27/10/2023
Health Special Reporters.
Wasu Daga Cikin Yan jaridu da s**a Daura Damarar Tunkarar Kalubalen da Bangaren Lafiya ke Ciki a Jihar Kano.
Manufar Gudanar da Aikin na Binciken Kwakkwafi akan wasu Asibitoci Tare da Gano matsalolin da Gwamnatin Jihar Kano zata kawo Gyara Cikin Gaggawa.
Duk da cewa Gwamnati tana kokarin ta wajen Gyara da kuma Samar da Kayan Aiki a asibiticin Jihar Kano, To amma Hakan bai Hana Gano wasu Muhimman abubuwa da kalubale Dake Bukatar daukin Gaggawa ba.
Haka Kuma Duk da yadda Ake Biyan Hakkokin ma'aikatan asibitoci to amma a Wani Lokaci akan samu Sakaci na wasu Ma'aikatan da basa zuwa aiki kokuma Rashin zuwa akan Lokaci
Rashin Mutunta wasu Marasa Lafiya da wasu likitoci keyi Wanda Hakan yasaba da Doka shima wani kalubale ne Dake Bukatar daikileshi.
Akwai asibitoci a karkara wadanda suke Bukatar Kulawar Gwamnati duka suna Daga Cikin abubuwa da zamu tunkara.
Akwai Muhimman abubuwa da s**a shafi Lafiya Dake Bukatar kulawa wadanda insha allahu wadannan Hazikai zasu Tunkaresu Domin Fito dasu fili don Daukar Matakin Gaggawa
Nan Gaba Kadan zamu saki sunayen manema Labaran da zasu Tunkari wadannan matsaloli Domin Kawo Gyara a Bangaren Lafiya