Damace Kawai Global Network

Damace Kawai Global Network Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Damace Kawai Global Network, Medical and health, Gatafa town, Auyo.

Damace Kawai is aimed at, working together to actualise our dreams of supporting our able mentor Dr. Nuruddeen Muhammad’s ambition of getting our dear state Jigawa working again.

Jigawa Northeast is in a safe hand 2023.Vote Dr Nuruddeen Muhammad for great representation at the red chamber.
24/12/2022

Jigawa Northeast is in a safe hand 2023.

Vote Dr Nuruddeen Muhammad for great representation at the red chamber.

17/01/2021

A MARI MATACCE DON MAI RAI YAJI TSORO....!

By Mansoor Ismail Gatafa Ælgatafawy ✍️

Ya ku yan uwana matasa! A yayin da duniya ke fama da fitintinu masu yawa, jere da juna, take fama da munanan bala’o’i marasa iyaka, wadanda suke girgiza zukata s**a shallake tunani da hankulan jama’a, sai ga zamani ya zo da wani sabon abu da ke bata tunani ke raunana tunanin zababbu da gama-garin jama’a, yana bijiro da al’umma zuwa ga rarrabuwa da rugujewa, yana kekketawa da yayyaga hadin kan jama’ar Musulmi da zaman lafiyarta.

Al’umma ba ta ji zafi ba, face saboda aukuwarsa, jama’a da daidaikun mutane ba su gushe ba, face wannan abu yana kekketa su yana karya su, yana jefa su cikin fushin zubar da jini. Wannan abu Allah ya tsare mu ba komai bane face cin mutuncin mutane da bata martabarsu da tuhumar barrantattu daga cikinsu da niyyar cin zarafinsu. Hakika wannan abin ki ne, kuma kaiton yin haka, Allah wadaran wannan abin zargi da wawaye suke riko da shi, hali ne da ke kaiwa ga watsa kazafi da kiren-karya da kalamai masu jawo fasadi a tsakanin Musulmi, ya kawo juya baya ga juna da kaurace musu. Hakan na lalata zamantakewa ya jawo kirkirar karya a kan mutum ba kunya ba tsoro, ba don komai ba, sai don a zubar da mutuncin wani haka kawai, kuma a haifar da cutarwa marar iyaka da za ta daidaita zaman jama’a ta girgiza tushen zaman al’umma.

Ya ku yan uwa matasa! bin aibobin mutane da al’amurorinsu don gano nakasunsu da gazawarsu da kazantarsu, mu sani mummunar hanya ce mai halakarwa. dabi’a ce ta mutanen da ake zargi kuma kazanta ce, kuma ta saba wa shari’ar Allah Madaukaki da shiriyar Manzonsa (SAW) wanda yake cewa:

“Albarka ta tabbata ga wanda ya shagaltu da laifuffukansa daga laifuffukan mutane.”

Yaku yan uwana matasa musamman yaran yan siyasa, shin ko kun taba wannan tunani?

Shin masu gidan ku suna ja muku kunne akan abinda kuke na aibantawa?

To wallahi duk maigidan da kaji baya tsawatar maka ka gujeshi, macucine!

Allah ya hanemu fadawa cikin jerin mutane masu wannan mummunar dabi'a ta zargi. Allah ya kara shiryar damu tare da yi mana jagora a dukkanin al'amuran mu na rayuwa, yasa mu gama da duniya lafiya. Amin.

Bissalam.

Mansoor Isma'il Gatafa
Media Mobilizer Auyo L.G.A
HEYOUD
12 - 01 - 2021.

14/12/2020

Shafin kungiyar izala ta karamar hukumar Hadejia, don yada da'awah, karantarwa sanarwa sada zumunci da yayata ayyukan wannan kungiya.

