29/06/2017
CUTAR SIKILA (AMO SANIN JINI)
SIKILA (AMO SANIN JINI).
***********************
Cutace dake rayuwa a cikin jini mutum bil
adama, cutar ana haihuwar mutum da ita ne,
ma'ana cutace da ke zaune a cikin jinin jikin dan
Adam.
Sikilar Wata cuta ce da ke k**a jajayen
kwayoyin halittu na jini. Wannan ciwo ba
kwayoyin cuta ke kawo shi ba, gadonsa ake yi
daga wajen iyaye, wadan da ke da wannan
nakasar a kwayoyin jini.
Wasu mutanen, nakasar tasu rabi ce, wadanda
ake wa lakabi da AS; wasu kuma duk kwayoyin a
nakashe suke, wadanda su ne a ke kira da SS.
Cutar Sikila na daga cikin jerin ciwukan da sai
dole an gada daga wurin mahaifiya da mahaifi
sa’annan yake nunawa.
Jikin kowane 'dan adam yana dauke da wani abu
da ake kira Genotype a turance. To wannan
Genotype din idan har ya kasance na miji da
mace su zo daya to kuwa 'ya'yansu duka zasu
kasance ba masu cikakkiyar lafiya ba.
Akwai → AA wannan shine lafiyayye
Akwai → AS wannan shine ke da rabin cutar
(ma'ana bai munana ba).
Akwai → SS To wannan shine mai cikakkiyar
cutar ta amosanin jini.
A lokacin duk lokacin da akayi aure tsakanin mai
SS da SS to duka ’ya’yansu su gaji wannan
nakasu (ma'ana zasu kasance masu dauke da
Sikila din). Su dukansu da ’ya’yan nasu kuma
kullum sukan kasance a cikin rashin lafiya, kenan
rabin zaman auren za'a iya yinsa a jinyace.
A lokacin da mai ciwon (SS) ya auri mai rabin
ciwon (AS), zai iya kasancewa wasu a cikin
’ya’yansu su gaji wannan ciwo.
Amma idan mai rabin ciwon (AS) ya auri wata
mai rabin ciwon (AS), to rabin ’ya’yansu ne za
su iya kasancewa masu amosanin jini, sauran
kuma
lafiyayyu.
Duk lokacin da mai AA ya auri mai SS Ko AS to
za'a iya samun sauqi kwarai da gaske.
Amma Idan Mai (AA) ya auri mai (AA) to fa
shikenan babu zance haduwa da 'ya'ya masu
dauke da cutar ta Amosanin jini.
KO CUTAR TA SIKILA KALA DAYA CE?
A'a Cutar ta Sikila kala 3 ce; Akwai mai sa
kumburin gabobi.
Akwai mai shanye jini gaba daya sai an rika yi
ana sanyawa mutum jini.
Akwai kuma mai sa zazzabi mai tsananin gaske,
a rika ganin mutum ko yaro yau ciwo gobe lafiya.
TO ANA WARKEWA DAGA WANNAN CUTAR?
A likitance babu maganin da ke warkarda
wannan cutar kasance wa cutace da take manne
da jini kuma cuta ce da take tare da jini a koda
yaushe.
Amma a musulunce tabbas akwai maganin da ke
warkar da wannan Cuta ta Sikila Domin Allah
(SWT) ya fada Cewa, Bai saukar da Cuta ba sai
da ya saukar da maganinta.
Don haka ga masu Sikila ko 'ya 'ya masu Sikila
ko 'yan Uwa masu Sikila ga Magani da Iznin
Allah.
Za'a nemi Ganyen Zogala a tare da Tare da
zangarniyar Zogalan a hade waje guda a markade
a rika shan rabin karamin Kofi sau 2 a rana
tsawon wata 2 In shaa Allahu za'a warke