24/12/2025
Ko Meyasa Idan Mutum Yayi Qiba Mutane Ke Tunanin Kamar Wata Alamace Ta Jindadi ko Ni'ima?
Mutane da dama idan sunga mutum ya canza yayi qiba sai su fara tunanin wani nau'in jindadi ne, ko ni'ima tasa yayi wannan qibar duk da qiba natare da nata qalubalen a lafiyar dan Adam wanda mai ita zai iya fuskanta.
Tabbas akwai qiba ta azaliya (biological: genetic, hormonal changes), akwai qiba wadda mutum zai iyayi sanadiyar canjin muhalli, cin abinci dayawa fiye qima, cin sarrafaffen abinci (processed foods), cin abinci mai suga sosai, rashin motsa jiki, hutu dayawa batareda yin wani aiki ba.
Akwai kuma wanda zai samu qibar sa tun yana jinjiri saboda shayar dashi nono fiye da qima (overfeeding).
Haka kuma akwai qiba wadda wasu rashin lafiyoyi ke iya kawowa misali, polycystic ovarian syndrome (PCOS), Cushing's syndrome dss.
Bayan wadannan nau'ukan qiba akwai kuma qiba wadda ita bata azaliya ba, bata sauyin muhalli ba, haka kuma bata rashin lafiya ko kuma daya daga cikin abubuwanda na missafa a sama.
Ko wacce irin qiba wannan?
Ita ce qiba yar kanti.
Eh, yar kanti.
Wacece qiba yar kanti?
Qiba yar kanti itace qibar da mutum zaiyi wadda batada alaqa da daya daga cikin abubuwanda na lissafa a sama.
Misali masu amfani da magunguna iri-iri domin suyi qiba.
Haqiqa akwai mutane da dama qibar su irin wannan ce __ ta shan magunguna, ko meye suke canza halittar su zuwa wannan? Oho.
Wataqil ko maganganu mutane ne na cewa idan mutum yayi qiba shine nau'in jindadi, walwala ko ni'ima. Wannan amsar dai banda ita.
Wannan dabi'ar tana qoqarin zama ruwan dare acikin al'umma. Haka kawai can idan aka fito kasan mutum gashinan dai alhamdulillah amma kawai bayan kwana biyu kaganshi kamar wani buhu.š¤
Wannan dabi'ar tafara yawa musamman acikin yan mata __ dayawa daga cikin su ba qibar gaskiya bace.
Abun yanzu bama akan yan matan kawai ya tsaya ba har maza su sun fara.
Nayi ta samun tambayoyi dayawa daga mutane dadama akan wai sunason suyi qiba in gayamusu maganin da zasu sha.š¤
Toh ki/kasan idan kana cikin su ilar da wannan qibar zata kawoma tafi duk wani buri daka/kike qoqarin cimma da wannan qibar. Toh Allah na tuba wani buri kuma?
Masu qibar azaliyar ma s**an iya fuskantar matsalolin rashin lafiyar dadama kamar su hawan jini (hypertension), ciwon sugar (diabetes), ciwon daji (cancer), minshari a lokacin bacci (sleep apnea), matsalolin zuciya, ciwon ga'bo'bi, matsalolin ciwon hanta dss.
Sai a kiyaye.
Shawarata anan shine gama su qiba ta azaliya yanada kyau su kula sosai da irin nau'in abincin da suke ci, rage cin abinci mai suga sosai, rage shan lemunan kwalba (soft drinks), samun isasshen bacci, motsa jiki, rage cin abinci mai qice.
Haka kuma ku masu qiba yar kanti damasu niyar yi, ina baku shawarar daku daina, illar da wannan zaiyiwa lafiyar ku tanada yawa. Akwai cututuka dayawan gaske da wannan zata iya haifarwa.
Nr. Abdullahi Musa.