Dr. Mukhtar Al-hafizy

Dr. Mukhtar Al-hafizy Fadakarwa tunatarwa

22/10/2024
11/04/2024
DAURAWA VS ABBA GIDA GIDAABINDA NA FAHIMTA :-NI AL-HAFIZY 1 -  MALAM IBRAHIM DAURAWA YA IYA MU'AMALA DA KOWA, DUK DA DAN...
05/03/2024

DAURAWA VS ABBA GIDA GIDA

ABINDA NA FAHIMTA :-
NI AL-HAFIZY

1 - MALAM IBRAHIM DAURAWA YA IYA MU'AMALA DA KOWA, DUK DA DAN IZALA NE AMMA BAYA DAGA CIKIN MASU CIN MUTUNCIN BAYIN ALLAH SABODA SABANIN FAHIMTA, NI DAI BAN TABA JI BA, KO DA YAKE BA KOWANE MALAMI NAKE SAURARON KARATUN SA SOSAI BA WATA KILA SABODA YAYI KARATUN ZAURE YA SAMU TARBIYYA TA MALAMAN ZAUREN.

2 - YA KWARE A HARKAR HISBAH DOMIN YAYI SHEKARU YANA SHUGABANCIN TA, DON HAKA, BA WAI BABU MALAMAN DA S**A FISHI BANE, A A KWAREWA A AIKIN HISBAH DA YANDA YAKE BADA GUDUNMAWA A HUKUMAR SABODA DADEWA DA YAYI, SHI YASA GWAMNATI BATA SAN RABUWA DA SHI, DOMIN (PRACTICE MAKE A PARFECT )

3 - YARON MADUGU NE, KAMAR YANDA ABBA YAKE YARON MADUGU, DON HAKA DOLE NE ABBA YA GIRMAMA WANNAN ALAQAR, DUKDA ABINDA YA FADA BA KUSKURE BANE, DOMIN SHI DA KANSA DAURAWA YACE : ZA SU YIWA YAN HISBAH TRAINING SABODA KURAKUREN DA AKE SAMU KUMA YACE : ZAMU KIYAYE DOKA,

4 - IDAN AKA BARI YAYI MURABUS YAN ADAWA ZA SUYI AMFANI DA WANNAN DAMAR SUYIWA GWAMNATI ME CI ILLA, BISA AL'ADAR YAN KWANKWASIYYA DA NA SANI, BASU CIKA BARI MASOYI YA ZAMA MAKIYI BA SE IN ABIN YA GAGARA,

5 - YAN IZALA SUN HADE KAN SU DOMIN SUNFI KOWA SANIN AMFANIN SA A HUKUMAR DOMIN MUNA DA MUTANE A HISBAH MUN SAN IRIN ROMON DEMOKORADIYYYAR DA AKE SHARBA, KUMA AKWAI DAMAMMAKI DA YAWA DA SUKE SAMU, DAN HAKA BAZA SU YARDA YAYI MURABUS BA, KUMA HAKAN DA S**AYI ABUNE ME KYAU, DA WASU NE DA MURNA ZA SUYI IDAN YACE YAYI MURABUS.

DARASIN DA NA KOYA:-

1 - MAFI YAWAN MASU YIN WA'AZI BA SA SO AYI MUSU WA'AZI.

2 - WASU YAN SIYASAR SUNFI FIFITA SIYASAR SU AKAN ADDININ SU

3 - IDAN GWAMNA YABA MUTUM MUKAMI KO DA YAGA KUSKURE KADA YAI MASA GYARA A BAINAR JAMA'A.

Allah ya gyara mana garin mu Allah ya taimaki gwamna da mukarraban sa, shi kuma DAURAWA Allah yayi ruqo da hannun sa yaci gaba da yin abinda ze kawo gyaruwa al'ummar mu.

IKON ALLAH MALAMAI A VILLAABIN MAMAKI SE KAGA MUTUM DA HANKALIN SA, AMMA YANA ZARGIN MALAMAI DAN SUNJE WAJEN SHUGABAN KA...
11/08/2023

IKON ALLAH MALAMAI A VILLA

ABIN MAMAKI SE KAGA MUTUM DA HANKALIN SA, AMMA YANA ZARGIN MALAMAI DAN SUNJE WAJEN SHUGABAN KASA !
KUMA DA ACE ZE SAMU DAMA A KIRA SHI SHIMA FA ZUWA ZAI YI,
ZUWA GURIN SHUGABA KO KAFIRI, KO MUSULMI, KO ADALI, KO AZZALUMI, BA LAIFI BANE, LAIFIN SHINE ME YA KAIKA ? KWADAYI KAJE KO NASIHA KAJE YI MASA, KO SHAWARA KAJE BASHI, KO KUMA TAIMAKON SA KAJE YI AKAN ZALUNCIN SA ?
WANNAN SHINE ABIN DUBAWA, MUNA KIRA GA MALAMAI IDAN SUN SAMU DAMAR HADUWA DA SHUGABANNI SU DINGA GAYA MUSU GASKIYA, MASAMMAN HALIN DA YAN KASA SUKE CIKI, IDAN DAI BAZA IYA FADAWA SHUGABA GASKIYA BA, TO ZUWA GURIN SA BA SHI DA AMFANI, KUMA HARAMUN NE,
ALLAH YA SA MALAMAN MU SU GANE KUMA SU GYARA, SU KAI BUKATUN AL'UMMAR SU, BA BUKATUN SU BA.

INNALLAHA YA MURU BIL ADLI WAL IHSANI...

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr. Mukhtar Al-hafizy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Dr. Mukhtar Al-hafizy:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram

Category