda zai yi sihirin da shi, ba zai bude ka ga abin a zahiri sosai ba ko kuma ba zai bari ka ji abinda yake fada lokacin da yake aikata sihirin ba kuma zai yi amfani da abinda ba za ka iya gane ko-menene ba. Mu'ujiza kuwa a fili ta ke.
2- Shi Sihiri Bokaye ne kawai suke yinsa kuma aikata shi kafirci ne.
3- Sihiri ba shi da hakika. Ma'ana, idan misali Boka ya buga ma ka kudin jabu, to kudin ba su da hakika, kodai daga baya su 6ace, ko kuma su koma abinda aka yi su da shi k**ar fararan takardu ko kasa ko kuma ya zamana kwata-kwata ba ma kudi bane, idon ka ne kawai ya ke nuna maka kudi.
Ka karanta karin bayani akan wannan sihirin acikin rubutunmu mai take 'Assihrut Takh'yiyliyy' wato sihirin rufa ido, acikin wannan shudin rubutun
https://m.facebook.com/sunnahmedicinepage/photos/a.1374341292684795/1546542498798006/?type=3&source=54
4- Galibi Sihiri ana yinsa ne don a cutar da wani ko don a nemi suna ko neman kudi. Yayinda Mu'ujiza Annabawan Allah suna yinta ne don su shiryar da bayin Allah zuwa tafarki madaidaci.
Karanta cikakken bayani akan sihiri da rabe-rabensa acikin wannan shudin rubutun
https://m.facebook.com/sunnahmedicinepage/photos/a.1374341292684795/2130355910416659/?type=3&source=54
(3) KARAMA كَرَامَة
Karama wani abun mamaki ne ko Al'ajabi da Allah Ya kan kaddara ya afku ta sanadin wani mutumin kirki, wanda shi kansa wannan bawan Allah bai san yadda aka yi abin ya faru ba kuma bai san zai faru ba.
Karama sai ga Musulmi kawai take faruwa kuma ba ta afkuwa cikin cutarwa ko aikata sa6o, saidai ga abinda mutane za su amfana ko abinda shi mai karamar zai samu fa'ida akai.
Misali, mutum yay ma ka addu'a ta alkhairi akan wani abu da ake ganin k**ar ba zai yiwu ba, sai kuma abin ya tabbata.
Yadda Karama ta ke.
1- Wanda karamar ta faru da shi bai san haka za ta kasance ba, shi ma kawai gani yay abun ya afku ta sanadiyyarsa.
2- Ba kullum ake kwana a gado ba. Zai iya yiwuwa watarana kayi Karama wata rana kuma Karamar ta ki aiki.
3- Karama ba ta faruwa cikin aikata sa6o ko barin ibada. Kamar ace akwai wani saboda tsabar k**arsa ba ya Sallah ko saboda tsabar karamarsa ba ya Azumi.
4- Karama ba Sihiri ba ce, ba maita bace, ba Kambun ido bane. Ita karama daga Allah take kuma bata cutarwa.
Karanta cikakken bayani akan 'Kambun ido' acikin wannan shudin rubutun.
https://m.facebook.com/sunnahmedicinepage/photos/a.1374341292684795/2243039979148251/?type=3&source=54
5- Karama ba ta da alaqa da aiki da Aljanu ko Rauhanay ko Mala'iku ko amfani da wasu Layoyi da dai sauransu.
Karanta cikakken bayani akan 'Rauhanay' acikin wannan shudin rubutun.
https://m.facebook.com/sunnahmedicinepage/photos/a.1374341292684795/2262898177162431/?type=3&source=54
Karanta cikin bayani akan 'Hukuncin shan rubutu da daura laya a addinin Musulunci' acikin wannan shudin rubutun.
https://m.facebook.com/sunnahmedicinepage/photos/a.1374341292684795/2066799786772272/?type=3&source=54
6- Babu wasu mutane da aka ware aka ace su ne kawai masu Karama, Malamai sun ce indai ka yi imani da Allah kuma kana aiki na gari, to kai Waliyyi ne kuma karama za ta iya bayyana a hannunka.
