Duniya ma'aurata

Duniya ma'aurata ﷽ ۝ sɪʀʀɪɴ ♝ rike ♝ ℳiji ۝ ▒▒▒✎☛Godiya ga (ﷲ ) da
yabani ikon bude wanna page tsira da aminci ga annabi
ℳuhammad ( ﷺ) alayan sa da sahabban sa baki daya✎

Praise be to ALLAH the guide to his path, to whom all service is
due, and his bounties and bliss be on messeger
SIRRIN GYARA JIKI
TO AS MUCH AS POSSIBLE, EDUCATE, INFORM AND
ENCOURAGE MUSLIM WOMEN TO APPLY THE TEACHING
SIRRIN DUNIYAR MA'AURATA
WANNAN DADALIN BUDE WANNAN PAGE SABODA GYARA
ZAMAN AURE DA DAIDAI TA ZAMAN AURE

MUHIMMANCIN AURE A ADDININ MUSULUNCI DA RAWAR DA IYAYE ZA SU TAKA AKAN TARBIYYAR YARADAGA Shapiu H abdullah Nata...✍🏿Aur...
23/04/2021

MUHIMMANCIN AURE A ADDININ MUSULUNCI DA RAWAR DA IYAYE ZA SU TAKA AKAN TARBIYYAR YARA

DAGA Shapiu H abdullah Nata...✍🏿

Aure abu ne mai matuƙar muhimmanci a addinin Musulunci. Manzon Allah S.A.W ya faɗa cewa "A lokacin da ɗan adam ya yi aure, ya cika rabin addininsa". Sannan kuma Manzon Allah S.A.W ya ƙara da cewa: "Aure Sunnah ta ne, duk wanda ba ya tare da Sunnah ta ba ya tare da ni". Manyan dalilan da su ke sa wa a yi aure sun haɗa da:

-Domin ba wa maza da mata damar rayuwa tare cikin farin ciki da ƙaunar juna bisa dokokin addinin Musulunci.

-Domin a samar da ƴaƴa da gina al'umma tagari.

-Domin samar da haɗakar da shari'a ta amince da kuma kare mutunci da rayuwar al'umma daga kowane irin ƙasƙanci.

Daɗi da ƙari aure abu ne a tsakanin maza da mata domin ƙaunar juna da zamantakewa mai ɗorewa da samar da kykkyawan yanayin da za su tarbiyantar da ƴaƴansu su taso su na masu taƙawa da tsoron Allah. A wannan zamani da mu ke ciki mutuwar aure ta zama ruwan dare. Wannan dalili ya sanya ya zama lallai mu gujewa wannan mummunar ɗabi'a ta yawan mutuwar aure, mu zamar da gidajen aurenmu su zamto tamkar Aljannar Duniya. Babbar hanyar da za mu bi wajen kaucewa ruɗun wannan duniya shi ne mu sanya tsoron Allah a cikin zukatanmu.

A matsayin goyon bayan aure, iyaye su na da muhimmiyar rawar takawa wajena taimako da ba da jagoranci da nusarwa ga ma'aurata. Akwai buƙatar su yi amfani da ƙwarewarsu da hikimarsu su nusar da su duk abin da ya dace game da wannan lokaci mai wahala na rayuwar aure. Su kuma ba su dukkan wani haɗin kai da goyon baya da gudunmawar da su ke buƙata ba tare da yin katsalandan kan abin da bai k**ata ba.

Farkon aure abu ne mai matuƙar muhimmanci. Akwai buƙatar mu yi duk mai yi yuwa domin samun yardar Allah. Iyaye su tabbatar da Taƙawa a matsayin mahaɗi mai matuƙar muhimmanci game da auren ƴaƴansu. A wannan zamani wasu daga cikin iyaye idonsu ya rufe sun ruɗu da ruɗunin duniya, abin duniya su ke kallo wajen aurar da ƴaƴansu a madadin su maida hankali wajen yi wa ƴaƴa zaɓin abokan aure nagari. Da dama daga cikin iyaye su kan duba matsayin mutum a muƙami ko tarin abin duniya ko wata alfarmar duniya kafin ba da aure wanda hakan ne kuma ya ke haifar da mummunan zaɓi.

