15/04/2026
Ruwan damuke Sha Yana Jin abubuwan damuke cewa Kuma Yana maida mana da martani akan maganganun mu na alkhairi kokuma Wanda bana alkhairi ba......
Masana kimiyya da dama sun gudanar da wani bincike akan abubuwan da suke kewaye damu, amma binciken Dr. Masaru Emoto fitaccen masanin kimiyya ne daga kasar Japan, ya girgiza duniya.....
Dr. Emoto ya gudanar da wani bincike na musamman inda yanuna cewa ruwa ba abune kawai da muke shaba yanada Rai, Kuma yanajin mu kuma yana fahimtar kalamanmu da tunaninmu.....
Dr. Emoto ya dauki samfurin ruwa ya sanya su acikin kwalabe daban daban, Bayan haka ya rika fadawa kowace kwalba maganganu mabanbanta, Ruwan da aka fadawa kalaman yabo da kauna kamar Nagode ko ina sonka.....
Da kuma Ruwan da aka fadawa munanan kalamai na kiyayya kamar Na tsane ka kokuma Wawa, kunsan abinda yafaru bayan Hakan.....????
Lokacin da aka daskarar da wannan ruwan guda biyu a firji sai aka duba siffarsa ta hanyar amfanida microscope, sakamakon yabawa kowa mamaki.....
Ruwan da aka yabawa ya samar da kyawawan siffofi masu ban sha'awa kamar lu'u lu'u da zinare, Ruwan da aka zage shi kuwa ya rikice, yakoma mai siffa mummuna, baka, kuma mara tsari......
Dan haka Jikin dan adam kusan kashi 70% ruwa ne, Idan har magana tana iya canza fasalin ruwan dayake cikin kofi, inaga ruwan dayake cikin jikinmu Kuma......?
Wannan yana nufin Kalamanmu sunada tasiri Idan muna fadin alhairi, jikinmu da rayuwarmu zasuyi kyau, shiyasa Wanda yake ambaton babu toh fa kullum zai dawwama ne a babun......
Kyakkyawan tunani yana gyara lafiyar jiki, Shiyasa idan aka karanta addu'a a ruwa aka sha, yake zama magani, domin ruwan ya dauki kyakkyawan sakon addu'ar......
Mu kiyaye harshenmu, mu rika fadar alhairi ga kanmu da kuma mutanen dake kusa damu, Domin ruwan jikinka yana sauraronka dafatan dai kaji Haladu saika Kiyaye Kaine kana Shan Ruwa kana Surutu na bacin Rai toh kasani dai ruwan ka yanajin ka.......