28/10/2025
Please Follow Dr. Shuwa Al'ihsan
Koda (kidneys) su ne sassan jiki da ke tace datti da gubobi daga cikin jini, sannan su fitar da su ta fitsari.
Idan ba a kula da abinci ba, abubuwan da muke ci na iya lalata aikin koda a hankali har ta kai ga cutar koda (kidney disease).
Ga abincin da ya kamata a guje masa don kare lafiyar koda.
1. Gishiri Mai Yawa (Salt/Sodium).
• Shan gishiri da yawa yana ƙara hawan jini, wanda ke matsa wa koda aiki fiye da kima.
• AGuji amfani da kayan miya masu ɗauke da sinadarin sodium kamar Maggi cube da soy sauce sosai.
• A rage amfani da abinci da aka yi musu seasoning da yawa.
Shawara:
" A yi ƙoƙarin amfani da kayan ƙamshi na halitta kamar tafarnuwa, albasa, da daddawa maimakon gishiri mai yawa".
2. Nama Mai Kitse da Jajayen Nama
• Yawan cin nama mai kitse (kamar nama ja, kilishi, suya, tsiren nama) yana ƙara yawan sinadarin protein da cholesterol a jiki.
• Wannan yana iya haifar da toshewar hanyoyin jini da kuma rage aikin koda.
Shawara:
"A Rage cin nama ja, a fi amfani da kifi ko kaza ba tare da mai ba.
3. Abinci Mai Sanyi (Processed Foods & Fast Foods)
• Abincin gwangwani, snacks, noodles, da chips suna ɗauke da sinadarin sodium da sinadarai masu cutarwa.
• Su kan yi wa koda nauyi wajen tace gubobi.
Shawara:
" A fi yawaita son dafaffen abinci da sabbin abinci daga gida da kayan lambu".
4. Kayan Zaki da Abin Sha Mai Sugar
• Yawan sugar yana haifar da ciwon suga (diabetes), wanda shine babban dalilin lalacewar koda a duniya.
• AGuji shan lemukan kwalba, energy drinks, da kayan zaki masu sukari da yawa.
Shawara:
"A fi amfani da ruwan zafi, ruwa na 'lemon', ko zobo ba tare da sugar ba".
5. Abincin da ke da Potassium ko Phosphorus Mai Yawa
• Idan kodar tana da rauni, waɗannan abubuwan na iya taruwa a jiki su zama guba:
• Banana.
• Avocado.
• Kayan dairy (madara, cuku, yogurt).
• Kayan gwangwani da kifi na tin
Shawara:
" Tuntuɓi likita kafin cin waɗannan, musamman idan an ce ana da matsalar koda".
6. Shan Barasa da Magunguna ba bisa ka’ida ba
• Barasa yana lalata ƙwayoyin koda kai tsaye.
• Shan magunguna kamar painkillers (ibuprofen, diclofenac, aspirin) ba tare da umarnin likita ba na iya lalata koda sosai.
ABINCI MAI KYAU GA KODA:
✓ Ruwa mai tsafta.
✓ Kayan lambu da fruits masu potassium kaɗan (kamar apple da watermelon).
✓ Kifi ko kaza ba tare da kitse ba.
✓ Wake, dawa, da gero a cikin ma’auni.
SHAWARA:
• A sha ruwa isasshe (amma ba fiye da kima ba).
• A daina amfani da gishiri ko magani ba tare da shawarar likita ba.
• A dinga duba aikin koda a asibiti akai-akai musamman idan ana da ciwon suga ko hawan jini.