CUPS Mata Da Marayu

CUPS Mata Da Marayu Wannan shafin mun kirkiro shi ne domin tallafawa mata, da zawarawa, da marayunmu. Allah Ubangiji ka daafa mana. Amin Ya Rabbi.

MURNAR CIKAR NAJERIYA SHEKARU 65 DA SAMUN 'YANCIN KAI Matan CUPS na addu'a ga Kasa Najeriya don samun cigaba da wuce mat...
01/10/2025

MURNAR CIKAR NAJERIYA SHEKARU 65 DA SAMUN 'YANCIN KAI

Matan CUPS na addu'a ga Kasa Najeriya don samun cigaba da wuce matsalolin mu.

Allah ya daukaka Kasar mu Najeriya Amin.

Matan CUPS...

IYAYEN Talakkawa NE.

Jama'a barkanmu da warhaka!Kowa da sana'ar da ta karbeshi. Mu kuma sana'armu kenan, wato kera motocin alatu. Toh amma ba...
14/09/2025

Jama'a barkanmu da warhaka!
Kowa da sana'ar da ta karbeshi. Mu kuma sana'armu kenan, wato kera motocin alatu. Toh amma ba nan ne gizo take saka ba. Wannan harka ne na ilimin zamani mai zurfi. Kusan kashi 80% na injiniyoyi wadanda s**a kera wannan motan da kuke gani, duk matasa ne, daga sassa daban-daban na duniya.

Matasanmu na Najeriya, musamman na Arewa, ina yi muku nasiha, addu'a da fatan alheri. Allah Ya yi muku albarka. Don Allah ku dage ku nemi ilimin zamani da na addini. Tabbas, ba zaku tabe ba. Insha Allahu, zaku ga haske a rayuwarku.

Nan bada jimawa ba zamu sake bude dandalin CUPS Computer and ICT training domin daukan sabbin dalibai. Muna son mu fara horaswa da dalibai 50,000. Ku tabbar da cewa kunyi ragista. A yanzu haka muna da dalibai kimanin 15,000 wadanda s**ayi ragista. Idan Allah Ya yarda, muna da kudurin horarsa da yan Najeriya miliyan daya. Ya Ubangiji Allah Ka daatanmana. Amin Ya Rabbi.

Jama'a na barku lafiya.

Dr. Idris Ahmed.
Shugaban CUPS.
14/9/2025.

13/09/2025

Jama'a barkanmu da warhaka. Zuwa yanzu kwararru 90 sun rattaba hannu. Ku ci gaba da yi mana addu'a. Allah Ka bamu gagarumar nasara

Free CUPS Computer and ICT Training - Latest UpdateUPDATE IN ENGLISH:Fellow compatriots, I write to update you with our ...
08/09/2025

Free CUPS Computer and ICT Training - Latest Update

UPDATE IN ENGLISH:

Fellow compatriots, I write to update you with our progress as follows:

1. We are now fully engaged with the new 160 Computer and ICT experts that we hope to recruit to teach and mentor you Computer and ICT. We have sent them emails and most of them have responded favourably. By Sunday, 14th September 2025, all the experts interested in working with us would have signed a legally binding MoU contract with the CUPS Organisation. The MoU details the job specification, duration of the training, monthly salary, how payment is made and finally rules of disengagement, should the need arise (We hope and pray this doesn't happen).

2. We are also fully engaged with the CUPS syllabus translators into Hausa language. The latest comprehensive syllabus is 41 pages. It is being translated into Hausa language. We expect to get at least 5 fully completed accurate translations by Sunday, 14th September 2025. The best 3 translations will be shared free in all the CUPS Tutor groups.

3. Following a successful engagement with the new Computer and ICT experts, 18 of them will be immediately recruited to expand the classes to 20. Network stability is a significant deciding factor. Starting with 20 classes means we will have a cohort of 50,000 students (there are 2,500 students in each class). However, if the network proves stable, we may decide to increase the number of classes and recruit more tutors.

4. Just before we commence training, all students will be rearranged into 10 classes where the language of instruction will be purely English, and the other 10 classes will be bi-lingual (English and Hausa). It is entirely up to a student to chose which language class to belong to. We created this arrangement to overcome the language issues/challenges encountered by the 3MTT program, which led it its failure in some Northern states.

Thank God, we have made significant progress over the last 3 weeks. This explains my absence from Facebook. Please, keep praying for the success of this program. Fellow compatriots, I leave you in peace.

Dr. Idris Ahmed.
President CUPS.
07/09/2025.


BAYANI DA HAUSA:

Jama'a Barkanmu da warhaka. Ga sabon karin bayani kamar haka:

1. A yanzu haka, muna cikin cikakken hulɗa tare da sabbin ƙwararrun kwamfuta da na ICT, su 160, waɗanda muke fatan za mu ɗauke su don su koya muku ilimin kwamfuta da ICT. Mun aika musu da imel kuma yawancinsu sun ba da amsa mai kyau. Nan da ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025, duk ƙwararrun masu son aiki da CUPS, za su sanya hannu kan kwangilar yarjejeniya (MoU) tare da Ƙungiyar CUPS. Yarjejeniyar MoU ta ƙunshi cikakkun bayanai game da yanayin aikin, tsawon lokacin karantarwan, albashi a kowane wata, yadda zamu biyasu albashi, da kuma ƙa'idodin rabuwa, idan har an samu akasi (Allah Ubangiji Ya kiyaye. Amin).

2. Hakanan kua muna cikin cikakken hulɗa tare da masu fassara manhajar karatun kwanfuta. Muna sa ran samun aƙalla cikakkun fassarori guda 5 daidai nan da ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025. Zamu raba mafi kyawun fassarorin kyauta a cikin duk azuzuwa 20 na kwamfuta.

3. Bayan nasarar hulɗa tare da sababbin ƙwararrun kwamfuta da ICT, zamu dauki 18 daga cikinsu nan take don faɗaɗa azuzuwan zuwa 20. Zamu ƙara ɗaukar wasu sabbin malamai yayin da muke samun ci gaba. Fara horaswa da azuzuwa 20 yana nufin zamu fara da ɗalibai 50,000 (akwai dalibai 2,500 a kowani aji). Duk da haka, idan hanyar sadarwa ta tabbata (Network), toh muna iya yanke shawarar ƙara azuzuwan da ɗaukar ƙarin malamai.

4. Kafin mu fara horarswa, za a sake tsara duk ɗalibai zuwa azuzuwa 10 inda harshen koyarwa zai zama Turanci kawai, sauran azuzuwa 10 kuma za su kasance masu amfani da harsuna biyu (Turanci da Hausa). Ya rage wa ɗalibi ya zaɓi ko wane irin ajin harshe zai shiga. Mun ƙirƙiri wannan tsari ne don magance matsalolin harshe da shirin 3MTT ya fuskanta, wanda ya haifar da gazawar program din a wasu jihohin Arewa.

Tabbas, munyi gagarumar nasara a sati uku da s**a gabata. Wannan shine dalilin da yasa baku ganni a wannan dandalin ba. Toh Allah Ubangiji Ya datanmana. Amin Ya Rabbi. Jama'a kuci gaba da yi mana addu'an samun nasara akan wannan tafiya. Jama'a na barku lafiya.

Dr. Idris Ahmed.
President CUPS.
08/09/2025.

Download CUPS Comprehensive Constitution!Fellow compatriots, we are delighted to avail you the CUPS comprehensive consti...
20/07/2025

Download CUPS Comprehensive Constitution!
Fellow compatriots, we are delighted to avail you the CUPS comprehensive constitution. This document is thoroughly thought out. It covers the CUPS mission, vision, membership rules and regulations, and every aspect of planned areas of CUPS operations.

The fact that we have made the conscious decision to publicly share this important document means that we are happy for our people to adopt it for their specific needs. All we ask for is for you to acknowledge at the top or bottom of your version that you have adopted it from CUPS original constitution.

As the CUPS organisation keeps evolving based on progress and world dynamics, we will keep updating the CUPS constitution and sharing it with the you.

Find attached at the comments section is link to version 1.2 of the CUPS constitution for your download and review.

Have a blessed Sunday, folks!

Dr. Idris Ahmed
CUPS President
20/7/2025.

19/07/2025

Karin Bayani Akan ICT Training Email ✉️

Jama'a barkanmu da warhaka. Kamar yadda yawancinku kuka sani, mun tara emails 📨 fiyes da 14,000. Toh amma har yanzu wasu sunce basu samu ba. Ga dabara nan da zata taimakeku.

Kamfanin Tecomex Forensics Ltd itace ta sayi email marketing din a madadin CUPS. Itace take da alhakin tura emails din. Saboda haka idan kun lalubi "Promotion" folder 📂 baku ga email ba, toh kuyi search na sunan"Tecomex Forensics Ltd", insha'Allah zaku sami wannan email din.

Toh Jama'a na barku lafiya. Allah Ubangiji Ya bamu gagarumar nasara akan wannan tafiyan ceton Arewa da al'ummanta. Amin Ya Rabbi.

Dr Idris Ahmed.
Shugaban CUPS.
19/7/2025.

Address

Coventry

Telephone

+447438798343

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when CUPS Mata Da Marayu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to CUPS Mata Da Marayu:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram