26/04/2021
"ZAZZABIN CIZON SAURO"🦟🦟
A ranar 25th ga watan Afrilu na kowacce shekara ne hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya watau WHO ta ware don bikin ilimantarwa da wayar da kan al'umma game da cutar zazzabin cizon sauro 🦟 watau "Malaria"
👉 Mecece Malaria: Malaria cuta ce da kwayar cutar protozoa mai suna plasmodium take kawowa mai yaduwa ta hanyar cizon sauro 🦟.
Malaria cuta da ta addabi duniya kuma tafi qamari a yankin afrika, bincike a shekarar 2019 ya nuna 94% na cutar yana faruwa ne a afrika, binciken ya qara da cewa an samu akalla mutane miliyan 229 da s**a yi cutar yayin da dubu 409 s**a mutu a shekarar 2019 mafi yawancin su 67% yara 'yan kasa da shekara biyar wanda adadin su yakai dubu 274. Bincike ya nuna cewa malaria ta laqume adadin kudi kimanin dala biliyan uku US$3billion a shekarar 2019 (WHO, 2020).
👉 Me yake kawo malaria: Dangogin Kwayar cutar Plasmodium wadanda wata nau'in sauro mace🦟 (Anopheline) take yadawa, akwai dangin plasmodia guda biyar da aka tabbatar suna kawo Malaria
➡️ Plasmodium falciparum
➡️ Plasmodium Vivax
➡️ Plasmodium Ovale
➡️ Plasmodium malariae
➡️ Plasmodium Knowlesi.
duk a ciki nau'in falciparum da vivax ne s**a fi hatsari kuma su ake samu a yankin afrika.
👉 Wa yafi hatsarin kamuwa da Malaria: Bincike a shekarar 2019 ya nuna cewa kusan rabin mutanen duniya suna cikin hatsarin kamuwa da malaria, daga ciki
➡️ Yara yan kasa da shekara biyar
➡️ Mata masu ciki
➡️Mutane masu karancin garkuwar jiki.
➡️ Masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.
➡️ Matafiyan da basu da kariyar garkuwar jiki na malaria.
👉 Alamomin malaria:
➡ Zazzabi mai zafi
➡️ Ciwon kai
➡️ Ciwon ciki
➡️ Amai da tashin zuciya
➡️ Ciwon gabobi
➡️ Kasala
➡️ Kasa cin abinci
➡️ Jin sanyi
➡️ Idan malaria tayi tsanani tana iya kawo jijjiga, karancin jini, surutai da gane-gane da sauran su musamman a yara.
👉 Maganin Malaria: Ana iya amfani da magunguna da dama don zazzabin malaria, sau tari maganin malaria yana zuwa a hadi ne wanda ake kira Artemisin based combination therapy (ACT) a turance saboda yadda kwayar cutar take iya bijirewa magani daya, daga cikin nau'in ACTs sun hada da
➡️ Arthemeter-Lumenfantrine A-L
➡️ Dihydroartemisinin-Piperaquine DP
➡ Artesunate-Amodiaquine AA
➡️ Sauran magungunan malaria ana iya amfani dasu gwargwadon yadda ingancin su ya bayyana da kuma shawarar ma'aikatan lafiya. Guji shan magani gaba-gadi yana da hatsari ga lafiyar ka.
👉 Kariya/Rigakafi: Hanyoyin kariya daga zazzabin cizon sauro sun hada da:
➡ Amfani da gidan sauro mai magani ko sange (Insecticides treated nets).
➡️ Tsaftace muhalli da ya hada da sare ciyayi, share bola, Hana taruwar ruwa ko kwata a muhallai da sauran su.
➡️ Amfani da maganin sauro mai inganci.
➡️ Shan maganin kariya kamar Sulphadoxine-pyrimethamine (fansidar) musamman ga mata masu ciki da kuma Proguanil (paludrine) ga yara masu sikila.
➡️ Rigakafi: Rigakafin malaria har yanzu yana kan gwaji, wanda aka fara kirkira shine RTS,S/AS01 wanda a yanzu yaci kaso 75% na cimma nasara kuma an fara amfani dashi na gwaji a wasu kasashen duniya.
➡️ Maganin kariya na lokaci: Ana bayar da maganin kariya na lokaci watau Seasonal malaria chemoprevention (SMC) ga yara yan wata 3 zuwa wata 59 a lokacin da cutar tafi qamari na tsawon wata hudu a jere, magungunan sun hada da guda daya na Sulphadoxine-pyrimethamine (fansidar) da kuma Amodiaquine na kwana uku a jere duk wata tsawon wata hudu.