Akwai wani labari mai daɗi da ya faru zamanin Khalifancin Hazarat Umar R.A a lokacin da ya ke gudanar da zagayen sirri domin duba halin da talakawansa su ke ciki sai ya ji wata tattaunawa a tsakanin wata uwa da ƴarta. Uwar ta na faɗawa ƴarta cewa ba ta samun riba mai yawa idan ta saida madara ko nono a saboda haka za ta ƙarawa nonon ruwa domin ya na yin yawa tayadda za ta na samun riba mai tsoka. Nan take sai ƴar tata ta ce da ita: "Ba za mu yi ha'inci ba". Duk da cewar a lokacin su ba musulmai ba ne.

Uwar ta yi ƙoƙarin gamsar da ƴarta akan su yi algus na haɗa ruwa da nono tunda babu Khalifa ko wani shugaba da ya ke ganinsu, amma ƴar ta ce sam ba za a yi ba, ya zama wajibi su bi koyarwar addinin musulunci domin in babu wanda ya ke ganinsu to Allah ya na ganinsu kuma ba za su kuɓuta daga girbar abin da su ka shuka ba.

Wannan kykkyawar ɗabi'a da wannan ƴa ta bayyanawa mahaifiyarta ta yi matuƙar burge Khalifa Umar R.A. inda sannu a hankali ya tura mutum ya sayo nono a gun wannan yarinya domin ya ga an yi algus da ruwa ko ba a yi ba, a lokacin da ya gano cewa lallai yarinyar nan ba ta bi umarnin haɗa nonon da ruwa ba sai ya bayyana cewa: "

"Wannan yarinya za ta zama uwa tagari mai girma. Nauyin Nagartarta ba ta tsaya a matsayin kuɗi ba ne, za ta kasance ne a matsayin auna mizanin nauyin ƙasa. Zan karrama ta da lambar yabo mai girma a matsayin kyautata, sannan kuma za ta kasance babban muradin ƙasa.

Khalifa Hazarat Umar ya sa an kawo masa yarinyar da mahaifiyarta fadarsa inda ya gabatar da ita ga ƴaƴansa ya buƙaci ɗaya daga cikinsu ya aure ta, "Wannan za ta kasance uwa tagari. Na sani babu wata amarya tagari sama da wannan mai kykkyawar ɗabi'a. Ba ta da matsayi a duniyance da za a lissafa, amma ta na da nagartar da za ta zama uwa tagari".

Asim ɗansa na uku wanda ba shi da aure shi ne ya auri yarinyar ta zama surukar Khalifan, daga jikokinsu aka samar da Hazrat Umar Bin Abdul'aziz wanda ya zama babban Khalifan Musulunci wanda ya jaddada nagarta da sauƙin kansa. Wannan lamari da ya faru ba zato ba tsammani ya nuna muhimmancin tarbiyyar yara da kykkyawar ɗabi'arsu irin ɗabi'un da ya k**ata mu nema a ya yin neman matar aure. Manzon Allah S.A.W ya faɗa cewa "babu wani gata da uba zai ba wa ɗansa sama da ɗora shi kan kykkyawar ɗabi'a".