(4). BADALI بَدَلٌ
ko a ce TAHRIYQUL ADAT تَحْرِيقُ العَدَات
Abinda ake cewa Badali shi ne:- a 6atar da hankalinka ta hanyar aikata wani abu wanda za ka kasa gane yadda aka yi shi. Shi Badali galibi ana yinsa ne ta hanyar a sanya wani mtum ya la6e yana magana, ta yadda za ka kasa gane daga inda maganar take fitowa. Ana iya amfani da 'chemicals' da wasu itatuwa wajen aikata badali. Misali mutum ya shafa wani ruwan itace a hannunsa, sai ya ta6a wuta kuma wutar ba za ta kona shi ba. Wani lokacin mutum zai iya cewa zai buga ma ka kudi misali, sai yay dabara, ya zuba kudin Aljihunsa, ya ce ga kudi ya buga ma ka, duk wadannan ana kiransu da suna badali.
1- Badali ba karama bace kuma ba sihiri bane, amfani da kayan aiki ne ko kuma 6oyewa mutum gaskiyar lamari.
2- Badali yana da hakika, domin kuwa idan mutum ya buga ma ka kudi ta wannan hanyar, to kudin na gaskiya ne tunda kudin Aljihunsa ya ba ka, haka ma in ya ce Aljaninsa ko Rauhaninsa zai magana to magana ce zahiri kake ji amma kuma wani mutum ne ya la6e ya ke yi ko mu recording aka kunna ma ka.
3- Badali ba shirka bane, saidai zai iya zama sa6o idan aka shirya damfarar wani aciki ko aka cutar da wani.
(5)- ISTIDRAJ الإسْدْرَاجِ
Istidraji, ko ka ce Talala, a harshen Hausa.
Shi ne wani abu mai k**a da karama ya bayyana a hannun wani Fasiqin mutum ko Kafiri, ta yadda zai dinga aikata abubuwan mamaki da al'ajabi, har ya tara jama'a ko ya kara nausawa acikin kafirci da sa6o, ba zai gane ba shi da wayo ba har sai ya gamu da Allah. Misali, a ce ga wani Kafiri amma idan yay wa mara lafiya addu'a yana warkewa ko a ce ga wani Fasiqin mutum wanda kowa ya san shi akan fasiqanci da 6arna amma in ya ce gobe abu kaza zai faru to sai a ga abin ya faru da gaske. Wannan ana kiransa da Istidraji, wato Talala mai k**ar sake.
Yadda Istidraji ya ke.
1- Istidraji ba tsafi bane, ba Karama ba ce kuma ba Badali bane, Allah ne Yake bayyanar da shi ba tare da wanda ya baiwa ya sani ba.
2- Istidraji yana bayyana ne a hannun Kafiri ko fasiqin mutum mai sa6o, ta yadda zai dauka hanyar da yake kanta daidai ce kuma har halakakkun mutane su dinga binsa a kanta.
3- Istdiraji zai iya faruwa ta yadda Kafiri zai dinga aikin taimakon al'uma ko cutar da al'uma ko kuma ya zamto ya gagari hukuma, har zuwa lokacin da Allah Zai kawo karshensa.
4- Istidraji yana iya faruwa ta yadda mutum zai ta aikata sa6o amma ya ga har yanzu ba abinda ya same shi, k**ar Allah Ya manta da shi ko ba Zai k**a shi ba, sai wata-rana kwatsam ya ji kamu.
Allah Ya kiyaye mu.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayarda magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08162600700.
Muna bayarda magunguna na karya sihiri da maganin matsalolin aljanu da sauran cututtuka na yau da kullum k**ar typhoid, malaria, hawan jini ciwon suga da dai sauransu. Ana iya tuntuɓarmu a wannan lambar 08134434846