04/09/2022
INA MAZAN: Ka auro 'Yar mutane lafiyar ta kalau, Da kai da 'ya'yan da kuka haifa kuka jigata jikinta, ta haihu sau Uku ko sau Hudu da dai sauransu.
Sai kai kake ganin ai ta tsufa, Waye ya barta ta tsufa? Ko mota ka saya duk wata sai kaje kayi mata service na dubu 20 ko dubu 30, Nawa kake bawa matarka taje tayi service? Nawa kake bawa matar ka ta sai kayan kwalliya ta sai kayan gyare-gyare?