29/01/2021

Zo kiji ƴar'uwata. (1)
Kin san Allah! Duk saurayin da zai dinga yi miki
daɗin baki yana shafar wasu sassan jikin ki,
ya fake da cewa tsananin Sonki ne ya jawo
hakan, to kar ki yarda da shi, gungumemen
macuci ne, mayaudari. A taƙaice ma bai san So ba,sha'awa kawai ya sani.
So na gaskiya nisantar sha'awa yake yayin neman aure, bazai
taɓa sawa ya shafi wasu sassa na jikinki ba.
So na karya kuma; manne suke da shaawa, don
ita ce ma jigon shi.
Duk wanda ke miki son gaskiya, wallahi ba zai
taba sha'awar k**a ko da hannunki ba ne, bare
ma har a wuce gona da iri.
Wata za ka ji ta ce
"Ai an sa mana rana da shi aurena zai yi"
Ko kuma
"Ya kawo kuɗin aurena ai shi ke nan!"
To bari ki ji: Ko aurenki ya yi, ba za ki taɓa jin
daɗin shi ba. Ko da kuwa kin ji, to na dan lokaci ne.
Domin kuwa don wani abu da yake sha'awa a
jikinki ya aure ki, kuma da ya kau, sonki shima zai kau a ran shi, shikenan ke ma sai ya kau da ke.
Ko da yake ! Laifinku ne ma wasu lokutan!
Yanzu in ka je hira wajen yarinya sau ɗaya sau
biyu, kuna bada tazara a tsakaninku gudun
hakan, sai ka ji ita da ƙawayenta na cewa; bai waye ba ne! Ko kuma; ina jin ma ba shi da lafiya ne!
Ka ji fa hauka!
Yoo in yana da lafiya shi Bunsuru ne da zai nuna
miki lafiyar tashi a kan t**i?
Wace iriyar wayewa ma k**e magana? Bayan ga
Iyayena da naki can a gida su ma ba su wayen
ba?
Shin wai ma in tambaye ki? Kina kallon fuskar ki
a mudubi kuwa? Ya kalar fatar jikin ki take?
Amma k**e kwaikwayo halayyar jar fata (Yahudawa) ? Ta yaya ma
k**e tsammanin za ta dace da ke?
Allah kyauta!
Allah Ya kawo mu lokacin da mata s**a maida
kan su maza, don haka ba sa tsoro.
Yanzu
wata macen ma wallahi sai dai kai ka ji tsoronta,
ta zama namiji ka zama mace!
Da ka yi magana sai ace maka; wayewa ce! Ni
dai Shapiu Nata na yi turrrr! Da wannan wayewar me
Ɗauke da tikitin shiga wuta kai tsaye😭

