11/10/2025
JARUMIN GADO: ASIRIN MALLAKAR ZUCIYAR MACE
HANKALI: Wannan karatu ne na manya (sako ne na musamman ga ma'aurata.)
'Yan uwa maza, da yawa daga cikinmu sun ɗauka cewa ciyarwa da suturarwa su ne kawai ginshiƙan riƙe aure. Mun manta da wani babban sirri mai ƙarfi da ke ɓoye a cikin shimfiɗa. Wannan sirrin shi ne gamsar da iyalinka.
Mace halitta ce mai banbanci. Jikinta da zuciyarta a haɗe suke. Idan ka gamsar da ita a shimfiɗa, ba jikinta kawai ka taɓa ba, ka taɓa ruhinta ne kai tsaye. Wannan aikin yana buɗe wasu ƙofofi a cikin zuciyarta waɗanda babu wani abu da zai iya buɗe su.
Lokacin da mace ta samu gamsuwa daga mijinta, wasu abubuwa suna faruwa a tare da ita kai tsaye:
SOYAYYARTA TANA ƘARUWA:
Tana fara ganin ka a matsayin cikakken namiji kuma jarumi na gaske. Tana jin cewa ka damu da ita kuma kana son farin cikinta. Wannan jin yana haifar da wata irin ƙauna da shakuwa na musamman.
BIYAYYARTA TANA ZAMA MAI SAUƘI:
Biyayyar da za ta yi maka ba za ta zama ta dole ba, za ta zama biyayya ce mai daɗi wacce take yi don tana son faranta maka rai, a matsayin godiya. Za ta yi maka biyayya ba don tsoronka ba, sai don SOYAYYARKA.
TANA SAMUN NUTSUWA:
Mace da take samun gamsuwa daga mijinta, tana samun kwanciyar hankali da natsuwa a ranta. Wannan yana rage rigingimu, masifa, da gunaguni a cikin gida.
FAƊAKARWA:
Ya kai maigida! Zama jarumi a gado ba yana nufin ƙarfin tuwo ba ne. Yana nufin ka zama mai lura, mai kulawa, da kuma mai son biyan buƙatar iyalinka kafin taka. Idan ka mayar da ita sarauniya a gadonka, ita ma za ta mayar da kai sarki a cikin dukkan rayuwarta.
Gado ba filin daga ba ne, filin gina soyayya ne.
Abdullahi Aliyu Boza