17/08/2025
-GA YADDA AKE KARYA SIHIRI KO SAMMU DA IZININ ALLAH.
-Duk Wanda Yake Zargin An yi Masa Asiri Ko Anyi Masa Sammu Ko Anyi Masa Wani Ƙulunboto, Ko Miyagu Sun Saka Shi Agaba, to ga Yadda Zai yi Ya Karya Sihirin da Izinin Allah: Za'a Samu Ƙwai Na Kaza Guda Bakwai, Sai A Dafa Shi Bayan An Dafa Sai A Ɓare Shi Dukka, Sai A Tofa Waɗannan Ayoyin Akan Kowanne Ƙwai Ɗaya Bayan Ɗaya:
-A Ƙwai Na Farko (1) Za'a Tofa Masa Aya ta 81 Cikin Suratu Yunus (Fa-lamma Alqau Qala Musa Ma Ji'itum Bihis Sihir: Innalaha Sa Yubtilu: Innallaha Yuslihu Amalal Mufsidin.)
-A Ƙwai Na Biyu (2) Sai A Tofa Masa Aya ta 118 Cikin Suratul A’raf, (Fa-waqa Al-haqqu Wa Batala Ma Kanu Ya'amalun).
-A Ƙwai Na Uku (3) Sai A Tofa Aya ta 69 Cikin Suratu Daha (Wa Alqi Mafi Yaminika Talqaf Ma Sana'u. Innama Sana'u Kaidu Sahir: Wa La Yuflihus-Sahiru Haisu'ata).
-A Kwai Na Huɗu (4) Sai A Tofa Aya ta 78 Cikin Suratu Ghafir, ("Wa Laqad Arsalna Rusulam Min Qablika Minhum Man Qasasna Alaika Wa Minhum Mallam Naqsus Alaik. Wa Ma Kana Li Rasulin Anyyatiya Bi Aayatin Illa Bi Iznillah: Fa-Iza Ja'a Amrullahi Quziya Bil-haqqi Wa Khasira Hunalikal Mubtilun").
-A Ƙwai Na Biyar (5) Sai A Tofa Aya ta 7 Cikin Suratu Ibrahim (AS) (Wa Iz Ta'azzana Rabbukum La'in Shakartum La'azidanna K*m Wa La In Kafartum Inna Azabi La Shadid).
-A Ƙwai Na Shida (6) Sai A Tofa Aya ta 23, Cikin Suratul Furqan. (Wa Qadimna Ila Ma Amilu Min Amalin Faja'alnahu Haba'am Mansura.
-A Ƙwai Na Bakwai (7) Sai a Tofa Aya ta 98, Suratul Kahfi. (Qala Haza Rahmatun-Min Rabbi: Fa'iza Ja'a Wa'adu Rabbi Ja'alahu Dak-ka; Wa Kana Wa'adu Rabbi Haqqa).
-Sai A Bawa Wanda Aka Yiwa Sammun Ya Cinye Kwai Bakwai ɗin Dukak, Wallahi Nan Take Sammun Zai Karye da izinin Allah.
-Ya Allah Ka Raba mu da Sharrin Masihirta da Sihirinsu Ka Raba mu da Sharrrin Miyagu da Maitarsu Ka Raba mu da Sharrrin Maƙiya da Ƙiyayyarsu Ka Raba mu da Sharrrin Mahassada da Hassadarsu Don Girman Matsayin Manzonka Muhammad (S) da Ahlin Gidansa Tsarkaka (AS)
Mumawa kowa fatan Alkhairi.