01/04/2020

Korona Baros; Tsumagiyar Kan Hanya!
Dr Nuruddeen Muhammad
MBBS, MWACP, FMCPsych

Bayan na kammala duba marasa lafiya a wani yammaci, ban san lokacin da na tsinci kai na cikin tunanin irin sa'ar da na yi kasancewata cikin ƙoshin lafiya ba. A wani gefe kuwa na shiga yanayin tausayawa ga waɗanda Allah SWT ya ɗorawa larurar rashin lafiya. Babu abun tausayi a duniya kamar maras lafiyar da bai da d'an abun hannunsa da zai nemi magani, karma a ce rashin lafiyar ta kasance ta ko a mutuce ko a yi rai. Amma mu likitoci kan ci karo da ire-iren waɗannan matsaloli a kullum, musamman ma a asibitocin gwamnati. A takaice dai, babu fa wata sana'a da za ta sa mutum ya ga tsananin talauci da kuma sheda raɗaɗinsa kamar zama Likita a Najeriya. A asibitocinmune za ka ga bil'adama ya juya bayansa yayi tafiyarsa gida da tabbacin cewa mutuwa zai yi saboda kawai bai da Naira dubu ashirin (20,000) ko dalilinta! Haka dai Malam talaka a wannan ƙasa ke mutuwarsa ke kukansa shi kaɗai. Amma fa a inda gizo ya ke saƙar shine, idan dai ba wata kiyayewar Allah SWT ta musamman ba, toh fa su kan su shafaffu da man na daf da ɗanɗana kuɗarsu!

Cutur numfashi ta korona baros ta sako ɗan Adam a gaba. Annobar ta zama gagara badau, gobara daga kogi maganinki sai LiIlahi, duba da yadda ta fara lallasa ƙasashen da s**a fi kowaɗanne ƙarfi a duniya. Cutar, ta yi ɗiban karan mahaukaciya da ƙasashen da su ka yi fice a ƙarfin tattalin arziki, da ƙarfin makaman ƙare dangi, da ƙarfin tsarin kiwon lafiya, da kuma lafiyayyun al'umma. Korona baros dai ta zama tsumagiyar kan hanya, ki shafɗi babba ki shafɗi yaro, wadda ba ta ware bambamcin launin fata, ko ƙarfin arziki, ko kuma aƙida.

Ƙasashen yammacin turai da arewacin Amurka, da kuma ma su arziki na nahiyar Asiya sun kere sa'a wajen kula da mutanensu da kuma son more rayuwa. Sun ɗaukaki rayuwar duniya ta yadda babu abinda suke tsoro kamar barinta. Hakan ya sa s**a tsunduma cikin duniyar kimiyya har ta kai da cewa ku san ba abun da ba su samo maganinsa ba sai dai mutuwar ita kan ta. Sun sa tsufa a gaba sai da s**a rage masa gudu. Sun yi kutse cikin taswirar halittar ɗan adam (wato DNA) domin ƙera wasu daga cikin sassan jiki. Sun kuma yi tanade-tanade irin na gayawa jini na wuce domin yanayin rashin lafiya na gaggawa. Kyakkyawan misali shine; a yau a birnin New York na Amurka an kai matakin da duk wani kira na gaggawa daga ɗan ƙasa da bai samu ɗauki cikin kimanin mintuna tara da rabi ba to tilas hukomomi sai sun bi ba'asi sun kuma ɗauki mataki na ba sani ba sabo.

Amma mu anan Najeriya za a iya cewa rashin sani (wadda ake cewa ya fi dare duhu) a tsakankanin shafaffu da man mu ya sa su tunanin cewa za su iya yin baba na ɗaka gemu na waje. Bi ma'ana, su a na su ɗan ƙaramin tunanin, za su iya son ran su yadda su ke so anan gida Najeriya, amma kuma su tsallaka Turai domin su mori waɗancan tanade tanade na lafiya ma su inganci da su turawa su ka tsarawa ta su al'ummar. Ma su hannu da shuni dai sun mai da zuwa waje domin duba lafiyarsu ya zama jiki. A matsayinka na jami'in kiwon lafiya a ƙasarnan kuwa, dole watarana sai ka haɗu da wanda zai yaɓa ma ka irin wannan batu a fuskarka. Akwai yanayin raini da wannan mutane ke da shi; mai kamar cewa ni fa waɗannan asibitocin na ku ba irin nawa ba ne.

