Ciki Da Raino

Ciki Da Raino Ciki da Raino – Shafin dake ba mata masu ciki da masu raino ilimi, shawarwari, da goyon baya a cikin harshen Hausa.
(2)

04/01/2026

CDR shafi ne da ake bayar da ingantattun shawarwari, ba shafin da ake koyar da zubar da ciki ba. Masu yi mana inbox, ya isa haka.

04/01/2026

Amarenmu na wannan satin, muna yi muku fatan alkhairi, da fatan Allah ya kawo kazantar daki amma ba takin shara ba.

Mikiya 😭😭😭Allah ya jikanki da rahama mahaifiyata - ita ce dalilin da ta sanya ni tunanin kafa irin wannan tafiya domin t...
04/01/2026

Mikiya 😭😭😭

Allah ya jikanki da rahama mahaifiyata - ita ce dalilin da ta sanya ni tunanin kafa irin wannan tafiya domin taimakawa uwaye kamarta. Kuma shafin nan sadaukarwa ce gareta.

Ku sanya min ita cikin addu'o'inku, Allah ya jikan iyayenmu gaba ki daya.

04/01/2026

Ku gayyato mana sabbin amaren nan, su zo nan mu basu bita. Kar a yi tafiya goyon ciki da raino cikin duhu.

Amsa:Fitowar ɗan digonni jini kaɗan bayan jima'i a lokacin da k**e dauke da ciki abu ne da ke iya faruwa saboda sashin b...
04/01/2026

Amsa:
Fitowar ɗan digonni jini kaɗan bayan jima'i a lokacin da k**e dauke da ciki abu ne da ke iya faruwa saboda sashin bakin mahaifa (cervix) yakan zama mai laushi da kuma saurin karɓar abu, wanda ake kira da 'cervical irritation'. Sau da yawa, wannan ba wani abin tsoro ba ne idan anga fitowar ɗigon jini mara yawa, kuma yana iya tsayawa nan da nan ba tare da wani jin ciwo ba.

Amma ki sani yar uwa! Duk da haka, fitowar jini ga mai juna biyu na iya zama alama ce ta kamuwa da infections (kamar vaginitis ko cervicitis) ko kuma wasu matsaloli masu barazana ga lafiya kamar ɓarewar ciki (threatened miscarriage), ko kuma mabiya ta rufe hanyar haihuwa (placenta previa), ko kuma rabuwar mabiya daga bango (placental abruption), musamman idan jinin da yake zubo miki mai yawa ne, ja-fat, tare da jin ciwo, murɗawar ciki, ko jin jiri.

Me ya kamata kiyi?

◾ Idan hakan ta faru dake, a dakatar da yin jima'i nan take, har sai likitanki ya duba lafiyar ki.

◾Ki kula da yanayin zubowar jinin sosai don sanin yadda yake fitowa. Zubar jini da yawa, ya sha banban da fitowar dan digon jini bayan kammala jima'i.

◾Ki garzaya zuwa asibiti nan da nan idan jinin dake zubowa mai yawa ne, ko mai sa ciwo, ko kuma ya zo miki tare da jin jiri ko murɗawar ciki (cramps).

Idan ya amfanar, ku taya mu yada wannan sakon domin wasu suma su amfana. Yada rubututtukanmu ta hanyar sharing a groups, profile da whatsapp na daga cikin gudunmawar da zaku iya bawa wannan shafin.

Mun gode

03/01/2026

Ku sanya ni cikin addu'o'inku!

Kwarai da gaske kuwa! Bama nakuda kadai ba, cinsa yana kara lafiya, jinin jiki da kuzari ga mai juna biyu.◾Yaushe za ki ...
03/01/2026

Kwarai da gaske kuwa! Bama nakuda kadai ba, cinsa yana kara lafiya, jinin jiki da kuzari ga mai juna biyu.

◾Yaushe za ki fara cin dabino?
◾A adadi nawa ya kamata a ci a kullum?
◾Menene amfanin cinsa ga mai tsohon ciki?

Mu hadu a comment, sannan ku taya mu yadawa domin wasu suma su amfana.

👇👇👇👇

03/01/2026

Da yiwuwar duk duk sun haihu fa a December 😳. Shiru nake jinsu kamar an aiki bawa garinsu.

Ga amsa mai wannan tambayar:Lokacin da ya da ce mai jego ta fara shirin tsarin iyali bayan ta haihu ya dogara ne kocokan...
03/01/2026

Ga amsa mai wannan tambayar:

Lokacin da ya da ce mai jego ta fara shirin tsarin iyali bayan ta haihu ya dogara ne kocokan da yanayin lafiyar jikinta, amincewarta, amincewar mai gidanta, da kuma burinta na samun wani ciki a nan gaba.

Domin karanta ci gaba, duba comment section.

03/01/2026

Wasu fa tuntuni sun yi nisa cikin hallarar jin yunwa😄, kina ciki ko kema kin fita da fitarki?

Me ya sa kwanciya a gefen hagu ke da muhimmanci ga mai juna biyu?A yayin da juna biyu ke ƙara girma, kwanciya a gefen ha...
02/01/2026

Me ya sa kwanciya a gefen hagu ke da muhimmanci ga mai juna biyu?

A yayin da juna biyu ke ƙara girma, kwanciya a gefen hagu yana muhimmanci ga uwa da jaririn.

Saboda kwanciya a gefen hagun yana bunƙasa gudanawar jini ga mahaifa da jariri. Domin babbar jijiyar jini da ke dawo da jini daga ƙugu da ƙafafu zuwa zuciya, wato "inferior vena cava" tana nan a ɓangaren dama da ƙashin baya. Don haka, idan mai juna biyu ta kwanta a gefen dama nauyin juna biyun zai danne wannan babbar jijiyar jini tare da taƙaita gudanarwar jini.

Idan kuwa mai juna biyu ta kwanta a gefen hagu nauyin juna biyun ba zai danne babbar jijiyar jinin ba. Wannan zai samar da isasshen gudanawar jini da iskar oksijin zuwa ga mahaifa da jariri.

Bugu da ƙari, kwanciya a gefen hagu yana tallafar aikin ƙoda wanda ke taimakawa rage kumburin hannaye, ƙafafu da idon sawaye.

Har wa yau, kwanciya a gefen hagu na taimakawa rage nauyi a ƙugu da gadon baya wanda hakan ke sauƙaƙa yin numfashi.

Za ki iya sa filo a tsakanin gwiwoyinki yayin kwanciya a gefen hagu domin ƙara jin daɗi.

© Physiotherapy Hausa

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ciki Da Raino posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Ciki Da Raino:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram