Arewa Physiotherapy Clinic and Gymnasium

Arewa Physiotherapy Clinic and Gymnasium I help people become active and pain-free. Would'nt the life be better if you were not in pain? I make content to educate and also make CONSULTATION.

You can watch my educational content at : https://www.youtube.com/

01/04/2025

Yanke Shakku Kan Alaƙar Cin Jan Nama Da Ciwon Gwiwa

Miliyoyin mutane a faɗin duniya ne ke fama da ciwon gaɓɓai sak**akon lalurori daban-daban. Matsalar ciwon gaɓɓai na da illar gaske ga ingancin rayuwa, tattalin arziƙi da walwala. A wani lokacin ma idan matsalar ta ta'azzara tana iya nakasa mutum, sannan ta tsugunar da shi ɗungurungum.

Sai dai, wani abin mamaki shi ne yadda mutane ke alaƙanta ciwon gaɓɓai musamman ciwon gwiwa da yawan cin jan nama. Wannan ya sa da zarar mutum ya fara ƙorafin ciwon gwiwa sai ka ji an ce masa "ka rage cin jan nama".

To ko ya lamarin yake?

Da farko dai, ya k**ata mu fahimci cewa ciwon gwiwa iri-iri ne kuma kowanne na da sababinsa. Saboda haka, ba abu guda ne ke kawo duk ire-iren ciwon gwiwa ba.

Ire-iren cutukan gaɓɓai da ke iya janyo ciwon gwiwa sun haɗa da:

1) Amosanin gaɓa: Amosanin gaɓa, wato 'osteoarthritis' a turance, ciwon gaɓa ne sak**akon zaizayewar gurunguntsin gaɓa yau da gobe, musamman a gaɓɓai maɗauka nauyin jiki k**ar gwiwar ƙafa ko gaɓar ƙugu.

2) Sanyin ƙashin gaɓa, wato 'rheumatoid arthritis' a turance. Sai dai, sanyin ƙashin gaɓa ya fi shafar ƙananun gaɓɓai k**ar gaɓɓan yatsun hannu da ƙafa.

3) Ciwon gaɓa na shigar ƙwayar cuta cikin gaɓa ko jiki, wato 'septic arthritis' a turance. Irin wannan ciwo na iya k**a kowace gaɓa idan ƙwayar cuta k**ar bakteriya ta k**a jiki gaba ɗaya ko kuma wata gaɓa guda.

4) Ciwon gawut, wato 'gout arthritis' a turance, ciwon gaɓa ne da ke faruwa sak**akon taruwar gishirin "urate" a cikin gaɓa.

5. Ciwon gaɓa na bugu/rauni: Irin wannan ciwon gaɓa na faruwa musamman ga masu wasannin tsalle-tsalle da guje-guje k**ar 'yan wasan ƙwallon ƙafa da dai sauransu. Misali, sak**akon lahani ko bugu ga gurunguntsin gaɓa ko gammon gwiwa (meniscal tear). Ko kuma yayin da haɗarin abun-hawa ya ritsa da mutum kuma ya samu karaya a kan gaɓa, wannan na iya lalata muhimman sassan kariya da ke cikin gaɓar har ya haifar da ciwon gwiwa.

To ko wanne irin ciwon gwiwa ne ke da alaƙa da cin jan nama?

Daga cikin ire-iren cutukan gaɓa da ke janyo ciwon gaɓa wanda ake alaƙantawa da yawan cin jan nama shi ne ciwon gawut, wato "gout athritis" k**ar yadda muka ambata a sama.

Yadda ciwon gawut ke faruwa

A al'adance, jikin mutum na samar da sinadarin 'purines', yayin da jiki ya narka wannan sinadari zai haifar da wani sinadari da ake cewa 'uric acid'. Sinadarin 'uric acid' zai narke ya bi jini sannan ƙoda ta tace shi zuwa cikin fitsari.

Amma duk lokacin da jiki ya samar da sinadarin 'purines' da yawa saboda yawan cin nau'in abinci/abinsha da ke ɗauke da sinadarin 'purines' ko kuma yayin da ƙoda ta gaza tace sinadarin 'uric acid' zuwa cikin fitsari, wannan zai haifar da taruwar sinadarin 'uric acid' a cikin jini fiye da ƙima.

Haka nan, taruwar sinadarin 'uric acid' a cikin jini fiye da ƙima zai sa ya riƙa duddunƙulewa har ya zama gishirin "urate". Wannan gishiri na 'urate' shi ne ke taruwa a cikin gaɓɓai ya haifar da ciwon gawut wanda ke haddasa matsanancin ciwo, kumburi da rirriƙewar gaɓɓai.

Bugu da ƙari, akwai nau'o'in abinci/abinsha daban-daban da muke ci yau da gobe waɗanda ke maƙare da sinadarin 'purines' a ciki. Kuma cin irin waɗannan abinci/abinsha fiye da ƙima na iya kawo hauhawar sinadarin 'uric acid' a cikin jini wanda kuma daga ƙarshe na iya haifar da ciwon gawut.

Daga cikin abinci/abinsha da ke ɗauke da sinadarin 'purines' akwai:

1. Jan nama, k**ar naman saniya, rago

2. Naman kayan ciki, k**ar hanta, ƙoda, matsarmama

3. Naman ruwa, k**ar jatan lande (shrimp), kifi sadin (sardines), 'lobster', 'mussels', 'anchovies'

4. Barasa/giya, abinci/abinsha da ke ɗauke da siga nau'in 'fructose' k**ar lemukan roba, askirim (ice cream), alawar cakulet da sauransu.

Har wa yau, ganyayyaki k**ar alayyahu (spinach) da shekan ɓera (asparagus) na ɗauke da sinadarin 'purines' sosai, sai dai bincike ya tabbatar da cewa sinadarin 'purines' da ke cikin alayyahu da shekan ɓera ba ya janyo hauhawar sinadarin 'uric acid' a cikin jini. Saboda haka, ba su shiga jerin abubuwan da mai ciwon gawut zai ƙaurace wa ba.

Yaushe za a fara ƙaurace wa waɗannan abinci/abinsha da aka lissafa?

Za a fara bayar da tazara ko ƙaurace wa cin irin waɗannan nau'o'in abinci/abinsha ne da zarar likita ya tabbatar cewa mutum na fama ciwon gawut.

Amma mutum zai iya ci gaba da cin waɗannan nau'o'in abinci/abinsha matuƙar ba a tabbatar yana da ciwon gawut ba ko kuma babu ƙorafin ciwo ko kumburin gaɓɓai a jikinsa. Sai dai, a har kullum mafi kyawun lamari shi ne tsaka-tsaki.

To ya za a gane ciwon gwiwa daga ciwon gawut ne?

Ana gane ciwon gwiwa na da alaƙa da ciwon gawut idan aka samu alamun ciwo, kumburi, rirriƙewar gaɓɓai a sauran gaɓɓan jiki musamman gaɓar babban yatsan ƙafa.

Bayan duba waɗannan alamu, likita zai nemi a gwada jinin mutum don duba ƙimar sinadarin 'uric acid' a cikin jini. Za a gane ciwon gawut ne idan sak**akon gwajin ya nuna sinadarin 'uric acid' ya hau fiye da ƙima a cikin jini.

Daga nan kuma sai likita ya bayar da magungunan da za su temaka wajen daidaita sinadarin 'uric acid' a cikin jini.

Sannan a gayyaci likitan fisiyo (physiotherapist) don ci gaba da lura da matsalolin ciwon gaɓɓai, kumburi da rirriƙewar gaɓɓai. Likitan fisiyo zai yi duk mai yiwuwa wajen magance waɗannan matsaloli don mutum ya ci gaba da rayuwarsa cikin karsashi da walwala. Domin shan maganin kawai ba tare da ganin likitan fisiyo ba na da haɗarin kassarewar aikin gaɓɓai, wato nakasa.

Alamomin ciwon gawut

Daga cikin alamomin sun haɗa da:

1. Matsanancin ciwon gaɓɓai; ciwon na iya k**a kowace gaɓa saɓanin zaton cewa iya gwiwar ƙafa ciwon gawut ke k**awa kawai.

2. Kumburin gaɓɓai, jin ciwo idan aka taɓa/matsa gaɓar da ta kamu, sannan bayan gaɓɓan sun kumbura, za su yi ja kuma.

3. Rirriƙewar gaɓɓai yayin hutu da kuma yayin ayyukan yau da kullum.

4. Idan ciwon gawut ya ta'azzara, za a iya ganin bayyanar bulli, wato k**ar taruwar ruwa a ƙarƙashin fata a gefen gaɓɓan, k**ar gaɓɓan gwiwar hannu, idon sawu da sauran sassa.

Abubuwan da ke ƙara haɗarin kamuwa da ciwon gawut sun haɗa da:

1. Abinci/abinsha da ke ci/abinsha da ke maƙare da sinadarin 'purines' [duba jerinsu a sama].

2. Ƙiba/teɓa: Jikin mai ƙiba na samar ya sinadarin ''uric acid' da yawa kuma ƙoda kan sha wahalar tace sinadarin zuwa cikin fitsari.

3. Sanannun cutukan jiki: Ga duk wanda ya san yana fama da wasu cutuka k**ar hawan jinin da ba a shawo kansa ba, ciwon siga, ciwon ƙoda da sauransu, to yana da haɗarin kamuwa daga ciwon gawut.

4. Jinsi: Maza sun fi kamuwa da ciwon gawut fiye da mata. Maza kan kamu da ciwon gawut tsakanin shekara 30 zuwa 50, yayin da mata kuma kan sami jinkirin samun alamun ciwon gawut har sai bayan sun daina haila.

