20/04/2025
Jiya Ake bani labarin wata Mata.
Tayiwa kishiyar ta irin wannnan mummunan tsafin. Matar da aka yiwa tsafin ta dade kwance tana jinya ba'asan ciwon ta ba, ansha wahala har angaji anbar wa Allah.
Kwatsam sai ita Matar da tayi irin wannan bakin tsafin ta fadi ta Mutu.
Few days after mutuwar azzalumar kishiyar, anzo ana kwashe kayan ta ana kokarin harhada kayan ta very possible, domin fara shirin raba gado.
Sai aka gan exactly, irin wannan ( Yar tsana din a dunkule da layoyi da zaruruwa dama wasu abubuwan da ba'a ko san menene ba ) sai kuwa aka kwance su duka aka Kona, wallahi cikin ikon Allah sai ga wannan boyar Allah din da aka yiwa tsafi ta mike tsaf kai tsaye tamkar bata taba wani rashin lafiya ba.
Shi kuma Mijin ya yita tsinewa waccan albarka, ya yita yimata Allah ya isa.
Kuma a dai dai lokacin da Allah ya kara mishi arziki da matsayi a duniya.
Ita dai wannan boyar nan din, karshen wahalar ta yazo. Yanzu haka da ita da mijin, da ita Matar suna nan zaune suna cin sabuwar rayuwar su.
Ita kuma waccan mushurukar ta shiga ( Musiba ta har abada ) domin, ta Mutu a mushuruka.
Inada tambaya, shin don Allah miye ribar data ci a yanzu🤔
Ta mutu mushuruka, kuma ga kishiyar tata yanzu ta samu lafiya kuma ta shiga sabuwar rayuwa ita da mijin.
Don Allah, muji muji tsoron Allah.
Shirka musiba ce kuma wallahi batada sakamako mai kyau.
Adaina shagala da yin Azkaar don Allah ✍️