07/07/2023
Kasa da sa'o'i 24 da ambaliyar ruwa, Gwamnatin Dikko Radda ta fara gina magudanan ruwa a duk inda ake bukatarsu
Gwamnatin jihar Katsina ta ba da wani umurnin gaggawa na ginawa tare da fadada magudanan ruwan da ake da su musamman cikin kwaryar birnin Katsina.
Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ta hannun mataimakinsa Faruq Lawal Jobe ta ce hakan zai ba ruwa damar wucewa salin-alin a duk lokacin da aka samu mamakon ruwan sama.
A lokacin da yake ganawa da manema labarai a lokacin da ya ziyarci inda aka samu ambaliyar ruwan, Hon. Faruq Jobe, ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta yi umurnin gaggawa na a sake buda magudanan ruwa a inda ba su wadata ba, da kuma gina sabbi a duk inda babu, domin ruwan ya samu damar wucewa ba tare da ya yi ambaliya ga gidaje da dukiyoyin al'umma ba.
Da wannan umurni na Gwamnatin Malam Dikko Radda, kamfanin da aka baaikin, zai kammala cikin kankanin lokaci ganin yadda damina ke kara inganta.
SSA Isah Miqdad,
Ofishin Daraktan Yada Labarai.
7/07/2023.