Kiwon Lafiya A Saukake

  • Home
  • Kiwon Lafiya A Saukake

Kiwon Lafiya A Saukake DM for Adverts and Business Promotion
or contact +234 907 208 5891 on WhatsApp Domin Tallata Hajarku

28/07/2025

Wai mai yasa matan Arewa dayawa masu juna biyu basa son zuwa awun ciki (Antenatal)?

19/07/2025

Kada masoya su jira sai daf da aure kafin su je suyi gwaje-gwaje. Yana da kyau suyi gwaji musamman na genotype da zarar sun aminta da juna tun farko-farkon soyayyar

19/07/2025

Ku rubuta tambayoyinku a sashen comments. Zamu amsa wasu daga ciki in sha Allah

19/07/2025

Daga wani gari kuke bin wannan shafin?

ME ZANYI TEƁA TA TA DAINA GIRMA?AMSAki rage cin abinci nau'in carbohydrates kakar su shinkafa, doya. Ki ƙara protein a m...
19/07/2025

ME ZANYI TEƁA TA TA DAINA GIRMA?

AMSA
ki rage cin abinci nau'in carbohydrates kakar su shinkafa, doya. Ki ƙara protein a madadin sa (kamar su ƙoyi, kifi da Nama), ki ƙara yawan ganyayyaki da ya'yan itatuwa da k**e ci, ki yawaita motsa jiki/yin atisaye. Akwai na musamman da akeyi saboda teɓa
Ki daina cin abinci daf da lokacin da zaki kwanta

Yin hakan zai taimaka sosai amma ba cikin ƙanƙanin lokaci ba

Sanarwa Mai Muhimmanci Ga Masu Yìn LayyaDaga Yahaya Surajo SobaMasanin Lafiyar Dabbobi+234 813 275 3439Assalamu alaikumM...
05/06/2025

Sanarwa Mai Muhimmanci Ga Masu Yìn Layya

Daga Yahaya Surajo Soba
Masanin Lafiyar Dabbobi
+234 813 275 3439

Assalamu alaikum

Muna masu sanar da mutane akan su kula tare da saka ido sosai akan naman da za su yanka yau ko gobe idan Allah ya kai mu.

Akwai cututtuka masu tarin yawa da mutane ke dauka lokacin amfani da nama na dabbobi ba tare da sun sani ba.

Muna kira da mutane da su natsu sosai wajen duba naman da za su kai wa iyalan su domin hidimar Sallah.

Da farko muna bada shawara akan kada mutum ya yarda ya yanka dukkan dabbar da aka lura ba ta da lafiya domin yanka dabba mara lafiya yana haifar mana da cututtuka masu tarin yawa kamar (Micobial resistance) TB, da sauransu.

Bayan an yanka dabba a lura da canjin kala da ake samu na nama indai an ga nama ya canza to yana da kyau a nemi (Vet. Technician) mafi kusa domin duba ingancin naman don gujewa daukar cuta mai yaɗuwa.

Sannan a duba kayan ciki wato (Vicerral organ) kamar su hanji, tumbi da sauran su domin' akwai 'internal parasite' dake rayuwa a ciki wato tsutsan ciki wa inda indai mutum ya ci to dole ne sai sun ci gaba da rayuwa a cikin mutum kuma suna da illa sosai.

Sannan a duba hanta da huHu da zuciyar dabba domin akwai cututtuka kamar su Fasciola, Hepatitis, traumatic pericarditis, CBPP/CCPP, TB da dai sauran su wadanda idan dai an ci nama da su to akwai matsala sosai, sannan kuma su cututtuka ne da wuta bata iya kashe su.

Sannan a gujewa yi wa dabbar da za a yanka allura ko ba su magani ko wani iri ne sabida hakan yana da illa ga lafiyar Ɗan adam.

Idan an samu irin wannan canjin ko kuna so mu duba muku lafiyar naman ku zaku iya nemanmu.