24/01/2021

WASU KURA KURAI DA MATAN AURE SUKE YI 'YAN AIKI KE AURE MAZAJEN SU
~~~~~~~~~~~~~~~•••••••••••~~~~~~~~~~
Ba sabon abu bane aji cewa' yar aiki ta aure maigida ko kuma ta kori uwar gidan ma gaba daya.
Wannan matsalar yana faruwa ba tun yanzu ba. Wanda kuma har wannan lokacin wasu matan sun kasa ganewa sune ke jawo hakan da kansu har abun yazo kuma ya damesu.
Mafi yawan mazaje sun fi son 'yar aiki mace ta kula da aiyukan cikin gida maimakon namiji saboda da dalilai na tsaro. Wasu matan kuma sun gwammace namiji yayi musu aiyukan gidan domin gudun kada su kawo wacce zata iya musu illa. Amma da yake maza sun fi karfin su a daukar matsayi hakan yasa wasu matan suke saduda amma ba domin suna so ba.
Sai dai kuma matan ke jawo matsalar da suke fuskanta da 'yan aikin su da kansu. Domin sune suke zaban wacce zata musu aikin ba Mazajen su ba.
Ga wasu kurakuren da mata suke yi har yan aikin su ke zama kishiyoin su.
1: DAUKO WACCE TA FITA WAYO:-Mata da dama idan sun tashi dauko' yar aiki a rashin sani sai su dauko macen data fisu wayo a badini amma a zahiri tayi k**a da doluwa.
Irin wadannan matan basa yadda su fito da fiskarr kyaun su na asali idan zasu je neman aiki. Sai suyi biji biji yadda mace idan ta ganta tamkar wata abar tausayi. Amma da zaran ta saki jiki zata soma fito da Halittun ta yadda duk wanda ya ganta zai kyasa.
2:- SAKA SU AIYUKA NA MUSAMMAN: Akwai wasu aiyukan da duk rashin son aikin mace ita ya k**ata ta yiwa mijin ta shi amma ba ta saka wata ta yi masa ba muddin dai ba yar cikinsa bane.
Aiyuka irin na gyaran dakin miji. Yiwa miji girki fita da miji sayayya duk bai dace mace ta bari 'yar aikinta ta ke mata ba.
3:- BARIN YAR AIKI TA FAHIMCI MATSALARKI DA MIJINKI:- Muddin zaku bari' yar aiki tana fahimtar abunda yake hadaki da mijinki sabani to tabbas zata iya amfani da wannan damar ita kuma ta rika daɗada masa da abun, yadda har zai soma sha'awar inama itace Matarsa. Don haka ki kiyaye hira da yar aiki akan matsalolin ki da mijinki.
4:- SAKA SUTURAN DA ZAI FITO DA SURAR TA: Kada ki ji kunyar taka mata burki muddin kika fahimci cewa 'yar aikin ki tana son rika shiga irin wanda zai rika fito da Surar ta a gaban mijinki.
Ana iya samun wani wasu Halittun ta da s**a fi naki da magida zai iya sha'awar su wanda hakan zai zama tarkon da zata k**ashi da su.
5:-.DAUKAR' YAR AIKIN DATA FIKI KYAU: duk kuwa da namiji a wani lokacin ba kyaun mace bane a gaban sa ba. Amma daukan yar aikin data fiki kyau tamkar kin Gayyatowa kanki matsala ne da kanki. Gara dai wacce kika fi kyau koda wani abu ya kasance za a zarge shi amma ba ke ba.
6:- BAIWA 'YAR AIKIN DAMAR KAWAI MIJINKI ABINCI: Cikin Sauki' yar aikin da take son aure miki miji zata iya amfani da wannan damar domin ganin ta ciyar dashi wani shirin da zata iya juya masa kansa ya ji ita yake so.
7:- WULAKANTA BAKI A GABAN TA: Idan kina wulakanta bakin mijinki a gaban yar aikin ki Ita kuma zata yi amfani da wannan damar wajen kyautata musu har ta shiga ransu. Hakan kuma zai bata damar samun shiga wajen mijinki cikin sauki ta hanyar wadannan da k**e wulakanta wa ita kuma tana daðaɗa musu.
8:- WANKE MASA KANANAN WANDUNANSA:- Akwai wani sirri na musamman a wanke kananan wanduna. Duk ma'auratan da suke wanke wa juna kananan wandunansu soyayya da kauna na musamman yana kara shiga tsakanin su. Don haka idan kika bar 'yar aikin ki ita ke wanke masa kuma ta goge masa sai aji a ranta inama itace abunda ke adana wandon nan yake shiganta. Don haka ki kiyaye.
9:- BATA DAMAR YIN HIRA DA MIJINKI:-Idan kika baiwa yar aiki mai wayo damar yin hira da mijinki cikin sauki zata iya aure miki miji. Domin zata iya amfani da Kalaman data san baki masa domin jawo hankalinsa.
