17/03/2026
MUHIMMANCIN KAI YARA ALLURAR RIGA-KAFI
Me ake nufi Allurar Riga-Kafi?
Allurar riga-kafi wata hanya ce ta kariya da ake amfani da ita domin kare jiki daga wasu cututtuka kafin su k**a mutum. Ana yin wannan allura ne ta hanyar saka ƙwayar cuta da aka raunana ko aka kashe a cikin jiki domin jikin mutum ya koyi yadda zai yaƙi cutar idan ta shiga.
Saboda haka idan yaro ya samu allurar riga-kafi, jikin sa yana samun kariya daga wasu cututtuka masu haɗari tun kafin su same shi. Wadannan cutuka sun haɗar da:
shan inna (Polio), Tarin fuka (Tuberculosis), Kyanda (Measles), Tetanus, Ciwon Hanta (Hepatitis B), Shawara (Yellow Fever).
NAU'IKAN ALLURAR RIGA KAFI DA AKE MA YARA DA AMFANIN SU
BCG:
BCG wata allura ce da ake yi wa jarirai nan da nan bayan haihuwa domin kare su daga cutar tarin fuka wato Tuberculosis. Wannan cuta tana iya shafar huhu da wasu sassan jiki, saboda haka wannan allura tana taimakawa wajen kare jarirai daga wannan cuta mai haɗari.
OPV (Oral Polio Vaccine):
OPV allura ce ta baki da ake bai wa yara domin kare su daga cutar shan inna wato Polio. Ana fara ba yaro wannan allura tun bayan haihuwa sannan a ci gaba da ba shi a makonni shida, makonni goma da makonni goma sha huɗu.
Pentavalent Vaccine:
Pentavalent allura ce da ke kare yara daga cututtuka guda biyar wato Diphtheria, Pertussis, Tetanus, Hepatitis B da Haemophilus influenza. Ana yin wannan allura a makonni shida, makonni goma da makonni goma sha huɗu bayan haihuwa domin ba yaro kariya daga waɗannan cututtuka.
Measles Vaccine:
Wannan allura tana kare yara daga cutar kyanda wato Measles. Ana yin ta lokacin da yaro ya kai wata tara domin kare shi daga wannan cuta mai yaduwa cikin sauƙi.
Yellow Fever Vaccine:
Allurar Yellow Fever ana yi wa yara a wata tara domin kare su daga cutar Yellow Fever wacce sauro ke yadawa kuma tana iya zama barazana ga rayuwa.
MUHIMMANCIN KAI YARA ZUWA WAJEN ALLURAR RIGA-KAFI
✅ Kai yara allurar riga-kafi yana taimakawa wajen kare su daga cututtuka masu haɗari da kan iya janyo matsaloli masu tsanani ga lafiyar su. Wadannan cututtuka sun haɗa da polio, kyanda, tetanus da kuma tarin fuka.
✅ Yin allurar riga-kafi yana taimakawa wajen rage mace-macen yara kanana. A kasashe da dama na duniya, an samu raguwar mace-macen yara ne saboda amfani da allurar riga-kafi.
✅ Allurar riga-kafi tana taimakawa wajen hana yaduwar cututtuka a cikin al’umma. Idan yawancin yara sun samu rigakafi, cututtuka ba sa samun damar yaduwa cikin sauƙi.
✅ Yin allurar riga-kafi yana taimakawa wajen kare lafiyar yaro tun daga ƙuruciya har zuwa lokacin da yake girma.
✅ Kai yara allurar riga-kafi yana rage nauyin da cututtuka ke jawo wa iyaye da kuma tsarin kiwon lafiya saboda rigakafi ya fi magani sauƙi da arha.
✅ Allurar riga-kafi tana taimakawa wajen tabbatar da cewa yara suna girma cikin lafiya ba tare da nakasa ko wasu matsalolin lafiya da wasu cututtuka kan haifar ba