Zurriyya Integrated Farms

Zurriyya Integrated Farms Your farms your Future

29/03/2026

1.Ginger fresh
2. Cloves
3. Salt
4. Lemon
5. Tooth paste

idan kasamu Maja mata guda 20 da zakaru guda 2 to kasamar ma kanka katamin kamfani.idan s**a samu issashen kulawa, wato ...
29/03/2026

idan kasamu Maja mata guda 20 da zakaru guda 2 to kasamar ma kanka katamin kamfani.

idan s**a samu issashen kulawa, wato abinci Mai kyau da ruwan sha Mai tsafta to mafi karanci zaka dinga diban kwai 12+ a yini in sha Allah.

sanan adinga Deworming dinsu kowani wata tareda basu rigakafin Lasota DA Gamboro Duk Kusan karshen wata.

wanan shi ne atakaice. ALLAH SUBHANAHU WATAALAH YA SANYA MANA ALBARKA A KASUWANCINMU. AMIN YAHAYYU YAQAYYUM

*Kiwon kaji Maja* _Idan 50 zaka zuba sai ka raba wannan lissafin gida 2._ Dan Allah asamu lokaci a karanta domin jama'a ...
28/03/2026

*Kiwon kaji Maja*

_Idan 50 zaka zuba sai ka raba wannan lissafin gida 2._

Dan Allah asamu lokaci a karanta domin jama'a su amfana su shiga kiwon Maja *(Noilers)*

Idan zakayi kiwon kaji maja guda *100*.

Kana bukatar
1. Abinci 240Kg = ₦ 140,000. (1 to 6 weeks)
2. Grower marsh 1000Kg (₦385,000 at 6 to 18 weeks)
3. 18 to 22 weeks za a basu pre-layer wanda zai k**a ₦ 125,000. Saboda Maja basa bukatar Calcium k**ar kaji layers.
*Abinci* za'a kashe ₦ 650,000
*Magani* da allurai ₦30,000
Sauran kayyayyaki for emergency ₦50,000
Total abunda za'a kashe ₦930,000

Kanada *Maja* guda 100, mata 100 maza 10.
Production rate 60 to 70%. Zamu dauki average 65% = 65

A wata kana da kwai (Eggs) guda *1950*

Ana saida kwai ₦300

300×1950 = ₦ 585,000 per months. Kuma *Maja* tana shekara daya da rabi *1½* years tana bada kwai.

Duk kullum maja zataci *13Kg* a wata kuma *390kg* = buhu 15. Wanda ana hada buhu daya ₦10,000.
Kaga ₦10,000×15 = ₦150,000 da wasu 'yan kunji kunji na kaza a barshi total ₦200,000 duk wata.

Ribar da mutum zai samu= ₦585,000 - ₦200,000 =₦ 385,000 duk wata. A shekara daya da rabi akwai wata 18months = ₦385,000×18= 6,930,000.

Idan kuma zakayi kyankyasa. Duk maja 1 ana sayar dashi wani wajan ₦800 ya danganta.

Kullum kana da kwai guda *65*

A kwana 4 zaka samu kwai guda 260. Idan ka sayi incubator mecin kwai 260 duk bayan kwana 21days zaka fitar da kaji 260 ( 260 × 800= ₦208,000).

Saika lissafa a wata kwai nawa zaka samu? Guda 1950. Idan ka samu incubator da zaka kyankyashe kwanka idan lokaci daya ka zubasu. A barshi kayi candling guda 50 ko 100 un-fertilize eggs ne saura 1850 (1850×800 = ₦1,480,000) a duk bayan kwana 21days.

Allah ya bamu sa'a Aameen ya hayyu ya Qayyum 🙏♥️

Harkan Agricultural Akwai Albarka sosai
Wannan littafin yana dauke da duk abinda kuke bukata na fara kiwon Maja in sha Allah kudinshi (3000) Ranar fara siya 1st April

Ibrahim Adamu Lokaci ✅️
Ku tuntubi wannan Number domin shiga harkan kiwo, koya da hanyoyin samun Riba 07039216446

Matan Noiler (Maja) guda 25 maza 2 a wata akalla zaka samu kwai 250_300.Domin akalla duk kaza daya tayi kwai 3 a sati.Ka...
27/03/2026

Matan Noiler (Maja) guda 25 maza 2 a wata akalla zaka samu kwai 250_300.

Domin akalla duk kaza daya tayi kwai 3 a sati.
Kaga kenan a duk sati zaka samu kwai 75 a sati.

Akalla a kullum zaka basu abincin da yakai 100_120gram.

