Adamawa State Primary Health Care Development Authority,Fufore LG.

  • Home
  • Nigeria
  • Yola
  • Adamawa State Primary Health Care Development Authority,Fufore LG.

Adamawa State Primary Health Care Development Authority,Fufore LG. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Adamawa State Primary Health Care Development Authority,Fufore LG., Yola.

04/09/2020

Matar Shehu ta zo wajensa cikin dare hankalinta a tashe, tana cewa da shi: “Na rasa abin da ya sami yaron nan; babu abin da yake yi ban da kuka a koda yaushe, kuma na yi masa irin duk abin da zan iya don ya yi bacci, amma abu ya gagara! ka yi masa wani dan kokari mana, ko ya samu ya yi bacci, ko dai ka yi masa abin da ka ga ya fi dacewa, ni duk hannayena sun gaji da daukar sa da jijjiga shi.”
Sai ya ce da ita: “Saboda me kika rude haka? Dauki wannan littafin ki buda shi, ki ajiye a gabansa.”
Sai matar ta fusata tana fada, tana cewa: “Yanzu wasa za ka yi mini game da wannan lamari? Haka kuma za ka yi mini, bayan ka auro ni tun da kuruciyata, ka gama biyan bukatarka da ni, ka bar ni cikin yunwa da tsumma, alhali ina ta faman yi maka hidima ba-dare-ba-rana, kuma wannan yaro danka ne, ba agola ba.
Saboda me za ka rika wasa da hankalina a kowane lokaci?”
Sai Shehu ya amsa mata da cewa: “Haba Hajiya, ai kuwa ina yin bakin kokarina, wajen kyautata rayuwarki, saboda me za ki rika yi mini irin wannan magana mai zafi, kina tayar mini da hankali?”
Sai matar ta rage karfin muryarta, sannan a fusace ta cigaba da cewa: “To wannan littafin na menene, kuma wace fa'ida za'a samu a cikinsa?”
Sai ya ce: “Kwantar da hankalinki, wannan littafin "KADURI" ke nan, (wani littafi ne maras ma'ana da ya kunshi bayanai na rashin kan gado) wanda duk lokacin da na karanta shi ga almajirai a masallaci, sai bacci ya kwashe su, wasu ma har ka ji suna minshari.
To idan kuwa har zai iya sanya bacci ya kwashe magidanta masu gemu, kamar wadanda aka yi wa sihiri saboda tasirinsa, me zai hana ya sanya jariri ya yi bacci kamar ya shaki banju?”

Address

Yola

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Adamawa State Primary Health Care Development Authority,Fufore LG. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram