11/04/2026
TATSUNIYAR FIFIDALO
FIFI-DALLO
Ga ta nan ga ta nan ku.
Wata Bafulatana ce dai tana da dańta ana
kiransa Maigari. Mijinta kuma ana kiransa Fifi-Dallo.
Kullum sai ta tatsi nonon saniyarsu ta dora wa ɗanta ya tafi talla.
Ana nan ana nan. Ran nan da ta kare tatsar nonon sal ta ce da shi, "To Maigari, sai ka tafi talla. Ka yi ƙoƙari ko ka sayar ka dawo da sauri."
Sai ya ce, ""ya ba ni da lafiya."
Sai ta cê dole ya tafi tallan nan. Shi kuma ya ce ba zai lya ba. Ta dai tilasta masa ya đauki nonon ya tafi yâna kuka.
Yana cikin tafiya a dokar daji kafin ya shiga
gari sai ajalinsa ya sauka. Sai ya fadi da kwaryar nonon nan ya mutu.
Shi ke nan sai wata tsuntsuWa ta zo za ta wuce ta gan shi a kwance. Da ta gan shi sai ta ce, Wannan lafiya kuwa?"
Sai ta sauka ƙasa.
Da ta sauka sai ta dudduba ta gani ba shi da rai. Sai ta ce a ranta, Lalle wannan kome aka yi đan gidan Fifi-Dallo ne.'
Sai ta tashi fir, ta je ta sauka a kan soron gidan su wannan yaron. Da saukarta sai ta ce:
Uwargidan Fifi-Dallo.
Uwargidan Fifi-Dallo.
Fifi-Dallo Maigari ya fadi.
Fifi-Dallo can a dokar daji
Fifi-Dallo har da rigar saƙi.
Fifi-Dallo har da wandon saƙi.
Fifi-Dallo har da hular saƙi.
Fifi-Dallo har da zobbansa bakwai.
Fifi-Dallo har da ƙwaryar nono.
Fifi-Dallo sai a je đauko shi.
Ashe ita Uwargidan Fifi-Dallo tana niƙa, ba ta san cewa tsuntsuwar nan da ita ta ke ba.
Sai ta bar niƙan ta kasa kunnenta.
Sai tsuntsuwar nan ta kuma cewa:
Uwargidan Fifi-Dallo.
Uwargidan Fifi-Dallo.
Fifi-Dallo Maigari ya fadi.
FIfi-Dallo can a dokar daji.
Fifi-Dallo har da rigar saki.
Fif-Dallo har da wandon sakl.
FIf-Dallo har da hular saƙi.
Fif-Dallo har da zobbansa bakwai,
Fif-Dallo har da ƙwaryar nono.
Fifi-Dallo sai a je dauko shi.
Da ta ji haka sai ta yi salati ta saka kuka.
Sai ta tafi da gudu ta nemo mijinta. Da
ta ga mijin nata sai ta ce da shi, Zo ka li
abin da tsuntsuwar nan ta ke fadi.
Sai shi ma mijin nata ya saurara ya ji abin da tsuntsuwar ta ke fada, ya fashe da kuka.
Tsuntsuwar ta ce, "Sai ku yi hakuri ku daina kuka,.".
Shi ke nan. Sai ya yi wa tsuntsuwar godiya. Ita ma matar ta yi godiya. Da s**a yi wa tsuntsuwar godiya, sai ita kuma tsuntsuwar ta yi musu gaisuwar ta'aziya sannan ta tashi abinta fir.
Shi ke nan. Sai Fifi-Dallo ya gayyaci mutane aka je aka dauko gawar Maigari a makara, aka kawo shi gida, aka yi masa wanka.
Bayan an gama yi masa wanka, kafin a kai shi a bunne, sai mutane s**a ce, "Da ma ba shi da lafiya ne ?"
So matar ta ce, "Ni dai na tatsar masa nono na ce ya je ya sayar.
Sai ya ce da ni ba shi da lafiya, Ni kuwa na ce dole sai ya tashi ya tafi. Na dai tilasta shi ya tafi tallan nar ba da son ransa ba. Yana kuka ma ya tafi. Yana cikin tafiya sai ya
gamu da ajalinsa a daji. Allah ne ya kai wata yar tsuntsuwa dajin ta gano gawar tasa."
Sai mijnta ya-ce, "Yo ke ashe da ma ya ce ba za shi ba kika tllasta masa don kin gani ba na nan?To yanzu ai ga shi nan kin rasa shi, ni ma na rasa shi.'"
Shi ke nan. Sai aka hada shi aka kai shi aka
bunne.
Sai ita ma ta dawo tana cewa, "Da na sani ai da. ban tilasta masa ya tafi tallan ba,"
Shi ke nan.
Kurunkus.
Bayani:
Me wannan labarin ya tuna muku na yarinta?