Sai ka samu injin kyankyasa ko kuma kajin hausa da talotalo suna dinga yi maka kyankyasa a wata kajin akalla su ci abinci buhu 3 da rabi.

✍️ Mainas

27/03/2026
27/03/2026
The Hidden Cause of Egg Drop in Layer ChickensMany farmers focus only on feed when egg production drops, but one hidden ...
27/03/2026

The Hidden Cause of Egg Drop in Layer Chickens

Many farmers focus only on feed when egg production drops, but one hidden cause most people ignore is stress.

Stress in layers can quietly reduce egg production without obvious signs. Your birds may look healthy, but internally, their system is affected.

Common hidden stress triggers include:

* Sudden change of feed or feeding time
* Overcrowding in the pen
* Poor ventilation or too much heat
* Lack of clean water
* Frequent disturbance (noise, too many people, predators)
* Inconsistent lighting (layers need steady light hours)

When chickens are stressed, their body shifts energy from egg production to survival — and that’s when you notice fewer eggs.

What you should do:

* Keep feeding routine consistent
* Ensure proper spacing and ventilation
* Provide clean, cool water always
* Maintain stable lighting (especially for layers)
* Reduce noise and unnecessary movement around the birds

Sometimes, it’s not disease… it’s just something small you overlooked.

👉 Pay attention to your birds’ environment — that’s where the real problem often hides.

Ga formular hada abincin kaji yara wato dayold. ga Kuma matsalolin ta.Wannan ita ce formularMasara 45kgDawa 5kgDusar mas...
27/03/2026

Ga formular hada abincin kaji yara wato dayold.

ga Kuma matsalolin ta.

Wannan ita ce formular

Masara 45kg

Dawa 5kg

Dusar masara 5kg

Kuli-kuli 10kg

Waken suya 25kg

Limestone 1kg

Bone meal 2kg

Zogale 4kg

Kuka 2kg

Ginger 1kg

Idan muka kalli wannan formular ta fuska goma za mu ga yadda ta zama ba mai kyau ba ce. Akwai gyararki acikin ta.

Abu na farko shine energy break down. Domin matukar kaza ta ci abinci to sai ta dawo da karfi irin wanda abincin ya Bata. Shine energy emission wato irin zafin da zata fitar daga jikin ta.

A lissafin zafin da kaza zata fitar anan ake iya gane yawan carbohydrates content din da za,a saka mata acikin abinci.

Wanda carbohydrates content zai daganta ne daga breed zuwa breed. Haka kuma daga girman kaza. Wato yar sati nawa ce. Ba kawai Ana duba girman abinci bane.

Kusan masara, dawa da Kuma dusar masara sun mamaye abincin Yan tsakin. Da abinda yafi 3600kcl. Wanda manyan kaji Wanda s**a goge da kwai ne kawai hakan bazai basu matsala ba.

Abu na gaba kuma shine zogale, ginger da kukar miya. Wadannan abubuwan a zahiri basu da hadi da juna. Zogale growth booster ne. Kukar miya daure ciki take yi. Ita kuma ginger naganin mura ce.

To rigakafin wata cuta ce?. Ko kuwa cutar menene ake son za,ayi magani. Idan abincin Yan tsaki masu mura ne to dole sai an cire kuka.

Idan Kuma na masu kashi ne to a fara yi musu maganin kashin. Idan Kuma rigakafi ne to matsalar Bawa kaza magani rigakafi koda wana lokaci Shima yana zamar mata cuta. Saboda concentration da over feeding.

Matsala ta uku shine menene prebiotics, mycotoxin ko kuma detoxic acikin abincin?.

Wato ba formular bace matsala ba. Shin tana dauke da duk abinda ake so dan girman kaza ko kuma kawai iska aka baka.

Idan Kuma formular tana yi ya za,a Iya yiwa kaji supplements wadancan abubuwan na sama.

Matsala ta hudu shine sau nzwa za,a Bawa kaji wannan abinci a huni kuma Wana kajin ma. Ina nufin breed

Menene expectation na girman su per day. Wato in kg dauyin nawa zasu Kara kullum.

Muhammad

Growth boosterWannan ana amfani da 80g a 25kg wato a buhu daya. Amma ba'a sakashi ya wuce ka'ida don haka idan yayi yawa...
27/03/2026

Growth booster
Wannan ana amfani da 80g a 25kg wato a buhu daya. Amma ba'a sakashi ya wuce ka'ida don haka idan yayi yawa yana kyau ku sani yana saka kaji kasa tafiya musamman masu saurin girma. Wannan magani a shawarance wanda zai sakashi cikin finisher ya saka rabi 40g a 25kg(buhu 1) saboda a cikin abincin finisher akwai oyster shell wanda shi yana aiki akan hakan.
Haka kuma wannan magani ba'a bukatar yawaita baiwa kaji don haka idan za'a basu a basu a cikin sati na 3 zuwa na hudu amma sai ya kasance kaji basa girma.Ana saka shine kawai a abincin Broilers,Talo-talo da alade.
Amma a duk lokacin da aka sakashi cikin abincin kaji dole a matsa musu da bada ruwa.
Bayan an kammala hada wadannan kayayyaki waje guda sai a hada waje guda a gaurayasu yadda komai da komai zai hadu yadda ya k**ata ( idan dusar stater ce kwayar dusar ana bukatar tayi laushi ma'ana kanana-kanana, idan kuma finisher ce zata danyi kauri amma ba sosai ba daidai yadda zata rika nikewa da sauri da zarar kaji sunci.
Idan kuma mutum nason kajinsa su danyi nauyi da kumari da wuri zai iya dan kara yawan masara da 1kg da waken suya koda da 0.5 kg ne a yayin da zai kara bone meal ko fish meal da 0.5kg ( amma ayi la'akari da yawan buhunan da za'a samar kafin kara wadannan abubuwa ma'ana buhu 4,2 ko 1 ne).Anan ne ake ganin dusar wani kamfani tafi ta wani saka saurin girma wata kuma hura kaji, iya yanda ka kware wajen hada dusar iya yadda zaka morewa hadata.
A bangaren ma'auni kuma sai a nemi abinda ake kira waighing balance idan adadin da ake bukatar aunawa dan kadan ne wato a gram idan kuma mai yawa ne akwai abubuwan auna nauyi dayawa sai ayi amfani dasu
Allah ya taimaka yasa ayi cikin nasara

Domen karin bayani ko shiga shafimmu na WhatsApp a turo cikakken suna ggari
https://chat.whatsapp.com/KTbp3UM0g5LDBX97p3b2En?mode=gi_t

Call Mie Basheer Yusup  YADDA ZAKA HADA ABINCIN KAJI BROILERS IRIN NA KAMFANI A GIDAYana da matukar muhimmanci ga mai ki...
27/03/2026

Call Mie Basheer Yusup
YADDA ZAKA HADA ABINCIN KAJI BROILERS IRIN NA KAMFANI A GIDA

Yana da matukar muhimmanci ga mai kiwon kaji yasan yadda zai hada abincin kajinsa da kansa musamman masu kiwon broilers (kajin turawa na nama).
Anan zanyi bayani ne na yadda mai kiwo zai hada abincin kaji broilers mai inganci k**ar yadda kamfani keyin nasa amma a gida

KAYAN DA ZA'AYI AMFANI DASU

Kayan da za'ayi amfani dasu sune k**ar haka:

1. Masara
2. Waken soya
3. Palm kernal cake
4. Oyster shell
5. Bone meal ko fish meal
6. Vitamins da Minerals Premix
7. Lysine
8. Methionine
9. Gishiri (salt).
10. Coccidiostart
11. Growth booster

YADDA AKE HADAWA DA KUMA AWO

Kada mutum yaga na kawo kaya dayawa ya karaya duka ana samunsu a kasuwa wajen sayarwa. Bayan an siyo wadannan kayayyaki sai batu akan yadda za'a hada abincin da kuma adadin da za'a saka wajen hadin.
Da farko bari mu dauki kayayyakin daya bayan daya:

Masara:

Za'a sami masara 50kg ga wanda zai hada abinci 100kg (buhu 4 kenan) ko 25kg ga wanda zai hada buhu 2, kawai dai duk adadin da mutum zai hada zai iya samun adadin da yayi daidai da jadawalin wannan kiyasi wato kari daga kan 50kg zuwa sama ko zuwa kasa adadin dai kawai shine a raba gida biyu ko ninkawa gida biyu Misali abinci buhu biyu ana bukatar masara 25kg , buhu daya kuma masara 12.5kg. Amma kafin a auna adadin da za'ayi amfani da ita sai a nikota k**ar yadda ake bukatarta (idan stater ce sai ayi nikan yayi dan laushi, idan kuma finisher ce sai a nika ta da dan kauri k**ar yadda ta kamfani take)

Waken suya:

Anan za'a sami waken suya 10kg ga wanda zai hada buhu 4 (100kg), 5kg ga mai hada buhu 2, 2.5kg ga mai hada buhu 1. Amma anan ana bukatar waken ya kasance nikakke kar yadda nayi bayani a masara kafin a auna ko ahada da sauran kayan hadin. Amma kafin a nika yana dakyau a soyashi ya soyu yana da guba a cikin sa a tabbatar da ya soyu domin kone wadansu sinadarai da ake kira anti nutritional factors dake kawo rashin saurin nikewar abinci a cikin kaji. Yanda za'a soyashi kuma za'a nemo yashi a zuba a cikin tukunya ko kwanon suya babba a dora akan wuta a rika juyawa bayan yashin ya danyi zafi a zuba waken suyar a ciki a rika juyawa akai akai har zuwa dan wani lokaci misalin mintuna 5 har zuwa 20 idan bai soyu ba ya dai danganta da yanayin zafin wutar da aka rura take, amma anan inason mai wannan suya kada ya bari waken suyar ya kone dayawa don idan ya kone dayawa babu wani amfani da zaiyi saboda za'a kone harda masu amfanin da ake bukata don haka idan za'ayi suyar a soya k**ar yadda ake soya gida (Marau-marau ko amaro ko gyada mai gishiri).

Palm Kernal Cake:

Wannan shine ake kira da kwakwar manja, ana samunsa k**ar yadda yake a hoton da yake kasa.Idan abincin buhu 4 za'ayi sai ayi amfani da 12kg ne kawai, idan kuma buhu 2 ne da 6kg na palm kernel cake za'ayi amfani, hakakuma ga wanda zaiyi buhu 1 sai yayi amfani da 3kg a hada.

Oyster shell :

Wannan ana amfani dashi ne idan dusar finisher za'a hada domin yana dauke da calcium sosai wanda ke sakawa kaji karfin kashi wanda zai taimakawa kajin samun kafin jiki dana kafafunsu da suke tsayuwa akai. Adadi kuma idan abincin da za'a hada 100kg ne wato buhu 4 kenan ana amfani da 1kg ne na Oyster shell, idan kuma buhu 2 ne 0.5kg za'a saka, 0.25kg a buhu 1.

Bone meal ko fish meal:

Sai Bone meal ko fish meal ga wanda zai hada 100kg (buhu 4) zaiyi amfani da 3kg na Bone meal ko fish meal wato a buhu 4 kenan, idan kuma 50 kg ne (buhu 2) za'ayi amfani da 1.5kg, 0.75 ga wanda zai hada buhu 1 (25kg).

Vitamins da Minerals Premix:

Wannan shi kuma za'a zuba 0.25kg a buhu 4, 0.125kg a buhu 2, 0.0625kg a buhu 1.

Methionine:

Sai kuma a sami methionine, shi kuma za'a saka 0.3kg a buhu 4 (100kg) 0.15kg a buhu 2 (50kg), 0.75kg a buhu 1 (25kg).

Lysine:

Sai kuma lysine: Wannan shi kuma za'a zuba 0.25kg a buhu 4, 0.125kg a buhu 2, 0.0625kg a buhu 1.

Gishiri:

Wannan ana amfani dashi dan kadan, 0.2kg a buhu 4(100kg), 0.1kg a buhu 2 (50kg) ,0.05kg a buhu 1 (25kg). Gishiri yana da matukar amfani a cikin sinadaran hada abincin kaji domin idan yayi karanci matsala ce, saboda mafi yawancin abincin kaji idan kukaga yaki saka kaji girma zai iya yiyuwa tun a kamfani aka sami matsala wajen saka gishiri saboda gishiri yana budewa kaji ciki suci abinci,yana kuma saita yanayin jikin kaji yana kuma aiki a matsayin antiseptic da bada kariya wajen halittu masu hadari a cikin kaji. Amma yana dakyau a kula idan gishirin yayi yawa yana kawo matsaloli wanda s**a hada da mace-macen kaji.

Coccidiostat/Coccidiocidal
Wannan ana bukatar 0.25g a buhu daya (25kg), 100g a buhu hudu. Ana saka wannan saboda maganin cutar kashi ta coccidiosis.

Growth booster
Wannan ana amfani da 80g a 25kg wato a buhu daya. Amma ba'a sakashi ya wuce ka'ida don haka idan yayi yawa yana kyau ku sani yana saka kaji kasa tafiya musamman masu saurin girma. Wannan magani a shawarance wanda zai sakashi cikin finisher ya saka rabi 40g a 25kg(buhu 1) saboda a cikin abincin finisher akwai oyster shell wanda shi y

Address

No. 25 Dawakin Tofa LGA
Kano

Telephone

+2348139248383

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zurriyya Integrated Farms posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Zurriyya Integrated Farms:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram