11/01/2026
Yan Comment sunce wannan mugu ne to ni Kuma nace alkhairi domin akwai wasu cututtukan da suke da wahalar magani yake magance su. Nayi Alkawari Cewa Idan kuka Saka Sadakatul Jariya Fisabilillah na siyan Soler GA wani Masallaci zan bayar da fa'idojin Shi da yardar Allah.
FALALAR YIN GAGGAWAN AYYUKAN SADAKATUL JARIYA
FĪSABĪLILLĀH
Alhamdulillāh, muna gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa ni’imominSa.
Hakika muna jinjinawa ’yan’uwa Musulmi bisa gudummawar da kuka bayar kwanakin baya, inda cikin ikon Allah aka samu Naira Miliyan Ɗaya, aka yi aikin jinya ga yaro mara lafiya.
Allah Ya saka muku da Aljannatul Firdaus.
Yanzu kuma, muna neman taimako domin AIKIN SAKA SOLAR SYSTEM NA MASALLACI, aikin Sadakatul Jariya wanda ladansa ke ci gaba da gudana har bayan mutuwa.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Idan ɗan Adam ya mutu, ayyukansa suna yankewa sai guda uku:
Sadaka mai gudana, ilimi mai amfani, ko ɗa nagari da ke masa addu’a.” (Sahih Muslim)
Allah Maɗaukaki Ya ce:
“Ku yi gaggawan zuwa ga gafarar Ubangijinku da Aljanna…” (Āli-Imrān: 133)
Rayuwar duniya mai wucewa ce, kuma babu wanda yasan wane aiki ne zai zama na ƙarshe a rayuwarsa. Saboda haka, yin gaggawa wajen aikata alkhairi babbar hikima ce.
Bayanan Aikin:
Jimillar kuɗin aikin da ake nema: ₦535,500
Abin da aka samu zuwa yanzu: ₦83,000
Har yanzu muna bukatar taimakon bayin Allah ba tare da Suna Raina Abun da zasu Saka a matsayin Sadakatul Jariya Fisabilillah ba domin kammala aikin kafin zuwan Azumi In Sha Allahu.
Kuma Idan akwai Wanda zai iya siyo komai yazo yasa Shima Muna maraba da wannan Domin butinmu shine ayi Aikin Domin gudanar da tafsiran azumi da sauran ibadu Cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
BANK DETAILS
Bank: Moniepoint MFB
Account Number:
6458095114
Account Name: Khairul Umma Foundation Services
Domin ƙarin bayani: 08037624598
“Ku rika aikata alkhairi, watakila ku rabauta.” (Al-Hajj: 77)
KADA KA JINKIRTA ALKHAIRI, DOMIN BA KA SAN WACE RANA CE TA ƘARSHENKA BA.
Allah Ya karɓa daga gare mu gaba ɗaya. Āmīn.
Yan'uwa Musulmi Don Allah muyi share ga wasu Domin suma su taimaka Fisabilillah