22/10/2024
Muhimmancin Bacci Ga Lafiyar Ƙwaƙwalwa Da Tunani
Bacci na da tasiri ga lafiyar gangan jiki, tunani, koyo, ƙirƙira, kaifin hadda, kaifin basira da kuma walwala.
Masana na ba da shawarar samun isashshen bacci da ya kai awa 7 — 9 kullum.
Haka nan, sau da yawa, bincike ya nuna tasirin motsa jiki ko atisaye wajen bunƙasa samun isashshe kuma ingantaccen bacci. Bugu da ƙari, motsa jiki ko atisaye na da tasirin magance ciwon damuwa da ciwon gaɓɓai waɗanda ke gaba-gaba wajen hana samun ingantaccen bacci.
© OccupationalTherapy Hausa
Send a message to learn more