29/12/2025
Yadda Ake Jima'in Neman Haihuwa
A darusan mu na baya mun yi bayanin cewa, shi Jima'i ana yinsa ne saboda abubuwa guda uku, na farko shine ma'aurata su kwantar da sha'awar da suke da ita na wannan Jima'i. Sai na biyu domin tabbatarwa da juna soyayya, na ukunsu wanda kuma shine yake da mahimmanci shine Jima'i neman haihuwa.
Ma'aurata da dama basu iya bambamce wadannan nau'ikan Jima'i ba, kawai dai suna yinsu ne yadda ya samu, hakan yasa wani lokaci za a yi ta Jima'i ba tare da samu sakamakon abunda yasa ake yi ba.
A wannan darasin zamu yi bayani ne akan Jima'i na neman haihuwa saboda shine yake da mahimmanci fiye da sauran, kuma shine akasarin ma'aurata basu san yadda zasu yi shi ba.
Shi dai wannan nau'i na Jima'i kamin ma'aurata suyi shi domin neman haihuwa, akwai wasu shirye shirye na musamman da ya kamata suyi domin yin wannan Jima'i da haka ne za a iya sa a smau dacewa da abunda ake fatan samu.
Abu na farko da ma'aurata zasu fara yi shine yin shawaran abunda suke burin ganin sun haifa, namiji suke son haihuwa, mace ko tagwaye, su tagwayen maza zalla, mata zalla ko shin kafa da wake, ana son suyi kamani da juna ko kowanne ya fito yadda ya samu. Wannan shine shawaran da ma'aurata zasu soma yi kamin tinkaran Jima'i neman haihuwa.
A kimiyance, a yanzu haka masana sun gano irin nau'in cimakan daya kamata ma'aurata suci ko su rika ci ko yawaita ci idan suna son yin ciki na musamman. Haka nan kuma su kauracewa cin wasu abincin Idan Namiji suke son haihuwa an ware irin abincin da mace zata rika ci, shima mijin nata haka, haka ma idan mace ko tagwaye ake son haifowa akwai abinci na musamman da Ma'auratan zasu maida hankali wajen cinsu. (a darasin mu na gaba zamu kawo irin wadannan cimakan)
Bayan kun maida hankali wajen cimakar ku, abu na gaba kamin Jima'in neman haihuwa shine kintatan lokacin Ovaluation na mace, wato lokacin da take daf da kenkensa kwan cikinta, a wannan lokacin maniyi na shiganta sai ciki. Wannan lokacin yana farawa ne daf da mace ta kusa yin al'ada, kuma a wannan lokacin duk mace take shiga Jaraba da sha'awar son yin Jima'i. Mata suna sanin wannan lokacin don haka ba wahala yake yi ba wajen macen data ke da sanin lokacin ganin watan ta.
Addu'a kamin afkawa Jima'i yanada matukar mahimmanci musamman a Jima'i na neman haihuwa. Don haka ya zama wajibi ma'aurata su nemi wannan bukatar wajen mai bayarwa domin neman abunda zasu dace da samu ya zama mai albarka.
Baya ga kintatan wannan lokacin ga Ma'auratan dake nema haihuwa, sai kuma yanayin kwanciyar jima'i daya dace da neman haihuwa. Domin ba duk yanayin Jima'i ake yi ba idan ana son mace tayi ciki.
Yanayin da s**a fi dacewa domin neman haihuwa sune yanayi na goho da kuma kwanciyar magirbi na miji akan mace. Wadannan sune ciki yake saurin shiga idan ma'aurata sunyi dace. Don haka kada masu neman haihuwa suje su yi ta yin yanayin kwanciyar da ba wadannan bane.
A Jima'i neman haihuwa ba a bukatar har sai ita mace ta samu gamsuwa musamman idan mace ce wacce take daukan lokacin kamin tayi zuwan kai, da zaran namiji ya kawo, to kada ya ce sai ya jigata mace ko ya juyata a dole tayi zuwan kai, wannan bazai bada abunda ake so ba. Haka nema shma namiji idan Dan tazarce ne kada yace zai zarce bayan yayi zuwan kai.
Ka da namiji yayi saurin cire arzakarinsa a gaban matarsa bayan yayi yayi zuwan kai har sai ya samu wasu lokuta gabansa ya tsane a cikin ta kamin ya dagata. Ita kuma mace kada ta ce zata yi wuf ta tashi taje ta wanke gabanta nan take ba. Ta bari sai bayan kaman mintuna 30 zuwa 40 kamin nan ta tsaftace gabanta. Haka nan a tsawon wannan lokacin zuwa makwanni 2 zata daina cin wasu abubuwa ko sha musamman wanda tasa zai iya wanke mata mara.
Daga nan sai ma'aurata su bi lamarin da Addu'a domin nema Allah yasa su dace da abunda suke nema wajen sa.
Wadannan a takaice shine shiri na musamman domin tinkaran Jima'i da maauara suke son suyi domin dacewa da yin ciki.
WHATSAPP CHANNEL GROUP LINK
ππππππππππ
https://whatsapp.com/channel/0029VbAeN1X2P59sFgPoIF3r
Magungunan ma'aurata