10:-RASHIN BAIWA MIJI LOKACI: Idan kin kasance irin matan nan ne da s**a damu da harkokin gabansu amma basu damu da kula da miji ba to a kwana a tashi zaki tsinci kanki cikin matan da 'yar aiki ta aure Mazajen su.

05/01/2021

Muna haɗa maganunnuka wanda s**a shafi traditional medicine,
Kamar na gyaran Nono
Kara kuzari
Sanyi
Kaurin gaba
Girman Nono
Girman ƙugu
Basir
Bada shawara a zamantakewar Auren ko kafin aure.
Dds....

23/09/2020

Ga araha ga amfani: Fa'idoji 6 dake tattare da cin dabino
Author: Shapiu H Abdullah Nata
Shapiunata@gmail.com
Dabino yana daya daga cikin 'ya'yan itatuwa masu matukar amfani ga jikin adam saboda irin sinadaren da ya dauke dashi. Dabino yana girme ne a bishiya kuma 'ya'yan na cure ne kuma ya fi son yanayi mai zafi.
Bayan 'ya'yan dabinon sun nuna ana iya cinsu hakan nan kokuma a cire kwallon da ke ciki a sarrafa su ta wasu hanyoyin don more lagwada da amfanin da dabinon ke dauke dashi.
Ga dai wasu fa'idoji guda shida da dabino keyi a jikin dan adam.
1) Dabino nada tasiri wajen kara kuzari ga masu aure:
Binciken masana kimiyyan sinadaren abinci ya nuna cewa dabino yana da matukar muhimmanci wajen kara kuzari tsakanin ma'aurata.
Domin samun wannan fa'idar, sai mutum ya debi dabino k**ar cikin hannunsa ya jika su cikin nonon akuya su kwana, da safiya sai a marka dabinon tare da nonon kuma ana iya kara zuma da cardamom.
Wannan hadin yana da mutukar amfani wajen inganta kwanciyar aure.
2) Maganin gudawa
Dabino da ya nuna sosai yana dauke da sinadarin potassium wanda ke da mutukar muhimmanci wajen magance gudawa.
Sinadarin fibre da ke cikin dabino kuma yana taimakawa wajen magance basir da sauran matsalolin da ke da alaka da fitar bayan gida da gyaran ciki.
3) Lafiyar zuciya
Dabino yana da matukar amfani wajen karawa wa zuciyar dan adam lafiya. An fi samun fa'idan da ke cikin dabinon idan an tsoma shi cikin ruwa ya kwana sai a dauko a ci da safe. Hakan yana da matukar amfani ga masu fama da ciwon zuciya.
Sinadarin Potassium da ke cikin dabinon yana kare buguwar zuciya da wasu cututuka masu k**a da hakan.
4) Karin kuzari
Dabino na dauke da suga wanda basu da ila ga jikin dan adam k**ar glucose, fructose da sucrose. Saboda hakan duk lokacin da mutum ke jin kasala idan yaci dabino zai samu kuzari nan take.
5) Karfafa garkuwan jiki da magance allergy
Wani abin mamaki game da dabino shine yadda take dauke da sinadarin sulphur wanda ba'a cika samunsa a 'ya'yan itatuwa ba amma kuma yana da matukar amfani da jikin dan adam cikinsu kuwa harda kara karfin garkuwar jiki da magance
6) Yana taimakawa masu son mayar da jikinsu
Dabino na dauke da suga, sinadarin Protein da ke gina jiki da kuma vitamins. Kilogram daya da dabino na dauke da calories 3,000 wanda hakan sun isa jikin dan-adam biyan bukatun ta na kwana daya.
Idan mutum ya rame kuma yana son mayar da kibansa, dabino na iya taimakawa wajen gina jiki sai mutum ya jibinci cin dabinon.

Shawara ta 1YAYA ZA KI ZABI MIJIN KIKi kyautata zaben mijin ki, ki sani rayuwar aure ba ta dawwama sai da fahimtar juna ...
16/09/2020

Shawara ta 1
YAYA ZA KI ZABI MIJIN KI

Ki kyautata zaben mijin ki, ki sani rayuwar aure ba ta dawwama sai da fahimtar juna da soyayya, sanna kuma kina daukaka shi fiye da kowa, shima yana fifitaki fiye da kowa

Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace a lokachin da yake koyawa budurwa yadda zata zabi mijinta abokin rayuwar ta

“Idan wanda kuka yadda da addinin sa da halayyar sa, ya zo muku toh ku aura masa, idan baku aikata ba barna da fasadi mai girma zai faru”

Wani mutum ya cewa Imam Hasanul basari: hakika ina da yarinya wacce na fi son ta cikin mutane
Wa kake ganin ya k**ata na aura masa ita?
Sai yace
Ka aurar da ita ga wanda yake kiyaye dokokin Allah madaukakin sarki
Idan yana son ta zai girmamata
Idan baya son ta ba zai zalince ta ba

An fadawa wani mutum mai hikima: Wane yane neman auren wance
Sai yace
Shin mawadachin hankali ne da addini?
Sai s**a ce: eh
Sai yace: ku aura masa ita

Ana bada labari cewa Nuhu dan Maryam alkalin garin Marwi yaso ya aurar da yar sa
Sai ya nemi shawarar makwabchin sa wanda bamajuse ne
Sai yace: tsarki ya tabbata ga Allah ana neman fatawa a gun ka kuma kai ne kake tambaya ta?
Sai yace: dole sai ka bani shawara
Sai bamajusen yace: Hakika kisrah sarkin farisa ya kasance yana zabar dukiya
Sarkin Rumawa kuma Qaisar yana zabar dagantaka da nasaba
Shugaban ku Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam yana zabar addini
Sai ka duba dawa za kayi koyi.

Ke ma dawa za kiyi koyi?
Wa zaki zaba a matsayin mijin ki?

Mai kudi?
Ko Dan dangi?
Ko mai addini?

Shawara ta rage taki ya yar uwa musulma
Allah ka azurta yan uwan mu mata da mazaje nagari
©Shapiunata@gmail.com

23/07/2020

GYARAN JIKI FATA TAYI LAUSHI DA SHEKI
Copyright BY: Shapiu Nata
EMAIL: Shapiunata@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: Duniyar ma'aurata
Kayan Hadi.
Man zaitun
Lallae
Kurkur
Madarar ruwa
Zaki hade wannan kayan guri daya sai ki kwaba ki shafe jikin ki da fuskarki Idan ya bushe sai ki murje sannan ki yi wanka.
SABULUN KURAJE
asef soap
pharmaderlm soap
kanwa
jar dilka
Zuma
lemon tsami
Ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, kinkwaba dilka da ruwan zafi cikin cokali cin abinci daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa Zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki k**ar ya rage minti biyar kafin ki shiga wanka, Indan kin shiga wanka sai ki kuma wanke fuskarki da sabulun k**ar uku ko Dama da haka.
SABULUN WANKA NA BAKAR MACE
sabulun salo ko sabulun Ghana
magiji.
Zuma
lemun tsami.
zaitun
a hada sabulun Ghana da magiji a dake a zuba Zuma a matsa lemun tsami kadan a saka man zaitun cokali daya a bada a kwaba, bakar mace da bata son tayi fari sai ta dinga wanka da shi, zai sa tayi kyau

26/06/2020

ALAMOMIN PERIOD KAFIN ZUWANSA
DA SATI 1 KO 2
////k**al.salis.dalhat
macce wadda zatayi Al ada kanji abubuwa da
yawa kafin zuwan al ada wato period
Wanda kusan mata da yawa sun dauka
wata babbar cutace Wanda ba
cutabace faruwa wasu abubuwane da
ake cema (ovulation discharge) and
(dysmenorrheoa) wato pain
juring period Wanda lokacinda eggs wato
o***y keyin kyakyasa akejin wanan radadin
da lokacinne abubuwa kanfaru k**ar
haka kuma ba ciwo bane kuma ba cutabace
matan kanjin abubuwa k**ar haka kafin
zuwan al
ada ko lokacin al ada
1.abdominal pain ciwon Mara
2.ciwon baya
3.ciwon kai
4.ciwon kafafu
5.fushi
6.kumburin fuska
7.jin alamun zazabi
8.jin zafi a breast
9.ciwon Kai
10.rashin karfin jiki
11.fitar fararen ruwa a farji masu karnin kwaii
12.ciwon jiki da ciwon kai
da sauransu
wanan duk ba matsalabace ko ciwo
lokacinda (ovulation.keyin aikine domin
kyakyasar egg) lokacinda.estrogen and
progesterone keyin yake lining na
blood da kuma afkuwar fadowar ovaries
yayin progestrone keyin aikinsa ananne
ciwon mara ko ciwon kai ke faruwa
kokuma kafin zuwan al adar
sha wari idan anji hakan kafin zuwan al
ada ko lokacinta
1.yin amfanida analgesic magani domin
rage radadi
2.kulada tsabtar jiki
3.kulada saka (always pad ) yayin al
ada
4.canza always akalla sau 3 a rana
5.kada kisaka ragga ko tsumma yayin
al ada
6.yin amfanida ruwan dimi yayin tsarki
7.kada a kuskura asha maganin
gargajiya domin rage radadi
8.kada asha ruwan sanyi sedai ruwan dimi
da sauransu
ALLAH YABADA
Written ✍ by Shapiu H Abdullah Nata

Address

Nigeria Kana
Kano
DALA

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2347065498318

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniya ma'aurata posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Duniya ma'aurata:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram