05/11/2022
Ya Ubangiji Ka Taimakeni Akan Ambatonka, Da Godemaka, Da Kyautata Ibadarka.🤲
An Kar6o Daga Abu-Hurairah R.A Yace :"Wani Mutum Ya Zo Wajan Ma'aiki S.A.W Sai Yace :" Ya Ma'aikin Allah, Na Hadu Da Wata Kunama Wadda Ta Harbeni A Jiya, Sai Ma'aiki S.A.W Yace Masa :"Ina Ma Za Ka Ringa Fadin Wannan Idan Ka Yammata : A'UZU BI KALIMATILLAHITTAAMMAAT MIN SHARRI MA KHALAQA, da Baza Ta Cutar Da Kai Ba."