29/09/2025
DOMIN KARE KANKA DAGA CIWON KUNNE....
________________________________
Da farko dai yana da kyau ka fahimci dalilin faruwar ciwon kunne kafin mu Kai ga yadda za kayi domin kare kanka.
Jerin dalilai masu zuwa, su ke sa ciwon kunne da watakil kafin yanzu ba ka sani ba.
1. Infection – Ana iya samun ciwon kunne idan ƙwayoyin cuta ko fungi s**a shiga cikin kunnen, musamman idan ruwa ya makale lokacin wanka ko wani abu.
2. Earwax mai yawa – Yawaitar man kunne sosai zai iya matse gangar kunne (eardrum) ya kuma haifar da ciwo.
3. Matsalar hanci da makogwaro – Kasancewar hanyoyin su a hade suke ta ciki, mura, ko ciwon tonsils suna iya aika ciwon zuwa kunne.
4. Rauni – Sannan rauni na iya samun kunne sakamakon amfani da cotton bud ko tsinke
________________________________
TO, YAYA ZAKA KARE KANKA?
1. N farko ka guji saka cotton bud cikin kunne da nufin fitar da datti
2. Bayan iyo/wanka, ka fitar ruwan da ya shige kunnen ka da tawul mai laushi.
3. Warkar da matsalolin hanci da makogwaro kafin su shafi kunne.
4. Ziyartar likita idan ciwon yayi tsanani domin a duba ki infection ne.
________________________________
A KULA
1. Kada ka yi amfani da ruwa mai zafi ko sinadarin da ba ka tabbatar da ingancin sa ba
2. Likita na iya baka maganin digawa a kunne ko maganin sha Don samun sauki
3. Idan kuma infection ne mai tsanani, ana iya buƙatar antibiotics - Amma likita ne kadai zai iya yanke haka.
Ciwon kunne dai idan aka yi sakaci da shi, ya kan iya kai ka ga rasa ji har abada!
28/09/2025