10/06/2020
MANUNIYA AKAN COVID-19 (1)
Daga Sheikh Aliyu Talex Zaria
Alhamdu lil-Lah!
Ya Allah! Kai ne abin godiya ba wani bawa ba. Kai Ka halicce mu, Kai Ka raya mu, Kai Ka umarce mu da mu kadaita Ka da bauta.
Ka bude Mana masallatanmu na Juma'a domin daukaka TauhidinKa da IbadarKa, bayan kwace Mana damar hakan da wasu bayinKa s**a yi, har na tsawon makwanni gona sha daya.
Ya Allah! Muna kara jaddada godiya a gare Ka, Kai kadai, bisa wannan ni'ima ta bude Mana wuraren Ibadarmu, domin mu cigaba da yada AddininKa, a bisa tafarkin Manzon tsira Annabi Muhammad saw.
Akida ce ta Ahlus-Sunna wal Jama'a, cewa Allah Shikadai ne:
- Mahaliccin kowa da komai.
- Mai mulkin kowa da komai.
- Mai gudanar da al'amuran kowa da komai.
- Mai cikakken iko a kan kowa da komai.
- Mai yin yanda Ya so a kodayaushe, a inda Ya so, K**ar yanda Ya so, a kan wanda Ya so.
- Rayuwar bayinSa da lafiyarSu ko rashnita, da mutuwarsu da tashinsu, da hisabinsu duk suna hannun Sa.
- Abinda Allah Ya ga dama shi zai tabbata, ba abinda wani bawa yake so ba.
- Cutar Corona, K**ar kowace cuta ko rashin lafiya, baiwa ce daga cikin bayin Allah, halitta ta aka yi, ba ita tai kanta ba. Tana karkashin mulkin Allah da gudanarwarSa, sai yanda Yai da ita. Bata isa ta K**a kowa ko Ka kashe wani ba, sai da izinin Allah. Wannan ita ce AQIDA ta tamanun da takwas(88) daga cikin Aqudun Ahlus-Sunna, daga littafinالعقيدةالطحاوية.
Ga nassinta kamar haka:
وكل شيء يجري بمشيئة الله تعالى وعلمه وقضاءه وقدره، غلبت مشيئته المشيئات كلها، وغلب قضاءه الحيل كلها، يفعل ما يشاء وهو غير ظالم ابدا، تقدس عن كل سوء وحين، وتنزه عن كل عيب وشين. (ولا يسأل عما يفعل وهم يسألون)، الانبياء:٢٣.
Ma'ana:
Kowane abu yana gudana ne da ganin-damar Allah da iliminSa da hukuntawar Sa da kaddarawar Sa.
Ganin-damar Allah ta rinjayi dukkan ganin-dama. HukuntawarSa ta fi karfi dukkan dabaru. (Allah) Yana yin abinda Yaga dama ba tare da zalinci ba har abada. Ya tsarkaka daga kowane mugun Abu da mara kyau. Ya tsaftata daga kowane aibu da cikas.
Sai malaminka ya kafa hujja da wata Aya ta Alqur'ani mai girma, cikin suratul Anbiya (23):
(BA A TAMBAYAR ALLAH GAME DA ABINDA YAKE AIKATAWA, SU BAYI NE ZA A TAMBAYA).
A karshen, mu bama karyata Corona ko HIV/ AIDS ko Ebola ko Lassa ko, ko, ko... Amma Muna cewa wallah tallahi ba su isa ba, Allah ne jadai Ya Isa.