Amma fa batun gaskiya anan shine: shin idan wani abu na gaggawa ya taso makwabta za'a naimo ko kuwa abokan hulɗa da ke can nesa? Da yawa harda waɗanda za su iya ɗaukar ɗawainiyar naiman lafiya a ko ina a faɗin duniya na mutuwa kullum a ƙasarnan ta silar bugawar zuciya da sauran makamantan cututtuka. Hakan na faruwane saboda ita dai bugawar zuciya ba ta jiran lokacin da ya wuce mintina talatin zuwa awa guda, ga shi kuma mu kwata kwata ba mu da wani tsari da k'warewa, da kuma isassun kayan aikin bada taimakon farko da kuma agajin gaggawa (emergency).
Babu wani abu da zai ƙara fallasa ainahin mummunan yanayin da harkar lafiyarmu ke ciki kamar wannan annoba ta Korona Baros. Ita dai wannan cuta idan tayi tsanani ta kan maƙure numfashin mutum ne, ta hanashi shan iska saboda lalata huhu da ta ke yi. A irin wannan yanayi kuwa kusan duk marasa lafiyar na buƙatar taimakon sinadarin iskar numfashi (wato oxygen). Wa su kuwa daga cikinsu har sai an kai ga ɗorasu akan injin numfashi na bentileto (ventilator).

Ita dai bentileto wata na'urar asibitice ta musamman mai taimakawa da numfashi wadda ke buƙatar likitoci na musamman (Anesthetics) domin sarrafa ta. Yau ƙasar Italiya ta shiga ƙarancin duka biyun, duk da kuwa cewa ƙasar na ɗaya daga cikin ƙasashe goma da su ka fi kowaɗanne ingancin tsarin kula da lafiyar al'ummarsu a duniya. Yanzu haka a arewacin ƙasar Italiyan, ƙwararrun likitocin da su kan su sun gajiya, ke yanke hukuncin wa zai rayu wa kuma zai mutu saboda ƙarancin na'urar bentileto.

Akwai dai darussa ma su dama da amafani ga Gwamnatoci da mu kammu ƴan Najeriya da ya kamata mu kiyaye daga wancan yanayi. Na farko dai dolene muɗauki dukkanin matakan kariya domin kare kawunanmu daga kamuwa da wannan cuta. Saboda da haka, abun a yabawa hukumomine, yadda mutanenmu da ke dawowa daga ƙasashen waje ke tabbatar da ingancin tsare-tsaren da aka tanadar a duk filayen tashi da saukar jiragen sama na Ƙasa da Ƙasa da mu ke da su a faɗin ƙasarnan. Amma fa akwai sauran aiki a gabanmu
Bijirewa gwaje-gwajen da aka tanadar a filayen jiragen da wasu mambobin majalisar tarayya su ke yi ba komai bane face nuna zallar rashin wayewa da ƙarancin sanin ya kamata a fili. Hakan misaline na irin tsantsar gadara da ƙafafa na wasu daga cikin shuwagabanninmu da ke kawo bala'in da kowama sai ta shafe shi. Shugaban ƙasa Muhammad Buhari yayi dai-dai da ya aikewa duka majalisun biyu da zungureriyar takarda dake gargaɗinsu akan waɗannan ɗabi'u.
Mu kuma ƴan Ƙasa a namu ɓangaren, dolene fa muzage dantse mu kiyaye dukkanin ƙa'idojin da masana da hukomomi su ke faɗa. Musamman ma na rage cinkoso, da yawaita wanke hannu, da kuma zama a cikin gida idan da damar yin hakan. Sannan kuma sai mu koma kan buzu domin yin addu'o'i da kuma tuba ga Ubangijinmu domin ya karemu daga wannan cuta, musamman ma irin nau'inta mai tsanani da k'asashen Amurka da Italiya ke fama da shi.

Domin kuwa a duk faɗin Najeriya fa ba mu da wannan na'urar numfashi ta bentileto (ventilator) da ta wuce guda Ɗari Biyu kacal. Sannan su kan su ɗari biyun na tattarene a manyan manyan asibitocin da ke manyan birane irin su Lagos, Abuja, Ibadan, Kano, Zaria da Fatakwal. Idan ka ɗakko wannan matsalar sannan ka ƙarata akan matsalolin asibitocinmu na yau da kullum irin na rashin wadatattu da kuma ingantattun kayan aiki da gadajen kwantar da marasa lafiya, da kuma rashin ƙwararrun ma'aikata, za ka gane cewa idan fa wannan cuta ta sakomu a gaba (Allah ya kiyaye) kamar yadda ta saka waɗancan ma su jan kunnen, toh fa sai ɗan buzun mu! Bambamcin dai kawai shine, a wannan karon, yadda aka dama haka kowa zai sha. Domin kuwa waɗanda a da ke guduwa Turai domin neman lafiya yanzu babu gurin zuwa. Ai dama duk girman duniyarnan dai kowa ya san gidan ubansa; duk da kuwa ƙoƙarin cureta wuri guda da a ke ta faman yi. Zuwan Korona baros kuma ya ƙara tabbatar mana da cewa giji dai lahira ce, kuma na ka dai dole sai na ka!

Akwai ƙwararan darussa kuma marassa daɗi da za a samu bayan wannan iftil'ain ya wuce. Ala dole sai wannan gijin na mu mai suna Najeriya ya zauna ya nutsu ya kuma san inda kansa ke masa ciwo. Zuwan Covid 19 ya sa lafiya ta ƙara tabbatarwa da kowa a duniya cewa ita ce dai uwar jiki, wadda Mallam bahaushe ke cewa 'sai da ke aka cin duniya, har ana ta marmari, har ana rawar jiki'. A saboda haka, ina da kusan tabbacin cewa duniya za ta zabura bayan wannan annobar. Za kuma ta shiga yin sabon shirin ko ta kwana - kamar yadda ta yi bayan barazanar nukiliya. Amma a wannan karon, za ta garzayane neman sabbin ilmin kiwon lafiya, da neman sani na musamman, da ƙirƙire - ƙirƙire da kuma uwa uba angiza magudan kuɗaɗe a gine ginen asibitoci da kayan aiki da horar da ƙwararru.
Mu ma dai a Najeriya dole mu shiga taitayinmu, mu kuma tsunduma a cikin wannan gudun yada kwarin wanin da za a yi domin tabbatar da cewa ba a ci gaba da barinmu a baya ba. Yanzu dai ya rage namu mu tattara hankalinmu a wuri guda, mu kuma farka, sannan musan ina muka dosa. Lokaci yayi da za muyi watsi da son zuciyoyinmu, mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar ɗai-ɗaikun banbance-banbance irin na siyasa, da ɓangaranci, da ƙabilanci dake tsakaninmu. A taƙaice dai, ba za mu taɓa iya tunkarar irin wannan ƙalubalen da ke gabanmu ba har sai mun zamto tsintsiya maɗaurin ki guda. A cikin irin wannan yanayi, tunanin cewa idan jifa ya wuce kaina toh ya fad'a kan uban kowa fa babban kuskurene. Tunda dai jifa irinna Korona ya nuna cewa zai iya yin kwana ya dawo ya fasa kan uban kowa ma!

Amma da yardar Allah SWT za mu ga bayan Korona Baros. Sai dai ya zama wajibi mu ƙudiri niyyar yin juyin juya hali a tsarin tunaninmu da kuma a aikace domin inganta harkar kiwon lafiyarmu. Domin ita fa harkar lafiya (ba ma ta Korona ba kawai) tamkar wata tsumagiyar kan hanyace, ta shafɗi Mallam Talaka ta kuma juya ta shafɗi Attajiri.

Admin: ÆLGATAFAWY

 .ITA GASKIYA!!!Gaskiya bada yawan mabiya take tabbataba, da karfin hujja ne, karfin hujjar gaskiya shi ne yake sa abita...
20/02/2020

.

ITA GASKIYA!!!

Gaskiya bada yawan mabiya take tabbataba, da karfin hujja ne, karfin hujjar gaskiya shi ne yake sa abita ba yawan mutane bane...

Kamar yadda babu rayuwa ga kasa Sai da ruwa, Hakanan babu rayuwa ga Zuciya Sai Dla Ilmi.Allah ka bamu Ilmi mai Albarka.

Sannan kada ka sifanta da girman kai, da dagawa, da isa, da fankama, domin wannan mummunar dabi'a ce, kuma bakin hali ne.

Ya Allah ka dora mu akan turba ta tawali'u domin neman yardar ya Allah. Amin.

 .A doctor who cannot take a good history and a patient who cannot give one are in danger of giving and receiving bad tr...
15/02/2020

.

A doctor who cannot take a good history and a patient who cannot give one are in danger of giving and receiving bad treatment.
~Paul

Everyone may agree upon the diagnosis, but not everyone may consent to the therapy(That is how Nigerians people are, most of us can cited, and explore problems but can not identify the way out, their complain always increase with poor problems solving finding method.) Indeed, for healing,things have to be sacrificed at times and separation or loss might always be heartbreak and leave scars of remorse or regret.

If our leaders are and we are the patients who has the problems???
Who really provide poor analytics problems solving finding???
Who has the Paul???
Answer please!!!!
Answer!!!!!
Answer!!!!

May Allah forgive our past sins and bless our struggles.Juma’at Mubarak.
14/02/2020

May Allah forgive our past sins and bless our struggles.

Juma’at Mubarak.

 .Before you examine the body of a patient,Be patient to learn his story.For once you learn his story,you will also come...
12/02/2020

.

Before you examine the body of a patient,Be patient to learn his story.
For once you learn his story,you will also come to know His body.

Note:Our leaders are our Doctors here(We are the patients)

Before you diagnose any sickness,make sure there is no sickness in the mind or heart. For the emotions in a man’s moon or sun,Can point to the sickness in any one of his other parts.

~Suzzy kassem.

When a lot of remedies are suggested for a disease, that means it cannot be cured.
~Anton Chekhov
(Always they're saying follow this,try this do this, A karshe Sai kaji ana cewa Ina matsalar take??)

 .Sau da yawa zakaga korafen talakawa akan Masu mulki.To amma, wai su shugabannin namu da muke korafi kansu, daga ina su...
09/02/2020

.
Sau da yawa zakaga korafen talakawa akan Masu mulki.
To amma, wai su shugabannin namu da muke korafi kansu, daga ina suke? Aljanu ne su? Ko allanmisiru ne? Mutane ne kamarmu, daga cikinmu, ‘yan uwanmu, masu kamanni irin namu, da s**a taso a tsakaninmu. In kuwa haka ne, meye marabinmu da su? Jama’a, mu sake nazari!

Watarana, bn Marwan, daya daga cikin sarakunan musulunci daga cikin kabilar Banu Umayya ya ji jama’a, musamman malamai da wasu cikin manyan gari suna ta korafi kan yadda yake tafiyar da mulkinsa. Cewa akwai zalunci, akwai sama-da-fadi, akwai kashe-kashe da dai sauransu. Nan take ya tara su. Bayan su taru, sai yace musu: “Ina jin duk korafin da kuke yi a kaina ko tsarin mulkina. Tambayar da zan muku ita ce: kuna son in zama irin su Abubakar da Umar?” Nan take kowa yace: “Eh, tabbas muna so.” Sai yace musu: “To, ku ma ku zama irin mutanen da s**a kasance karkashin su Abubakar da Umar.”
......
??

Oh, how precious time is! Blessed are those who know how to make good use of it. Oh,if only all could understand how pre...
06/02/2020

Oh, how precious time is!
Blessed are those who know how to make good use of it.
Oh,if only all could understand how precious time is, undoubtedly everyone would do his best to spend it in a praiseworthy manner!!!

.

Address

Gatafa Town
Auyo

Telephone

+2347062691479

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Damace Kawai Global Network posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Damace Kawai Global Network:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram