30/06/2022
Wanda Ya San Kimar Goro.....
Wani Uba ya cewa diyarsa a lokacin da ta gama karatu " yanzu kin kammala makaranta, ki dauki wannan motar da na siya shekaru da yawa da s**a shude. Amma kafin na baki ita, inaso ki dauke ta zuwa wajen masu saida kwancen motoci dake can gefen gari ki ga nawa za su yi mata kudi"
Wannan yarinya ta dauki mota ta kaiwa wadannan mutane masu siyen kwancen motoci, sai ta dawo wajen babanta ta ce " sun taya motar dala budu daya ($1,000), sun ce wai motar ta gaji sosai, wato ta tashi daga aiki.
Sai uban ya ce " yanzu ki dauki motar ki kai ta shagon 'yan jinga ( shago ne da suke karbar kayan kudi a matsayin jingina sai su bada aron kudi, in ka dawo da kudin sai su baka kayanka).
Sai yarinyar ta dawo da motar tace " sun min tayin dala dari kacal $100, sunce sabida motar ta tsufa sosai.
Uban ya kara cewa da 'yar tasa ta dauki motar ta kai wajen tarawa da adana motoci ( musamman tsofaffin motoci na tarihi).
Nan da nan yarinyar ta dawo ta cewa mahaifinta " wasu mutane a gurin sun ce za su bani dala Dubu Dari $100,000, saboda " mota ce mai daraja gami da dadadden tarihi, kuma ma'abota adana kayan tarihi suna matukar son irin wanann mota".
Sai uban yaiwa diyar tasa nasiha kamar haka:π
"Gurin da ya dace da kai, nan ne ake ganin darajarka yanda ya kamata". Idan wasu basu darajaka ba, kada ka damu, hakan yana nufin baka je inda aka san darajartaka bane, domin wadanda s**a san kimar goro sune suke sanya shi a algarara sannan su dinga yayyafa masa ruwa.
βοΈ BBilkeesu IbraheemIBilkeesu Ibraheem