5. Samun ciwon gawut a dangi: Samun mai ciwon gawut a cikin dangi na nuni da cewa wani a dangin na da haɗarin samun ciwon.

Daga ƙarshe, ina fatan mun gane ire-iren ciwon gaɓa da sabubansu, sannan mun gane alaƙar cin jan nama da ciwon gwiwa, kuma mun gane cewa ba kowane irin ciwon gwiwa ne ke da alaƙa da cin jan nama ba.

Duba da haka, da zarar ka fara fuskantar alamun da muka ambata, tuntuɓi likitan fisiyo a asibiti mafi kusa da kai don duba ka.

©Physiotherapy Hausa

04/01/2025
08/09/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Eze Stanley, Salma Alhassan

04/09/2024

Ka San Haɗarin Ɗaga Yara Da Hannu?

Daga cikin raunukan da iyaye ko masu raino kan yi wa ƙananan yara ba tare da an sani ba akwai raunin gwiwar hannu da ake cewa "Pulled elbow" ko kuma "Nursemaid elbow" a turance.

Raunin "Pulled elbow" 'yar ƙaramar gocewar ƙashi ce a gaɓar gwiwar hannu da ta fi samun ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara shida. Raunin na faruwa ne sak**akon saɓulewar ko yagewar tantanin "annular ligament" da ke riƙe da kan ƙashin "radius" a gaɓar gwiwar hannu.

Me ke kawo wannan rauni?

Sak**akon gaɓoɓin yara 'yan ƙasa da shekara shida ba su gama yin ƙwari sosai ba, saboda haka, tantanin da ke riƙe da kan ƙashin na "radius" bai gama ɗaure ƙashin tamau ba. Wannan ya sa ƙananan yara aka fi jefa wa cikin haɗarin gamuwa da wannan rauni yayin ɗaukansu.

Saboda haka, wannan rauni yana da alaƙa da rashin lura ko ganganci yayin ɗaukan ƙananan yara k**ar:

Riƙe tafin hannu ko tsintsiyar hannun yaro tare da ɗagawa da hannu ɗaya ko hannu biyu yayin:

i. goyawa a baya.

ii. yi wa yara lilon hannu.

iii. ɗagawa domin ɗorawa ko saukewa daga abin-hawa, ko kuma tsallakar da su rami ko tudu.

iv. Fisgo hannun yaro yayin wasanni, da dai sauransu.

Domin kauce wa yi wa yara wannan rauni, a zaɓi riƙewa ko ɗaga yara ta hanyar riƙe damatsansu ko kuma sanya hannu tare da riƙo su ta hammata.

Alamun wannan rauni:

1) Yaron da ya samu wannan rauni ya kan yi ƙorafin ciwo daga gwiwar hannu zuwa tsintsiyar hannu musamman idan aka yi yunƙurin motsa hannun.

2) Haka nan, yaro zai maƙale hannun a jikinsa, sannan ya miƙar da gwiwar hannun tare da juya tafin hannun zuwa jikinsa.

Sai dai, irin wannan rauni ba kasafai ya ke zuwa da kumburi a gwiwar hannun ba.

Saboda da hake ne ake kira ga iyaye da masu raino da su guji ɗaga ko ɗaukar yara musamman 'yan ƙasa da shekara shida ta hanyoyin da aka ambata a sama, sannan iyaye su nusar da masu rainon yaransu domin kiyaye afkuwar wannan rauni.

Garzaya da yaro asibiti da zarar an lura da yaro ya kasa amfani da hannunsa, kuma yana ƙorafin ciwo a gwiwar hannu zuwa tsintsiyar hannu, musamman bayan zargin faruwar ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo raunin da aka ambata a sama.

© Physiotherapy Hausa

20/08/2024

| Daga cikin matsalolin da ke yi wa lafiyar baya barazana akwai sauye-sauyen da ke faruwa a ƙashin baya yayin da shekaru ke ƙara miƙawa. Waɗannan sauye-sauye na iya shafar ƙasusuwan baya, tsokoki, fayafayan tsakankanin ƙasusuwan baya, tantanai, laka da jijiyoyin laka.

Yin buris da ciwon baya ko kuma ɗaukar ɗabi'ar shan maganin rage ciwo kullum na daga cikin haɗuran da ke iya janyo tiyatar baya can daga ƙarshe.

Adana kuɗinka/ki ba sai ka sayi maganin ciwon baya kullum ba, tuntuɓi likitan fisiyo a yau.

Daga cikin muradan likitan fisiyo shi ne taimaka wa mai ciwon baya shawo kan ciwonsa ba tare da shan maganin rage ciwo kullum ba tare da ceto mai ciwon baya daga barazanar tiyatar baya.

© Physiotherapy Hausa

Address

Kofar Nassarawa, Emir's Palace Road, Kano
Kano
700231

Telephone

+2348068133126

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Physiotherapy Clinic and Gymnasium posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Arewa Physiotherapy Clinic and Gymnasium:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram