20/10/2025
AMFANIN YA'YAN KABEWA GA LAFIYA
(1) Taimakawa Aikin Garkuwar Jiki:
Ya'yan kabewa suna da wadataccen sinadarin zinc, wanda yake taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa lafiyar garkuwar jiki.
Sannan Zinc yana taimaka wa jiki ya yaƙi cututtuka kuma yana karfafa samar da kwayoyin garkuwa. cin Ya'yan kabewa a kullum na iya bawa garkuwar jikinka ƙarfi sosai, musamman a lokacin sanyi da mura.
Yadda Yake Taimakawa:
Ƙara Samar da Kwayoyin Garkuwa: suna dauke da Zinc Wanda yana da matuƙar muhimmanci wajen haɓako da aikin kwayoyin garkuwar jiki
Kariya Daga Cuta: Shan ko cin ya'yan kabewa a kai a kai na rage yiwuwar kamuwa da cututtuka ta hanyar ƙarfafa garkuwar jiki.
(2). Inganta Barci Mai Kyau
Kwayoyin kabewa suna ɗauke da tryptophan, wani sinadarin amino da yake taimaka wa jiki samar da serotonin, wani hormone da ke sa nutsuwa da barci. Cin ya'yan kabewa kafin kwanciya na iya inganta barci da taimaka wa masu fama da rashin barci ko tangardar barci.
Ƙara Samar da Serotonin: Serotonin yana taimakawa wajen daidaita yanayi da tsarin barci.
(3). Inganta Lafiyar Fata da Gashi
Yawan antioxidants da ke cikin ya'yan kabewa na taimakawa wajen lafiyar fata da gashi. Antioxidants suna yaƙi da free radicals, sannan suna rage bayyanar tamukar tsufa da kuma kare fata daga lalacewa.
Haka kuma, zinc da ke cikin ya'yan kabewa na taimakawa wajen samar da collagen, wanda ke ƙara ƙarfafa gashi.
Amfanin Kyau:
Kare Tsufa da Wuri: Antioxidants suna kare fata daga lalacewar da yanayin muhalli ke haddasawa.
Ƙara Girman Gashi: Zinc yana taimakawa wajen gyara gashin da ya lalace da kuma ƙarfafa ci gaban gashi.
flow:- Salihannur-Herbal-Medicine
Whatsapp:- 0816 882 5594
Call:- 09073338538