30/10/2024
Maigidanmu, Manzon Allah صلى الله عليه وسلمAnnabin gaskia ne, Annabin cika Alkawari ne 👇
Zaka fahimci cewa wallahi Manzon Allah,صلى الله عليه وسلم Manzon Allah ne acikin Qissoshi da Hadisai Ingantattu, Shin Ko kasan alkawarin da Manzon Allah صلى الله عليه وسلمYayi wa Suraqa Bin Maliq tun yana raye Sai bayan mutuwar Manzon Allahصلى الله عليه وسلم alqawarinsa yacika??
Suraqa Bn Maliq yanadaga cikin sahabban Manzon Allahصلى الله عليه وسلم masu dogon tarihi, Wanda Yayi hidima wa musulunci , lokacin da Manzon Allah صلى الله عليه وسلمzaiyi hijira zuwa garin Madina don Addinin Allah Yasamu wajen Zama akan hanyarsa Shi da abokinsa Sayyidina Abubakar S**a hadu da Suraka Bn maliq anan suraqa yakarbi musulunci yace zaiyi aiki wa addini da Manzon Allah.صلى الله عليه وسلم
~ Yayin da Manzon Allah صلى الله عليه وسلمyajuya Zai tafi garin Madina suraqa Yace 'Ya Manzon Allah صلى الله عليه وسلمkamun Kyauta Wanda bazan taba mantawa da ita ba, Manzon Allah صلى الله عليه وسلمYace kasan "Kanbin zinare 👑" na Kan Sarkin farisa Sarki Qisra.
Suraqa Bn Maliq yace 'Eh ya Manzon Allah nasanshi , Manzon Allahصلى الله عليه وسلم Yace kaje nabaka Shi Kyauta , Yace Manzon yaushe Zan karbi wannan "Kanbin 👑" Annabi Yace bansani ba amma dai za'a baka Shi kaje, Suraqa Bn Maliq yace 'ya Manzon Allahصلى الله عليه وسلم Ko Zaka rubutamun arubuce don nasamu evidence Annabi Yace 'Eh a rubuta masa Sayyidina Abubakar yadauki paper 📜 da biro yarubuta masa Kyautar da Annabi yamasa.
Bayan Shekaru Manzon Allah,صلى الله عليه وسلمya rasu Sayyidina Abubakar Yarasu Sai Zamanin kalifancin Sayyidina Umar Bn Kathab Yatara mayaka da sojoji Yace aje ayaki Sarkin farisa Sarki Qisra, aka Yaki Sarki Qisra aka ci ganima akansa aka dauko wannan "Kanbin Zinare 👑 na sarkin farisa" , Suraqa Bn Maliq yaji labarin "Kanbin 👑 Sarki Qisra" an sameta cikin ganima Sai ya Hau doki Sai fadar Sayyidina Umar Bn Kathab tare da Wannan takardar 📜 Kyautan da Annabi ya masa.
~ Suraqa Bn Maliq Yana zuwa Sai yace wa Sayyidina Umar Bn nazo karban "Kanbina 👑" Yace Wani "Kanbi" Yace kanbin Sarki Qisra Umar Bn Kathab Yace Waya baka Yace Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
Yace ina hujjarka daza tanuna cewa Annabi Yabaka wanann "Kanbin👑" yadauko takardar 📜 da Annabi ya rubuta masa ana budewa Sai akaga an rubuta :
" لقد أمر رسول الله صلى الله عليه وسلم لي سورقة بن ملك عن يلبس سواري و تاجه كسر"
"Hakika Manzon Allahصلى الله عليه وسلم Yayi umuri wa Suraqa Bn Maliq da ya sa Kanbin👑 Sarki Qisra".
Allahu Akbar nan take Sayyidina Umar Bn Kathab Yace wannan rubutun rubutun sayyidina Abubakar ne , don Umar yasan Abubakar bazaiyi Karya wa Manzon Allah صلى الله عليه وسلمnan aka Miki wa Suraqa bin Maliq Kanbin Sarki Qisra👑, Wanda Sai bayan rasuwar maigidanmu, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Allah yaci masa alkawarin da Manzon Allah صلى الله عليه وسلمYayi masa.
Wannan Shi Zai Kara maka yarda da Manzon Allah صلى الله عليه وسلمcewa Annabi manzone nagaske Kuma daga Allah , baya Magana bisa son rai da zucia (صلى الله عليه وسلم.🥰
By Nura Ashiru twd