Dr Kamal Fita Atom

Dr Kamal Fita Atom Great Anatomist/Vibrant Comrade/Medical Student/Teenager

18/04/2022

*MAGANGANUN ANNABI*
*(S.A.W) GAME DA LAFIYAR JIKI*

1: Ku shaayar da Matayenku masu ciki Nono, domin yana qara qarfin Hankalin Jariri.

2: Duk wanda ya saba yawan ci da sha, zuciyarsa zata Qeqashe.

3: Abubuwa 3 jiki na jin dadinsu:

i: Sanya Turare.

ii: Tufafi mai
laushi.

iii: Shan Zuma.

4: Ina shawartanku da Zuma, na rantse da wanda raina yake hannunsa, babu wani gida da akwai zuma cikinsa face mala'iku sunaiwa mutan gidan Istifaari, Idan Mutum yasha Zuma, Magunguna Dubu sun shiga cikinsa, kuma Cuta Dubu ta fita,daga jikinsa, in yamutu alhali zuma na cikinsa, wuta bazata shafeshi ba!

5: Duk maison Qarfin Hadda, to ina shawartansa da shan zuma.

6: Idan mace ta Haihu, yazama, farkon abinda zata ci shine

Danyen dabino mai zaqi da kuma
busashe, domin da ace akwai wani abu dayafi wannan kyau ga mai jego, da Allah madaukaki ya shaayar da Maryaama a.s shi sanda ta haifi Isa a.s.

7: Naman saniya cuta ne, Nononta Maganine, Naman tumakai Maganine, nononsu cutane!!!

wannan modern science ya tabbatar dashi, domin Red meat cutane ga Lafiyar mutum, musamman wanda yakai 50+yrs,bsadaqa Rasulul Amiyn

8: Kuci Kankana, domin ita yayan
itace Aljannah ne, acikinta akwai Albarka dubu, da Rahama dubu, kuma cinta waraka ne daga dukkan cuta.

9: Kuci Kankana, domin ita abinci ce kuma abin sha, tana wanke ciki kuma tana qara lafiya , kuma tana gyara Fata.

10: Annabi Nuh ya kaiwa Allah
koken damuwa, sai Allah ya masa
wahayi akan yaci Inabi (grape) domin yana tafiyarda Damuwa!!!!!!

Allah ka Qaremu da Lafiya, Lallai
Manzon Allah s.a.w shine Babban
Qwararren likita, wanda ya qware batare da Course ko training ba! Allah kai salati ga Manzon Allah s a w.Barkan mu da shan ruwa jamaa🥛

04/04/2022

KULLUM DAI MATSALAR RASHIN TSARO GABA TAKEYI A KASARNAN.....
Hakan abune mai matuqar ban tsoro da tada hankalin duk wani mai tunani,domin kuwa abun yazama kamar wutar daji ganin yadda yake watsuwa da sauri cikin kauyuka,garuruwa da jihohinmu na arewacin wannan kasa.
Dayawa daga cikin kauyukan Sokoto,Zamfara da Katsina tuni yan bindiga sun dade da mamayesu ta hanyar kashewa da korar mamallakan wadannan kauyukan,wanda s**ansu wanda s**a tsira da rayuwar tasu basusan takamai-mai na Inda s**a dosa ba ayayin gudun ceton rai da sukeyi.
Suna gudun ne batareda debo kayan abinci ko wani nau'i na dukiyaba wanda zai taimakama rayuwarsu bayan sun tsira din,hakan ke tilasta wa dayawansu barar abinci da yar suturar da zasu sanya.
Dayawa a yayin harin da aka kaimusu a gidajensu tun anan ake kashe wadansu a cikinsu,wasu su rasa yayansu wasu mazajensu.
Wasu kuma tun anan a yunkurin gudun ceton rai ke rabuwa da yayan cikinsu,ko matayensu wanda watakil wannan rabuwar itace rabuwa ta karshen da zaiyi wahala a kara haduwa,domin rabuwa ce babu shiri,ba kuma wanda yasan inda dayansu ya dosa.
A Irin wannan yanayine har yanzu wasu acikinmu ke ganin ba'a yima wannan gwamnatin adalci ba matuqar aka sokesu ko aka ce sun gaza mussamman ta fuskar TSARO(Domin shine kadai abunda sai dashi akeyin komai koda Ibada kuwa)!

Muna rokon Allah yakawomana zaman lafiya a kasarmu🙏🏽

_Comr Kamal Fita Atom
4th April,2022

22/03/2022

TALAKAWA HAR YANZU DA SAURANMU.......

Ganin yadda zabe yake ta gabatomu,abun da matuqar ciwo ace har yanzu mutanenmu mussamman na arewacin kasarnan basu gama fahimtar muhimmancin katin zabe da zaben ba.

Ina mamakin yadda siyar da kuri'a ya zama kamar abun burga a wajen talaka,tayaya mutumin da ya sayi kuri'arka yaci zabe kake tunanin zaka sami wakilci nagari daga wurinsa?

Mutum zai siyar da kuri'arsa akan 500,1000 ko 2000 kawai saboda bukatarsa ta yan mintuna,batareda tunanin wahalar da siyar da kuri'ar zai janyomasa na shekaru ba.Menene amfanin badi ba rai?

Duk shugaban da zai sa kudi ya sayi kuri'a, alamace babba ta rashin nagartar wannan mutumin,domin hakika yasan bashida nagarta da shugaba ke da ita b***e ya samu mabiyan da zasu kada masa kuri'ar da zaibashi damar hayewa wannan kujerar,hakan yasa zaiyi amfani da kwadayi na dayawan cikinmu wajen siyan yancinsu (kuri'arsu) wanda koda ya hau wannan kujerar ba abunda zai tsinanamaku har sai ya biya muradansa da na wadanda suke kusa dashi,talakawa kuma ko o'ho.Sanin cewar tabbas ba cancantar sa ce ta sa yaci zabenba,aljihunsa ne yasa kuka zabeshi.

Abin takaici ma shine koda kayi niyyar hana irin wadancan talakawan da suke kokarin siyar da kuri'ar su,sai s**e" Ai wannan shine rabonmu,domin Idan yaci dama munsan bazamu sake ganinsa ba"Dama tayaya kuke tunanin wanda ya sayi mutumcinku kuka siyarmasa zai sake sauraronku?.

Ko kuma ka ji wadansu aciki suna cewa"Ai wanda yabaka wannan kudin ya sayi kuri'arka shine ke yi dakai(ma'ana shiyasan darajarka)".Tayaya mutumin da ke maku kallon kaji(Kaji sai da tsaba) yasan darajarku?

A karshe muna kira ga dai-daikun mutane,kungiyoyin gwamnati,kungiyoyi masu zaman kansu,da kowacce Irin kungiya da su tashi tsaye wajen wayar da kan mutane akan illar siyar da kuri'a ga Dan kasa.

Allah ya zabamana shugabani masu son cigabanmu da son cigaban kasarmu,Allah ya zaunar da kasarmu lafiya.....

Naku;
Comr Kamal Fita Atom
21st March,2022

Address

Kano

Telephone

+2348135972900

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr Kamal Fita Atom posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram

Category