27/06/2024
Ma'aikaciyar lafiya: mai aikin dare (Night shift)
Mazaje da dama sukan guji auren ma'aikaciyar lafiya musamman "Nurse" saboda aikin dare (aikin kwana). Akwai abubuwan da kuke buƙatar sani game da hakan, ga wasu daga cikin abinda na nazarta a tare da mas'alar:
1. Tabbas babu makawa aikin dare tilas ne ga ma'aikatan jinya "Nurses" maza da mata, musamman waɗanda basu jima sosai da fara aiki ba, da waɗanda basu da fannin ƙwarewa "specialty". Ƙalilan ne cikin ma'aikatan jinya waɗanda basa aikin dare. Aikin dare shine aiki mafi tsayin zango da Nurses suke yi a asibiti, aiki ne na kimanin awanni 12, kuma shine ke zama ƙalubale ga Nurses mata, musamman matan aure da masu shirin yin aure.
2. Ba kullum ne ake aikin dare ba, galibi baya wuce kwana 4 (a jere) bayan haka za'a yi hutu (Off) na tsahon kwana 3, ko kuma kwana 7 (a jere) sannan ayi hutu (Off) na kwana 7, sannan a shiga aikin yamma, da kuma na safe, haka yake a kowanne wata, ya danganta da tsarin asibitin da kuma unit ko ward ɗin.
3. A jihohinmu na Arewa galibin nurses mata (ba duka ba) suna aiki ne a ɓangarorin da ake jinyar mata zalla, kamar ɗakin haihuwa, ɗakin awon ciki, ɗakin jarirai, ɗakin rigakafi, ɗakin mata majinyata da sauransu.
4. Asibiti muhalli ne mai aminci ga 'ya mace mai mutunci da kamewa. A gefe guda kuma muhalli ne mai haɗari ga 'ya mace mara tarbiyya mara kamewa. Kowanne tsun-tsu dai kuka gidansu yake, idan dai ka yarda da nagarta mace, to kada kayi shakka a tare da ita yayin da ta tafi aikin dare domin tana cikin hidimar al'umma har sai ta dawo gida.
5. Shi fa aikin lafiya musamman sashin jinya aikine na sadaukarwa, kowanne mutum zai yi burin bayarda gudunmawa wajen ceton rayukan al'umma da kulawa dasu yayin da suke cikin mawuyacin hali, idan ance mace ba zata yi aikin jinya ba to abin tambaya shine waye zai jinyaci mata ?
5. Kowanne namiji idan yana da mara lafiya mace (Uwa, 'ya, 'yar uwa ko mata) fatansa shine ta sami kyakkyawar kulawar jami'ar jinya mace musulma jajirtacciya mai karamci.
6. Akasarin nurses mata suna da juriya, hazaƙa, himma da ƙwazo, domin sun saba hidimawa marasa lafiya daban-daban, don haka babu shakka ana saran zasu kasance a sahun gaba a fannin jigilar iyali a halin zaman lafiya da halin jinya. Don haka, tabbas ya dace ayi rigegeniya wajen auren jami'ar jinya "Nurse" wacce aka nutsu da halayenta.
7. A ƙarshe, ga duk namijin da ya san cewa shi duk da muhimmancin aikin jinya ga 'ya mace, duk da yadda ya nutsu da nagartar mace, idan har ya kasa nutsuwa da fitarta aikin dare, gwara ya haƙura da auren "Nurse" salun-alun, domin baya yiwuwa ka rabata da wannan aikin bayan ka aureta komai wadatarka, domin ba don kuɗi kaɗai akeyi ba.
8. Hana matarka, 'yarka, ko 'yar uwarka yin aikin jinya hani ne bisa kyakkyawan aiki, domin aiki ne mai muhimmanci ga al'umma, ya kusata a wayi gari a rasa mata amintattu waɗanda zasu yi.
Allah ya fahimtar damu!
✍️
Nurse Umar S. A