Vet._Yahaya Surajo Soba
Meat inspector officer
Animals health technician

03/06/2025

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh

DAN ALLAH TSAYA KA KARANTA.Daga: Dr. Abdurrahman DambazauRanar Litinin 17/2/25, Mun shiga ɗakin da ake kwantar da marasa...
23/02/2025

DAN ALLAH TSAYA KA KARANTA.
Daga: Dr. Abdurrahman Dambazau
Ranar Litinin 17/2/25, Mun shiga ɗakin da ake kwantar da marasa lafiya na ɓangaren tiyata (Surgery). tare da likitan da ke hannun dama na a wannan hoto.
Wannan likita sunan sa doctor bashir Aliyu, likita ne na tiyata a babban asibitin koyarwa da ke azare(FMC AZARE), asibitin da nake koyan aiki a matsayi na, na ɗan ƙaramin likita.
Bayan mun shiga sai ya ga wata yarinya ƙarama wacce ita ma tana buƙatar tiyata(surgery) amma kuma bata cikin list na wannan rana. Abun da muke nufi da list shine: duk ranar da za ai tiyata ana ware iya mutanen da za ayi ma a wannan rana.
Ma'ana yarinyan bata cikin waɗan aka tsara zai ma tiyata a wannan rana.
Bayan ya ganta sai ya kira ni, yace dambazau ka shirya mun yarinyar nan anjima bayan na gama tiyato ci biyu da nake dasu zaka tayani na mata. sai nace mai to, Naje nai duk shirye shiryen da ake ma mara lafiya idan za amai tiyata.
9:30 na safe dr bashir ya shiga ɗakin tiyata ya fara ayyukan sa, wajen karfe 12 na rana, ya gama tiyatan farko, zuwa 3 na rana, ya gama tiyata na biyu, wanda alokaci ko a ido ka kalle shi kasan ya gaji, amma duk da haka wajen uku da rabi yace dambazau a ɗakko yarinyar nan, a kawo ta ɗakin tiyata. Sai naje Nama nurses magana aka kawo ta.
Akwai kayayyaki da akace iyayen yarinyar su siyo, za ai amfani da su a lokacin da ake tiyatan, wanda sakamakon yana yi na rayuwa basu da halin da zasu iya siyo wa. dr bashir ya ciro kuɗi a aljihun shi yace dambazau gashi ka basu suje su siyo, na basu s**a je s**a siyo, bayan sun siyo muka fara tiyata, wanda bamu gama ba sai wajen shida na yamma.
Tambayar anan shine;
Shin da gaske ne likitoci basu da kirki??
Ko wani ɓangare na rayuwa ba ka rasa ɓatagari ko mara sa kirki, amma musani ɓangaren likitanci ɓata garin ƙalilan ne in ka haɗa su da sauran ɓangaren rayuwa irin su shari'a, ƴan sanda, banki, jarida da sauran su.
A kwana kin nan akwai matar da tai iƙirarin likitoci a asibitin malam aminu kano sun cire mata mahaifa, wanda duk wanda ya shiga ɓangaren comment zai ga yadda mutane ke faɗar abubuwa mara sa daɗi akan likitoci. muƙaddara labarin gaskiya ne, atunani na hakan bazai sa likito ci su zama ɓata gari ko masa kirki ba.
Akwai likitoci da yawa wanda suke sadaukar da lokacin su, dukiyar su, da kuma jindaɗin su, don suga sun taimaka ma mara lafiyan su(Patient). hasali ma har da waɗan da s**a rasa rayuwar akan hanyar taimakon mara lafiya irin su Dr muhd musa habeeb, (consultant anaesthesia AKTH) Allah ya jiƙan sa da gafara.
Aikin likitanci aiki ne da ke tattare abubuwa da dama wanda idan mutum ba acikin sa yake ba bazai taɓa gane su ba.
Dan Allah adunga ma likitoci uzuru.
Nagode

Dr Abdurrahman Dambazau

Daga shafin Dr. Dambazau TV

TAMBAYA DAGA MEMBA"Dan Allah meke k**k ciwon hanta. Wani mataki za abi dun rage ciwun Kuma Dan Allah wani kalan abinci z...
19/02/2025

TAMBAYA DAGA MEMBA

"Dan Allah meke k**k ciwon hanta. Wani mataki za abi dun rage ciwun Kuma Dan Allah wani kalan abinci za a ringa ci Kuma ba matsala dun kana rayuwa tare da Wanda bedashi Ina jiran amsa nagode"

16/02/2025

Ina masu shan maganin zazzabin cizon sauro kamar su Artemether? Ku matso kusa. Ga shawarwari

16/02/2025

Muna ƙirga kwanaki ƙalilan kafin zuwan watan Ramadan, shin wani shiri kukayi domin kula da lafiyar ku lokacin azumi?

16/02/2025

MENENE MAGANIN RAGE TUMBI?

Tambaya daga memba

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kiwon Lafiya A Saukake posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Kiwon Lafiya A Saukake:

  • Want your practice to be the top-listed Clinic?

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram