07/11/2025
AMFANIN SHAMMAR GA MATA TA ƁANGAREN NONO
Haƙiƙa, gaskiya ne cewa nono ado ne ga mace. Rashin sa ko ƙanƙantar sa na iya zama tawaya a wajenta. Haka nan, girman sa da kyau yana iya jawo hankalin mijinta fiye da yadda take zato.
Saboda haka, ƴan'uwa mata, yana da muhimmanci ku fahimci wannan bayani sosai, domin gyaran nono ya kasu kashi uku:
1. Rashin nono ko ƙanƙantarsa – tana so ya ƙara girma.
2. Girman nono ya wuce kima – tana so ya rage ya koma madaidaici.
3. Nonon ya kwanta gaba ɗaya – tana so ya miƙe ya koma kamar na budurwa.
Akwai hanyoyi da dama da ake amfani da su don magance waɗannan matsaloli, amma za mu fara da bayani a taƙaice kan na farko, wanda shine ƙanƙancewar nono. Wannan shine matsala mafi yawa da mata ke buƙatar mafita akai.
Hanya mafi sauƙi don ƙara girman nono:
1. Shan garin Shammar (Fennel): Ki samu garin Shammar mai kyau ki riƙa ɗiba tea spoon ɗaya kina zubawa a cikin ruwan dumi kofi ɗaya, sannan ki sha safe da yamma.
2. Shafawa da mai: Ki samu man Hulba da man Gelo (Castor Oil), ki haɗa su waje ɗaya, sai ki garwaya. Ki riƙa shafawa a kan nono gaba ɗaya sau biyu a rana.
3. Sanya rigar mama mai dacewa: Kada ta matse sosai, kuma kada ta yi yawa.
In sha Allah, idan aka bi wannan hanya na tsawon wata ɗaya, za a ga canji ba tare da wahala ko kashe kuɗi mai yawa ba. Idan kin samu biyan buƙata, to ki dakata da amfani da maganin don kada girman nonon ya wuce misali har ya zube.
NB: Ana samun waɗannan magunguna a wajen masu sayar da magungunan Musulunci (Islamic Medicine). Shammar na asali yana da ƙamshi kamar turare, idan aka baki wanda baya ƙamshi, to ba na asali bane.
Fatan mu shine Allah ya mana dace gaba ɗaya, ya kuma ƙara mana lafiya, ya kuma bawa marasa lafiya lafiya.
Ameen Yā Hayyu Yā Qayyum.