M.tar'tilil Qur'anil Kareem mlf

M.tar'tilil Qur'anil Kareem mlf Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from M.tar'tilil Qur'anil Kareem mlf, AIDS Resource Center, Nigerian, Malumfashi.

Gobe in Allah ya kaimu akwai azumin Arfa mu daure muyi shi saboda dunbin falala da ladar dake ciki Allah bamu ikon yiKar...
04/06/2025

Gobe in Allah ya kaimu akwai azumin Arfa mu daure muyi shi saboda dunbin falala da ladar dake ciki Allah bamu ikon yi

Kar a manta da yaiwata kabbarbari a wadannan kwanaki masu albarka.

🙏

In Sha Allah yau Zaku kasance Da wake na (Lamiyya da Haqiyya)daga Bakin Dalibai na Faslu Aliyu Bin Abi DalibLive stream ...
17/05/2025

In Sha Allah yau Zaku kasance Da wake na (Lamiyya da Haqiyya)daga Bakin Dalibai na Faslu Aliyu Bin Abi Dalib
Live stream
By 3:00pm
Facebook channel
Elhussain Graphic da'awah

Dr. Shehu ladan Army malumfashi,Hukumar wannan makaranta Mai suna Asama dakuma Dalibanta sunayima babban malamin mu Mala...
28/04/2025

Dr. Shehu ladan Army
malumfashi,
Hukumar wannan makaranta Mai suna Asama dakuma Dalibanta sunayima babban malamin mu Malam Shehu ladan Army (Hafizahullah) Addu'ar Allah yabashi lafiya Mai dorewa Arayuwar sa

Malam ALLAH yaqara maka lafiya da Nisan kwana, Allah yasa kaffara CE,

TAR'TILIL QUR'ANIL KAREEM MALUMFASHI

Idan kana so ka kiyaye mutuncinka da kimarka, ka yi mu’amala mai kyau da mutane, ka girmama su, ka mutunta su, kuma ka t...
05/03/2025

Idan kana so ka kiyaye mutuncinka da kimarka, ka yi mu’amala mai kyau da mutane, ka girmama su, ka mutunta su, kuma ka tabbatar da cewa halayenka, dabi’unka, da tarbiyyarka sun dace da mu’amalarka a aikace.

Akwai wasu mutane, musamman mata, da suke tunanin cewa idan mutum ba mijinsu ba ne, to babu buƙatar su girmama shi ko yi masa biyayya. Suna ganin kamar ana ba su umarni ne, wanda hakan yana nuna cewa ba sa son a gaya musu gaskiya don su gyara halayensu. Sai dai maganar gaskiya ita ce, biyayya ga miji wajibin aure ne, amma idan mace tana da irin wannan tunanin na kin karɓar gyara da gaskiya, to ko da mijinta ne, ba lallai ba ne ta yi masa biyayya yadda ya kamata. Domin tunanin da ke hana mutum yarda da gyara yana da alaka da girman kai da rashin son gaskiya.

Addininmu na Musulunci yana koyar da kyautata mu’amala da mutane, girmama manya, da yin adalci a cikin dukkan hulɗa da mutane.

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba wanda zai girmama wani domin yana da matsayi sai Allah zai ɗaga matsayinsa.”
(Tirmidhi)

Haka nan, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba ya cikinmu wanda ba ya girmama manya, bai tausaya wa ƙanana, bai kuma girmama malamai ba.”
(Ahmad)

Akwai bambanci tsakanin biyayya ga miji da kuma girmama mutane da s**a girme mu a shekaru ko masu gaya mana gaskiya. Don haka, dole ne mu girmama su idan muna son gaya mana gaskiya da kuma yi mana gyara a inda tunaninmu bai kai ba. Kyakkyawar mu’amala da girmamawa alama ce ta tarbiyya mai kyau, kuma yana daga cikin kyawawan halayen da Musulunci ya koyar.

elhussain Graphic da'awah ✍️

14/11/2024

RAYUWA,JARRABAWA CE

Idan Allah S.W.T Ya Amsa Addu'arka,To Zai Qara Maka Imani.

Idan Kuwa Ya Jinkirta Karbar Addu'arka,To Zai Qara Maka Haquri.

Idan Kuwa Bai Amsa Makaba,To Ya Dauke Maka Wani Nauyi Wanda Shine Mafi Kyau A Qarshen Lamarinka

24/09/2024

“Kada neman Duniya ya mantar da kai neman Lahira, domin Idan har baka rasa lokacin neman duniya ba, Toh aikuwa bai kamata ace ka rasa lokacin neman lahira ba.”

Kina ji na ko? Ki dage kiyi koƙari ki samu lambar ɗaya daga cikin abokan angona karda a tashi taron bikin nan baki fita ...
23/09/2024

Kina ji na ko? Ki dage kiyi koƙari ki samu lambar ɗaya daga cikin abokan angona karda a tashi taron bikin nan baki fita da fitarki ba.

Domin nima a irin hakane na same sa. Maza tabbas tsada suke ba wani ɓoye-boye.

Yan'uwa na mata Addu'a Allah yazaba masu mazaje nagari masu kishin su masu Tausayi

'uwa kada kice Allah yabaki miji ko ma waye !! Wannan kuskurene babba fata kawai kiyi Addu'a Kuma kizabi Miji nagari

lokaci ne yar'uwa kijira shi in sha Allah da Alkhairi zaixo agareki kanwata !!!

'awah

21/09/2024

KA TAUSAYAWA MATARKA.

Kada ya zamto a rayuwar aurenku burinka kawai shi ne ka dinga ƙuntatawa matarka. Ita ɗin amana ce a gareka, ita ɗin ƙanwa ce a gareka, ita ɗin mata ce a gareka, ita ɗin rufin asiri ce a gareka, kuma haƙiƙa ita ɗin abar tausayi ce a gurinka. Itace wacce za ta kula da tarbiyyar ƴa'ƴanka, ta kula da dukiyarka, ta kuma kula da gidanka a lokacin da kake nan ko ba ka nan.

Duk mutumin da za kaga yana ƙuntatawa matarsa, yana zaluntarta ba tare da wani tausayi daga gareshi ba, to haƙiƙa wannan bai cancanci ya zamto miji nagari a gurin kowace mace ba.

Su mata ababen tausayi ne, ababen jin-ƙai ne, ba jarumta bace kace kai kullum baza ka dinga kyautatawa a gareta ba, ko kace kullum za ka dinga ɓata mata rai, haƙiƙa hakan alamun naƙasu ne da tawaya a gareka. Ku tausaya musu, ku ma sai Allah ya tausaya muku.
*DA 'AWATUS SUNNAH*

Daka Samu Mace Me Matsala A Halayenta Wallahi Qara Kasamu Me Matsala A Halitattata Inde Halayanta. Da Addininta, Yanada ...
08/09/2024

Daka Samu Mace Me Matsala A Halayenta Wallahi Qara Kasamu Me Matsala
A Halitattata Inde Halayanta.
Da Addininta, Yanada Kyau

Idan Yanada Kyau 😊 Toh Yafimaka Sauki Akan Kasamu Dirinta Yamaka
Amma Halayanta Akwai Matsala

Sannan Idan Kanada Matarka
Yadda Kagantan nan Kayi Hakuri Da Ita
Kaji Kawai Tamaka Idan Ba Hakaba
Za Kaita Wahala Akan Matan Banza

Ita Waccan Din Dakake Ganinta A Wajan
Idan Ka Kawota Gidan ka, Zakaga Wata Saboda Haka Idan Ka Auri Matarka, Kasama Kanka Tamaka, Shine Kwanciyar Hankalinka.

Misali Abubuwan Damuke Rayuwa
Dasu Bakuna Jin Yamaku ba,
Toh Haka Kuyi Hakuri Da Matayan ku
Kusa Aranku Bakuda Kamar su,

Allah Kabamu Mataye Nagari
Masu Kyakykyawan Hali
Da Kuma Addini, Amiin ya Allah

06/09/2024

DARAN JUMA'A DA RANAR JUMA'A

Daga Anas ɗan Malik(رضي الله عنه) yace:

"Lallai Manzon Allah ﷺ yace: ku yawaita salati a gareni ranar juma'a da daren juma'a, kuma duk wanda yayi min salati guda ɗaya Allah zai masa sati goma".

صحيح الجامع للألباني رحمه الله

Address

Nigerian
Malumfashi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when M.tar'tilil Qur'anil Kareem mlf posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram