30/01/2026
Idan kin gaji da yin alluran tazaran haihuwa kizo ga Patch. Mannawa kawai zakiyi ajiki shikenan kin huta.
Patch wata hanya ce ta tazarar haihuwa wadda ake liƙawa a fata, tana sakin sinadarai a hankali zuwa jini domin hana ɗaukar ciki.
Patch ɗin na ɗauke da sinadarai biyu:
~ Estrogen
~ Progestin
Yadda Patch Ke Aiki a Jiki
~~~~~~~~~~
Sinadaran da ke cikin Patch suna aiki ta hanyoyi uku:
✓ Yana hana fitowar ƙwan mace (ovulation), don haka babu ƙwan da zai haɗu da maniyyi.
✓ Yana sa majinar bakin mahaifa (cervix) ta yi kauri, wanda hakan ke hana maniyyin namiji shiga mahaifa.
✓ Yana canza yanayin mahaifa, ta yadda ko da an samu haɗuwa, ba zai yi sauƙin samun ciki ba.
Yadda Ake Amfani da Patch
~~~~~~~~~~~
~ Ana liƙa Patch sau ɗaya a mako.
~ Ana liƙa Patch na makonni uku a jere,
~ Sannan a bar mako guda ba tare da Patch ba domin jinin al’ada ya sauka.
Ana iya liƙa Patch a:
~ Hanu
~ Cinya
~ Baya
~ Ciki
(amma ba lika a kan nono)
Amfanin Patch Ga Lafiyar Mace
~~~~~~~~~
1. Yana hana samun ciki da ba a shirya ba.
2. Yana sauƙaƙa amfani, ba sai an sha kwaya kullum ba.
3. Yana taimakawa wajen daidaita jinin haila.
4. Yana rage ciwon mara da radadin al’ada.
5. Yana rage yawan zubar jini ga masu al’adar jini mai yawa.
6. Yana taimakawa wajen rage kurajen fuska ga wasu mata.
Laulayi Ko Matsalolin da Za Su Iya Faruwa
~~~~~~~~~~
Ba duka mata ba ne ke fuskantar waɗannan matsaloli, amma wasu na iya samu:
1. Tashin zuciya
2. Ciwon kai
3. Jiri
4. Ciwon nono ko kumburinsa
5. Ƙarin kiba (ga wasu)
6. Canjin yanayin al’ada a farkon amfani
7. Fitar Patch daga fata idan bai manne da kyau ba
Kada A Yi Amfani da Patch Idan:
~~~~~~~~~~
1. Kina da hawan jini mai tsanani.
2. Kina da ciwon zuciya ko tarihin bugun jini.
3. Kina shayarwa kuma jaririnki bai kai watanni 6 ba.
4. Kina da ciwon dajin nono ko tarihin sa.
5. Kina da ciwon hanta mai tsanani.
6. Kina shan taba sigari kuma shekarunki sun haura 35.
7. Kina fama da zubar jini ta farji ba tare da sanin dalili ba.
8. Kina shan wasu magunguna k**ar:
~ Magungunan farfadiya
Rifampicin (maganin tarin fuka)
Shawara:
1. Kada a sayi Patch a yi amfani da shi ba tare da shawarar ma’aikacin lafiya ba.
2. Dole ne likita ko ma'aikacin jinya su tantance mace kafin fara amfani da Patch.
3. Idan Patch ya fita daga jiki ko aka manta a canza shi a kan lokaci, a je asibiti domin samun shawara.
Lafiya Uwar Jiki