Health talk free.

  • Home
  • Health talk free.

Health talk free. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Health talk free., Medical and health, Kofar Fada Kankara, .

Nafahimci Mata Dayawa Sun kasa gane wannan matsalar meyasa take faruwa dasu.........Kin taɓa mamakin dalilin da yasa iri...
25/10/2025

Nafahimci Mata Dayawa Sun kasa gane wannan matsalar meyasa take faruwa dasu.........
Kin taɓa mamakin dalilin da yasa irin wannan kurajen basa bacewa daga fuskar ki, ko kirjin ki, awasu lokutan harda wajen private part na mace? 😳
Kuma idan kikaje Asibiti sai ace Miki bakida infection, kokuma ayita Baki cream Kala kala Amma kuraje Suki tafiya......

Toh kusani mafi yawanci ba matsalar fatar jiki bace, matsalar hormones ne........

Idan hormones s**a rikice, sai kuraje su fara fitowa ko ina, ko kina da tsabta ko kina amfani da magunguna masu tsada ko mayuka masu tsada 😔

Wasu suna ta kashe kuɗi akan creams da tablets amma basu san tushen matsalar na cikin jininsu bane......
Akwai wadda tace mun ta sayi Marine collagen supplement akan wannan matsalar har Naira 72,000 Amma kurajen sunki tafiya, Kuma batasan adadin kudin da ta kashe ba akan wannan matsalar ta hormonal Acne.....

Kawai nayi dariya nace Allah sarki abinda zayyi miki Maganin wannan matsalar tayiyu ko 2,000 ba lallai yakai ba, Amma kinata Bata kudin ki.......

Inada tambaya Duk shafe shafen dazakuyi irin wannan kurajen suna tafiya kuwa?????
Ku rubuta Mana a comment section

24/10/2025

*JI KA KARU*

*Rashin nagarta ta mahaifa da tsananin zirga zirga ga mace na daga cikin ababen dake sa yawan zubar da ciki a kula*

*Shima kalar jinin mace na daga cikin ababen farko da ake la'akari dasu wadanda ke sa zubewar ciki ga mace.*

*Dabi'ar yawan shan magunguna barkatai ga mace shima sila ce daka iya sa ciki ya rika zubewa ga mace.*

*Harga ALLAH idan mace nada alamun hawan jini, ciwon koda da sugar da Cutukan makoshi zasu haifar da yawan Zubewar ciki.*

*Mata masu gajerun mahaifa da wadanda ke dauke da kwayoyin cutar sanyi irin su PID suna sa zubewar ciki.*

🧫 Ma’anar TB (Tuberculosis)Tuberculosis (TB) wata cuta ce mai tsanani wadda kwayar cuta mai suna Mycobacterium tuberculo...
13/10/2025

🧫 Ma’anar TB (Tuberculosis)

Tuberculosis (TB) wata cuta ce mai tsanani wadda kwayar cuta mai suna Mycobacterium tuberculosis ke haifarwa.
Cutar na fi yawa tana k**a huhu (lungs), amma tana iya k**a wasu sassan jiki k**ar ƙashi, koda, kwakwalwa, da lymph nodes.

🦠 Dalilin Cuta (Causative Agent)

Kwayar cutar da ke haifar da TB ita ce:
👉 Mycobacterium tuberculosis
Wani lokaci kuma nau’o’in Mycobacterium bovis ko Mycobacterium africanum na iya haddasa ta, amma su ba su da yawa k**ar ta farko.

😷 Yadda TB ke Yaduwa (Mode of Transmission)

TB tana yaduwa ne ta iska:

Idan mutum mai TB ya yi tari, atishawa, ko magana, ƙwayar cutar na fita cikin ƙura mai santsi (droplets) a iska.

Mutum mai lafiya idan ya shaki wannan iska, zai iya kamuwa da cutar.

> Ba a yawan samun TB daga abinci ko ta jini, sai dai idan an sha madarar saniya mai cutar TB (Mycobacterium bovis).

⚠️ Alamomin TB (Signs and Symptoms)

TB ta huhu (Pulmonary TB):

1. Tari mai ɗaukar lokaci fiye da makonni biyu (2).

2. Tari da jini ko majina mai duhu.

3. Zazzabi mai sauka da hawa, musamman da dare.

4. Gumi mai yawa da dare.

5. Asarar nauyi sosai (mace ko namiji ya rame).

6. Rashin sha’awar abinci.

7. Jin rauni da gajiya sosai.

8. Wahalar shakar iska.

TB a wasu sassa (Extrapulmonary TB):

Koda: Fitsari da jini, ciwon gefe.

Ƙashi: Ciwon ƙashi, kumburi, ko lanƙwasawa.

Kwakwalwa (TB meningitis): Ciwon kai, amai, suma, da rashin iya magana.

Lymph nodes: Kumburin wuya da ba ya ciwo.

🧪 Hanyoyin Gano TB (Diagnosis)

1. Tari da jini (Sputum test): Ana bincikar kwayar cuta a dakin gwaje-gwaje.

2. Chest X-ray: Don gano ko huhu sun sami matsala.

3. Tuberculin skin test (Mantoux test): Ana saka sinadari a fata, idan fata ta kumbura, alama ce mutum yana da TB ko ya taba kamuwa.

4. GeneXpert test: Gwaji na zamani da ke gano kwayar TB cikin lokaci kaɗan.

5. Culture test: Ana girma da kwayar a dakin gwaje-gwaje don tabbatarwa.

13/10/2025

GA WASU DALILAN DA KAN JAWO RASHIN MOTSIN JARIRI A CIKIN MAHAIFIYA

1. 💤 Jariri yana barci: A wasu lokuta, jariri kan sami lokacin hutawa (barci) na sa’o’i kaɗan, wanda ke sa ba a ji motsi sosai ba.

2. 🍞 Ciwon yunwa ko ƙarancin abinci a jikin uwa: Idan uwa bata ci abinci ko bata sha ruwa sosai ba, jariri zai iya rage motsinsa saboda ƙarancin mak**ashi.

3. 🩸 Karancin iskar oxygen zuwa jariri: Wannan na faruwa idan akwai matsala a placenta (gishirin uwa) ko a umbilical cord (jijiya).

4. 🩺 Matsalolin lafiya na uwa:

Ciwon hawan jini (pre-eclampsia)

Ciwon s**ari (gestational diabetes)

Zubar jini ko ƙuruciyar mahaifa (placental abruption)

5. ⚠️ Mutuwar jariri a cikin mahaifa (stillbirth): Idan babu motsi gaba ɗaya na dogon lokaci, hakan na iya nuna cewa jaririn bai raye ba — wanda ke buƙatar gaggawar likita.

6. 💊 Amfani da wasu magunguna: Wasu magunguna, musamman masu kwantar da jiki (sedatives), na iya rage motsin jariri.

7. 🧍‍♀️ Yanayin uwa: Idan uwa tana cikin damuwa, gajiya, ko ta kwanta a wani wuri na tsawon lokaci, hakan na iya rage jin motsin jariri.

---

Abin da ya k**ata a yi:

Idan kika lura jaririnki bai motsa k**ar da ba, ki:

1. Ci abinci mai sauƙi (irin su ’ya’yan itace ko shayi mai ɗan zaki) sannan ki kwanta gefe ɗaya (musamman gefen hagu).

2. Ki lura da motsi a cikin awa 2 – a kalla ya k**ata a ji motsi sau 10.

3. Idan ba ki ji motsi ba, je asibiti nan take don a duba jariri da ultrasound ko fetal monitoring.

04/10/2025

Akwai alaka tsakanin wasu cutukan da kuma canjin yanayi, a fahimci Wannan lokaci da muke ciki ana cikin zazzabi mai zafi, tari, zafin makoshi, mura, ciwon kai da ciwon gabobi.

Meyasa ❓❓❓

04/10/2025

Ya k**ata a ankare anya ba Alamun coronavirus bace mutane ke fama da ita ❓

Amma tsananin ciwon kai, abune mai sauki ga wasu daga cikin cutuka masu yaduwa musamman mura ta influenza, encephalitis, meningitis, HIV, da COVID ko kuma ma sepsis.

Wallahi Mutane na cikin zazzabi mai zafi.

04/10/2025

TAMBAYA DAGA MEMBER

Aslm Dr don Allah inada tambaya ka taimakeni.

Wllh Dr Tunda nayi bari haryau period Na bai saida taba.Yenzu wata biyu kenan august period Na yadawo amma bajini ne yeke zuwaba wani abune brown yake fitamini. Amma haka Na lissafa kwanakin am'adana yana cika 7 days saiya dauke.

To Wannan watan da muka fitakuma tun on 22 yafara Xuba sauna tapasa ganyen gwaiba da kanwa don yawankemin marana to sai wani baqin Dotti da danjini jini kadan yakefita amma nagama lissafa kwanakin al'adana bai tsayaba nayiwanka nacigabada ibadana gabana kuma ya daye Ga kaikayi idannasosa kuma sai gurin yadaye har yana fitarda jini don Dr me matsalata kataimaka min intak**a yafiya asibitima zantafi.

AMSA

Daga bayanin da kika bayar, alamu suna nuna cewa matsalar da k**e fama da ita tana iya zamowa cutar halittun haihuwa ne (reproductive tract infections), ko sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinki (hormonal imbalance) wanda yake hana al’adarki tafiya yadda ya k**ata. Wannan ne yake sanya jinin ya rika fitowa ba bisa ka’ida ba, ko kuma ya zama ruwan kasa maimakon ja-zur.

Yin amfani da ganyen gwaiba ko kanwa wajen wanke mara ko farji yana da hadari. Idan kinyi amfani dashi ne wajen wanke gabanki, to, yana iya lalata sinadaran kariya da suke cikin farjinki (normal vaginal flora), yana iya jawo miki infection k**ar candidiasis da PID, ko kuma ya haddasa miki zubar jini, kaikayi, da kumburin farji. Idan kuma sha kikayi, to, kanwa tana ɗauke da sinadaran sodium carbonate masu ƙarfi zasu iya lalata miki hanji, ko mahaifa, ko koda matukar k**e dimanci shanta a koda yaushe. Game da shan ganyayyaki kuma, wasu suna iya rikitar miki da tsarin hormones dinki har su jawo rashin haihuwa, zubewar ciki, ko zubar jini maras ƙa’ida.

Ba za'a iya baki cikakkiyar amsa a nan ba sai kinje asibiti anyi miki gwaje-gwaje k**ar pelvic examination, urine test, da ultrasound domin gano musabbabin matsalar.

A fuskar addini kuwa, idan jinin yana da siffofin jinin

02/10/2025

Tsananin zazzabin cizon sauro ga mace na iya sa al'adar mace ta zarce zuwa wata na gaba...ba Damuwa

11/09/2025

Yanayin garkuwar jikin kowane Mutum keda nasaba da haifar da canje canjen da duk za a hadu dasu bayan anfani da Magunguna, abinci da sauran kayan anfani na yau da kullin da ake anfani dasu ajiki.

11/09/2025

Aradu duk wanda yake fama da mugun ciwon kafafu, baya kwankwaso da ciwon jiki ya daina anfani da su fearless

11/09/2025

Daga safiya zuwa yanzu sau nawa kasha ko kikasha ruwa,kuma yakai litre nawa ?

08/09/2025

Idan aka samu akasi ko Matsalar rashin haihuwa ga iyalai matakan da ake anfani dasu sune:-

1- A bangaren uwargida a tabbatar da tana al'adar ta duk wata lfy lau.

2- A tabbatar da bata taba anfani ko bata kan maganin tazara a zahiri ko a boye musamman idan ba a taba haihuwa ba.

3- A fahimci shekarun haihuwar ta basu fada ko zarce 35yrs, 40yrs zuwa 55yrs a duniya ba.

4- A fahimci Uwargida bata da alamun matsalolin infection.

5- A tabbatar da Uwargida bata alamun ciwon sugar.

6- A fahimci mummunar kiba ga Uwargida.

7- A tabbatar da mace na samun kusanci da maigida musamman lokacin da take da damar daukan ciki wato lokacin ovulation. Shine Kwanaki 14 kafin zuwan wata al'adar.

8- A tabbatar da nagarta ta Mahaifa, bututun kwai, na hannayen mahaifa su fallopian tubes inda kwai na Uwargida dana maigida ke cudanya su wuce mahaifa dan tabbatuwar juna biyu.

9- Yananyin dabi'ar kwanciyar aure musamman lokacin da Maigida ke releasing akwai dabi'un da idan Uwargida na aikatasu ba kasafai ciki ke saurin shiga ba.

10- Na karshe daga cikin ababen da zan iya kawo wa shine karfafa gwiwa ga Maigida, samar da wadataccen abinci, cire damuwa, Kwanciyar hankali da nuna soyayya tsakanin iyalai na daga cikin ababen dake kwantar wa matan mu hankali.

Address

Kofar Fada Kankara

234

Telephone

+2348066537033

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Health talk free. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Health talk free.:

  • Want your practice to be the top-listed Clinic?

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram